Mene maganin ciwon ciki na barin hannun hagu



*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑* 1⃣2⃣2⃣Mene maganin ciwon ciki na barin hannun hagu❓
  🤔Ciwon ciki na bangaren hagu yawanci yana faruwa ne daga hanji ga mata kuma yafi faruwa ne saboda hannun mahaifa na hagu idan ciwon bai yawa ba yana tafiya dakansa cikin kwana 1-2,amma idan ciwon yazo da zazzabi, Ciwon yayi yawa ko wurin ya kumbura, ko kashin jini, ko yawan tashin zuciya ko amai, ramewa, ko fatar tazama yellow to akwai bukatar zuwa asibiti.
 🔸 *Diverticulitis* yana yawan kawo irin wannan musamman mutanen da suka kai shekara 40 zuwa sama, diverticulis wasu yan jikkuna ne ke samuwa akan hanji to idan suka kece ko suka kumbura ko infection yashiga sai diverticulis din yafaru yana zuwa da zazzabi, tashin zuciya, amai, kumburin ciki. Idan wannan ne yawanci Idan aka chanza abinci akasamu hutu sosai da wasu yan antibiotics anasamun lafiya
🔸 *Gas,* shima yana kawo ciwon ciki na bangaren hagu saboda idan gas yashiga cikin hanyoyin ko bututun narkarda abinci zuwa hanjin takashi inda daga nan sai bayan gida saiya haifarda kumburin ciki da marsalar narkewar abinci. Yana zuwa da ciwon cikin bangaren hagu, gudawa, amai, kashin jini, bugun zuciya, ramewa. Shikuma cin abinci dayawa, yawan hadiyar iska yayin hadiyar abinci, chin chingum, cin abinci ko shan abu mai gas, kokuma chin abinci dasuke da wuyar narkewa duk suna kawo shi.
 🔸 *Indigestion,* rashin narkewar abinci nakawo irin wannan ciwon cikin na hagu, yana zuwa da kumburin ciki, yawan tusa, tashin zuciya, ciwon zuciya.
 🔸 *Hernia, kidney stones, shingles,* duk suna kawo shi
👩‍👩‍👦‍👦Amma ga mata kawai akwai endometriosis, karin hannun uwa, ciwon al'ada, chanza wuri da hannuwa mahaifa keyi, ciki na wajen mahaifa, pelvic inflammatory disease.
👨‍👨‍👦‍👦 Amma ga maza kawai, hernia, chanza wuri na maraina
 Kaga treatment dole sai angane miye yakawo shi idan kuma yazo ne kawai cikin kwana daya zuwa biyu yatafi kuma bawani ciwo bane dayawa kuma ba wadancan alamun to ba damuwa.
*DR SHUAIBU MB*                     Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com

Comments