MENENE ALAMOMIN KIDNEY STONES, YAYA AKE GANESHI?



DR SHUAIBU MB(KIWON LAFIYA)
***DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑


 TAMBAYA 2⃣
DR MENENE ALAMOMIN KIDNEY STONES, YAYA AKE GANESHI?

 Kidney stone yawanci calcium oxalate ne, anasamun shi a abinci da muke ci, dayake jikin mu yana amfani da abinci wajen samun karfi bayan haka sai afitarda wanda ba abukata yabita hanyoyin jini zuwa kidney shikuma kidney yafitar dashi ta fitsari
Dayake fitsari yana tattaro datti da guba dayawa Aidan sukazo kidney suka isle babu ishasshen ruwa to saisu taru saisu farazama stones din,stones din suna da girma kamar kwallon golf.
 Wani lokacin stones din suna fita ta fitsari batareda mutun yasani ba Wani lokacin kuma akanji zafi yayin fitarsu.

 ***ALAMOMIN SA***

 1⃣Yawan jin zafi a wurin

 2⃣Fitsari da jini

 3⃣Tashin zuciya da amai

 4⃣Kwayoyin jini na halitta farare acikin fitsarin

5⃣ Za aga ana fitsari baikai yawanda akeyiba abaya kuma akai akai

 6⃣Radadi lokacin fitsari

 7⃣Bukatar yin fitsarin ta karu

 8⃣Zazzabi

9⃣ Idan stones suka dade a cikin jiki zasu iya dade hanya daga kidney zuwa bladder wanda yin hakan zaikawo ma fitsari cikas wajen fita daga jiki

 ABUBUWANDA KE KAWO SHI

1⃣ Mutanen dasuke da kidney stones va ayi maganinsa ba zai iya jawo matsanancin ciwon kidney

2⃣ Karancin ruwan jiki

3⃣ Shan ruwa kasada cup din glass na ruwa takwas arana

4⃣ Idan babu isasshen ruwa da zai dama acids din sai acids din yazama more acidic

 5⃣Idan fitsari yahadu da acidic na muhallin watau muhallin da mutum yake rayuwa yana fitarda air pollution zai iya haifarda stones

 6⃣Akwai cututtuka dasuke haddasa stones kamar urinary tract infection da crohon's disease dasauransu

7⃣ Kidney stones yafi kama maza akan mata kuma dayawa yafi kama yan shekara 30-50 da haihuwa sannan idan akwai history na family dinku kaima kana da hadarin kamuwa dashi.

8⃣ Sannan inka tabayinsa akwai yuwuwar gaba ka kara saminsa

9⃣ Akwai magungunna na ciwon kai suma suna kara jefa mutum cikin hadarin kamuwa dashi,
 Anace ma maganin TOPAMAX

 1⃣0⃣Sannan dadewa ana amfani da vitamin D da calcium na kara hadarin kamuwa da stone na kidney

1⃣1⃣ Sannan abincinda yakeda protein da sodium dayawa amma yanada calcium kadan shima yana haddasa ko kara hadarin samun stones, yanayin tafiyarda rayuwa ta yan ba ruwanmu, ko kiba, hawanjini, gudawa, matsalar hanji duk suna kara jefa mutum cikin hadarin kamuwa da kidney stones

 ***TREATMENT***

 Treatment din yakasu kishi kishi ne wani lokacinma a gida mutum zai iya Treatment dinsa basai anje asibiti ya danganta ne da girmansa.

 Idan mutum yataba samun kidney stones din abaya dama to treatment a gida lafiya lau a wajensa amma Idan farko ne yanada kyau yafara tattaunawa da likita tukunna

 Akwai matakai da mutum zai iyayi don taimakawa ma likita wajen warkarda shi

1⃣ Farko arika shan ruwa akalla cup goma na glass arana

2⃣ Akwai abinci da akeci wanda yake hana samun stones din dakuma wanda idan ansamu yana hanashi tasiri inma basu girma ba zasu fita ta hanyar fitsari
👇
 Basil, apples, celery, grapes da pomegrates

 Cikin hour 48-72 insha Allah ana iya fitardashi duka inde an sha ruwan sosai kullum akayi amfani da wasu daga Cikin wadannan abincin ko duka

3⃣ Kidney beans, yanada matukar magani idan aka dora shi aka tukunya da ruwa yayi hour shidda yana tafasa sai a safke atace ruwan abarshi yahuce asha duk bayan hour biyu zuwa kwana daya zuwa kwana biyu

 4⃣Saikuma vitamin B6 supplements suna taimakawa sosai.

ALLAH YAKARA LAFIYA MAI AMFANI

Comments