*DAGA ZAIREN KIWON LAFIYA🚑🚑* *CIWON NONO LOKACIN SHAYARWA* 1⃣1⃣7⃣ Ciwon nono yana daya daga cikin dalillai dayake sa wasu matan dakatarda shayarwa.
Wani ciwon kan nonon na zuwa dasauki wani kuma yana zuwa da zafi sosai kusan kishi 26% matan da ke shayarwa na samun wannan zafin ne dalilin cracking akan nonon watau tsatstsagewa idan aka lura kila za aga shine
🤱 Wasu matan kuma yanayin position dasuke rike yaranne ke haifarda wannan zafin.
🤱 Wasukuma matan yanayin da suke barin yaran saisunji yunwa sosai ake basu nonon shiyasa wajen sucking din saisu rika irin kamar basu taba shaba
♦Akwai zafi da akeji dayake farko a wunin watau farkon shan nono a farko wuni kuma da ruwan nonon yazo sai adena ji.
♦ Wasukuma zafin na dorewa harkusan 30 second, wasukuma zafin na kaiwa daga wannan shayarwa zuwa wata watau de wuni ake anajinta.
♦ Wasukuma suna jin zafi ne farkon kwanaki ukku da haihuwa ko sati daya.
🔸Idan fatar bata lalace ba watau ba tsatstsagewa, ko kuma kan nonon bai chanza ba kafin da bayan shayarwa, kuma ba bleed bawani dan kurji kowani abude bako to kawai a chanza yanayin rike yaron ko position dinda akeba yaron nono kokuma adena dadewa kafin abashi.
Amma idan akaga wadannan abubuwa kamar haka :- 🤱Zafi yazama kowace shayarwa anajinsa
🤱Zafin yayi yawa matuka
🤱Zafin yana ko anajinsa daga wannan shayarwa zuwa ta gaba batareda anji sauki ba.
🤱 Zafin yawuce sati biyu bayan haihuwa.
🤱 Kokuma aga kan nono ya tsatstsage, ko yana bleed, ko wurin ya sale to aje asibiti.
✍ *DR SHUAIBU MB* Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com
Salam , Barka da wannan lkc Ina fama da ciwon nono Kuma Ina shayarwa Yana zugine kamar maruru ne yafito ataimakamin da magani . Nagode
ReplyDelete