*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
*RASHIN GAMSUWA LOKACIN JIMÀ'I* 🤔✍
Jima'i wani abu ne dayawuce ace ankai kololuwar jin dadi
kawai lokacin da akeyi, wani abune na kawance wanda shi zai kaiga jin dadin na
koluluwa yayin saduwa, bayadda za ayi aji dadin saduwa idan mutum yazama shi
bai chanza ba. Ga wasu dalillai dasuke kawo wannan matsalar
♦-Tunani dayawa, idan lokacinda
mutum ko ake saduwa kamata yayi mutum zuciyarsa tazama ba abunda yake Tunani a
zuciyarsa, domin duk yadda abokin saduwar ki ko ka yazama ko tazama kwararriya
ko duk abinda zaikara dadin saduwar inde zuciya tana tunani ko saqe saqe to
bayadda za ayi aji dadin saduwa
♦ -Rashin soyayya, idan ba soyayya
abune da bazai yuwu asamu gamsuwa ba kokuma aji dadin saduwa
♦ -Kwatance, idan mutum namiji ko
mace zairika kwatanta nashi mijin ko matar da wasu na kawayen su ko matan
abokansa kokuma kwatanta abinda muke kallo ko muke karantawa a litattafai ko
mujallu to mutum bazai rika jin dadin jima'iba
♦-Zargi, idan mutum zairika Zargi
abokin zamansa da rashin kamewa to ba yadda za ayi arika jin dadin jima'i
♦-Idan akwai rashin jituwa ko
fada tsakanin ma'aurata yana haddasa rashin jin dadin jima'i
♦-Yin sauri ko gaggawa a wajen Yin
jima i nasa rashin jin dadinsa, ayi hkr arika daukar lokaci tundaga fira,
wasanni da yan abubuwa da ba a rasa ba kafin jima'i sunasa aji dadinsa amma
sauri a harkar nasa rashin dadinsa
♦-Rashin ingantaccen tsarin wurin
jima'i, misali ga tambayoyi. Dakin ya chanchanci wurin jima'i?, dakin akwai
natsuwa?, dakin akwai abubuwanda ake bukata,?, ya dressing din ma'auratan yake
sunyi irin yanda zai iya daukar hankali?, anyi wanka?, ana kamshi?, gyaran
jiki, abincin da akaci last wanda yadace ne a lokacin?, dasauransu
♦ -Samun wanda kuka dace a wajen
bukata ta jima'i, idan tunfarko akasamu akasi akahadu wanda ko wadda bukatar ku
batazo daya ba akan wannan to yanada wuya arika jin dadin jima'i
♦-idan abaya antaba samun cin
zarafi na jima'i to abin yakan shafi tunani tayadda ko a gaba baza aji dadin
jima'i ba
♦-Rashin chanzawa, mutum zaice shi
yadda yakeyi haka zaiyi kokuma yadda yakeso haka zaiyi ba tunanin abokin ko
abokiyar jima'in yakamata arika yin abinda kowa zai samu gamsuwa bawai abinda
mutum daya keso ba. Tattaunawa shine yakamata
♦ -Tsafta, tunda ruwan jiki zasu
hadu, halshina zasu chakuduy, zanen gado zai dauki zufa ko gumi, idan yakasance
ba tsafta ana kyankyamin juna akwai matsala kina ko kana kyankyamin saka
halshenka cikin na patner dinki ko dinka koshi yana kyankyamin sanya bakinsa
akan jikinki ko kirjimki kokuma hancinsa akan gashin kanki ko ke kina
kyankyamin sa ya za ayi aji dadin jima'i
♦ -Rashin chanza position ko style
ta kwanciya, babban abune dayake sanya Rashin jin dadin jima'i
♦-Jima'i ba yaki bane bakuma fada
bane kuma kowa nada hakkin ya nema lokacinda bukatarsa ta taso idan akace mace
batada wannan damar ko hakkin saidai namiji yayi lokacinda yakeda bukatarsa
amma ita batada wannan kuma yayi yadda yakeso batareda tunanin bukatinta ba to
bayadda za ayi aji dadin Jima'i
♦-Rashin aiwatarda wasanni
kafin jima'i yana sanya Rashin jin dadin jima'i
♦-cold hindplay, wannan gabace mai
mahimmanci tayadda za aga idan aka kai kololuwa akasamu gamsuwa musamman namiji
shikenan sai bacci kokuma kaga kamarma makiyan juna bawani wasa ko maganganu na
soyayya bare maganar yabawa da godewa juna, wannan yanasa aji ba ajin dadin
jima'i. Abinda yakamata bayan ankai kololuwa angamsu sai a matse juna sosai a
sumbachi juna musamman mace sunason a matse su ahadasu a jiki sosai a sumbachi
su ayaba kyawunsu ko wata halittarsu a fadamasu dadadan kalamai irinna soyayya
musamman arada masu a kunnuwan su kamar i love you wannan zaisa surika gamsuwa
sosai
♦-Ra'ayi akan jima'i, wasu
suna daukar jima'i ma kamar sabo ne, idan da a addinance zasu fahimci cewa
jima'i abune maikyau da tarin lada to zasu rika jin dadinsa, haka idan da zasu
san irin amfaninsa a lafiyance shima zaitaimaka sabo da wasu basujin dadinsa
musamman mata sabida Ra'ayi ko tunaninsu akan -Tsoron daukar juna biyu, wannan
babban abune dayake taimakawa wajen rashin jin dadin jima'i ga mata saboda tana
tsoro kada ciki yashiga kada sperm yashiga ko bayan angama jima'i ma tana tsoro
tanata tunanin ranar al'adarta tazo taga jini ko akasin haka, saboda haka
bayadda za ayi taji dadin jima'i
♦-kowane mutum namiji ko mace yanada
inda bayaso ataba ko batason a taba lolacin jima'i dole a kiyaye kuma yanada
kyau arika koyama juna abubuwa da kowa keso dakuma yadda yake ko take so
♦-Rashin yin magana koya take
yana ragema jima'i karsashi yayinda ake cikin aiwatarda shi kalamai ko wani
abude na fitowa daga bakunan juna nakarama jima'i dadi kuma nasa ma'aurata suji
dadi kuma kowa ya gamsu
♦ -Ga mata dasuka taba aure wani
wuri suka rabu suka sake wani auren kokuma Ga mazanda ba mata daya gareshi ba
kokuma shima yataba auren abaya to kada arika tunani yadda nabaya yake ko take
kokuma yadda akeyi dana ko data baya
♦-Low self esteem, rashin gamsuwa da
jikinki ko tunanin cewa kinada wani rauni ko wani nakasu a jikinki kokuma
tunanin rashin iya gamsarda mijinki watau de bakida tabbas dakanki
♦-Sonkai, idan yakasance daya daga
cikin ma'aurata keson biyan bukatarsa kawai batareda la'akari da dayanba, ayi
atafi ayi barci to baza aji dadin jima'i ba
Dukdade ba duka bane amma
wadannan wasu daga dalillan ne da dayawansu ba magani suke bukata ba.✍ *DR SHUAIBU MB 2/9/2018*
*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
*meke kawo ciwon ciki nabarin hannun hagu* ❓❓
🤔 ciwon ciki na
bangaren hagu yawanci yana faruwa ne daga hanji ga mata kuma yafi faruwa ne
saboda hannun mahaifa na hagu idan ciwon bai yawa ba yana tafiya dakansa cikin
kwana 1-2,amma idan ciwon yazo da zazzabi, Ciwon yayi yawa ko wurin ya kumbura,
ko kashin jini, ko yawan tashin zuciya ko amai, ramewa, ko fatar tazama yellow
to akwai bukatar zuwa asibiti.
♦ *Diverticulitis* yana yawan kawo
irin wannan musamman mutanen da suka kai shekara 40 zuwa sama, diverticulis
wasu yan jikkuna ne ke samuwa akan hanji to idan suka kece ko suka kumbura ko
infection yashiga sai diverticulis din yafaru yana zuwa da zazzabi, tashin
zuciya, amai, kumburin ciki. Idan wannan ne yawanci Idan aka chanza abinci
akasamu hutu sosai da wasu yan antibiotics anasamun lafiya.
♦ *Gas* , shima yana kawo ciwon ciki
na bangaren hagu saboda idan gas yashiga cikin hanyoyin ko bututun narkarda
abinci zuwa hanjin takashi inda daga nan sai bayan gida saiya haifarda kumburin
ciki da marsalar narkewar abinci. Yana zuwa da ciwon cikin bangaren hagu,
gudawa, amai, kashin jini, bugun zuciya, ramewa. Shikuma cin abinci dayawa,
yawan hadiyar iska yayin hadiyar abinci, chin chingum, cin abinci ko shan abu
mai gas, kokuma chin abinci dasuke da wuyar narkewa duk suna kawo shi
♦ *Indigestion* , rashin
narkewar abinci nakawo irin wannan ciwon cikin na hagu, yana zuwa da kumburin
ciki, yawan tusa, tashin zuciya, ciwon zuciya
Amma ga mata kawai akwai
endometriosis, karin hannun uwa, ciwon al'ada, chanza wuri da hannuwa mahaifa
keyi, ciki na wajen mahaifa, pelvic inflammatory disease.
Hernia, kidney stones,
shingles, duk suna kawo shi
Amma ga maza kawai, hernia,
chanza wuri na maraina
Kenan treatment dole sai angane miye
yakawo shi idan kuma yazo ne kawai cikin kwana daya zuwa biyu yatafi kuma
bawani ciwo bane dayawa kuma ba wadancan alamun to ba damuwa *.✍ DR SHUAIBU MB 2/9/2018*
Comments
Post a Comment