*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA*🚑🚑 *LUNULA*
Lunula shine wannan farin abin kamar wata dayake fitowa kasan farce a kowane dan yatsa kamar wata, saidai dayawa mutane basu san ma minene shiba ko amfani sa ko miyake nunawa a irin lafiyar mutum. Dayawa akan fahimci wasu matsaloli na lafiya da mutum yakeda su a wurin wannan dan farin abin dake kan farce, shiyasa bai kamata ace duk duk sati ko duk lokacin da mutum ya yanke farce ko yagadama yasa razor yayita karkarar bayan farce sa ba.
Lunula ba lalle bane yazama fari ba a a saidai don ana ganinsu ne ta farci kuma ba akan farcin yakeba kalkashi farcin yake, idan lunula ya lalace to farci ma zai lalace idan kuma farcin ya lalace za aga shi yanana nan da wani farcin yafito shima za agansa inde bai lalace ba.
Ta hanyar chanza color, ko size ko bacewar lunula za a iya fahimta lafiya ko akasin lafiya ga mutum wanda bayan mutum yawarke daga cutarda ke damunsa sai aga koda ya bace yana dawowa a hankali kokuma yana komawa normal color dinsa ta asalin.
Duk yatsun mutum duka yakamata ace ansamu lunula, karancin lunula akan farcin mutum yawan raunin karfi da garkuwa ko kariya da mutum yakeda ita, wanda wani lokacin mutum zaiji bayada karfi ga yawan gajiya koya yayi aiki sai gajiya, kokuma mutum yaga kawai ga babban yatsan ne yakeda shi shima alama ce ta jikin ba karfi kuma alama ce ta zuwan wani cuta ko ciwo kowane lokaci.
Mutane da basuda ita gaba daya ba lalle ne ace suyita famada rashin lafiya ba ko cututtuka ba amma za aga sunada wata cuta dasuke famada ita, ga yara da basuda ita iyaye ba abin damuwa bane insuka kara girma za aga tana fitowa a hankali.
Sannan ga wadanda basu samun isasshen bacci sosai da daddare suma tasu na dushewa a hankali kuma inta bace bazata sake dawowa ba shiyasa idan mutum baya samun bacci da dare yaga yana bacewar to saiyayi kokarin samun bacci sosai.
Yatsu 8-10 yakamata ace sunada lunula a kowane mutum sune normal de.
*Girmanshi* yakamata akalla yakai daya saman biyar na farcin
*Color dinsa* yakamata yazama fari, yawan fari yawan lafiyar mutum, karancin farinsu karancin lafiyar mutum
Lunula babba na nuna isasshen circulating na jini, karantarsa na nuna rashi circulating na jini sosai, bacewarsa na nufin karancin jini
Ivory color shine normal, mutane masu karfi, masu cikakka lafiya, masu kuzari.
🔻Pink color, na nuna kode mutum yasamu diabetes kokuma yana gabda samun diabetes din
💚Grey color, yana nuna raunin wasu gabobi na jiki misali mutum yaga baya iya narkarda abinci sosai, ciwon ciki, yawan famada karancin jini, yawan kasala.
💜Purple color na nuna karancin halbawa jini zuwa ga zuciya wanda matsaloli jijiyoyi suke haddasawa, wanda za ayita famada jiri, ciwon kai
⚫Black color, yana nuna matsanciyar ciwon zuciya, xancer ko cin ko hadiye ko shakar guba.
👍 Lunula ga babban dan yatsa kawai musamman pink color na nuna matsalar ko raunin hunhu wanda za aga mutum na saurin kamuwa da mura sosa, kuma zai iya samun diabetes
🖕Lunula ga yatsa na tsakiya, yanada alaqa da tunani da kwalwa, yazama pink color yanuna rashin samun bacci, mafalke mafalke, jiri, ciwon kai da rashin mayarda hankali
👆Lunula ga yatsa manuniya watau index finger yanada alaqa da hanji da ciki, to idan akaga yazama pink yana nuna rashin circulation ga hanji sai aji ba ason cin abinci saboda baki ba dandano
✋Lunula akan yatsanda akesa ma zobe watau ring finger, idan yazama pink za aga idan macece tana famada matsalar rashin tsayayyae jinin al'ada
✋ Lunula akan karamin dan yatsa bai cika futowa ba gaskiya inma yafito za aga yana zuwa da zazzabi kokuma idan jane to alamar matsananciyar ciwon zuciya
Ga wasu mutanen zasuga basuda lunula akan farcin su ko daya, wannan ga wadanda suka san ko miye shi kokuma miyake nufi wani lokacin sukan damu amma ba lalle bane yazama abin damuwa ba, wani lokacin gawasu sukan ga nasu ne akan babban dan yatsa kawai wasukuma duka basu gani, lunula yana shigewa a kalkashi fata saboda kowane mutum yanada lunula a farkon rayuwarsa saidai daga baya saboda dalillai dana fada asama ya bace
Dukda wasu mutanen damuwa ma tanasa ya bace ko matsalar karancin jini ko rashin samun ingantaccen abinci, amma idan bakada ko bakida lunula ko daya kuma akwai wadannan alamomin ko abubuwa tareda mutum yakamata aga likita
♦Gani bishi bishi ko jiri.
♦Sai damkar ciki ko ciwon ciki
♦Mutuwar jiki
♦Kasala
♦ Mutuwar jiki
♦Rashin sha'awa ko mayarda hankali kan abinda mutum keyi na yau da kullum
♦Rama ko kiba dasauri batareda dalili ba.
Sauran color na lunula dasuke da hadari itace 🔵blue, wanda haka yake nuna Azure lunula kuma yana nuna wilson's disease wanda akafi sani da *hepatolenticular degenaration* ciwone da ake gadon shi inda sinadarin copper ke yawa a jiki mutum yadda kwalwa, hanta dasauran mahimman sassan jiki basu iya daukar sinadarin saboda yawa
Akwai alamomin da banda Azure lunula watau blue color na lunula, akwai su dasuke nuna wannan matsalar ta ta wilson's disease kamar haka
🔸Rashin dandano
🔸Ciwon ciki
🔸Kasala sosai
Jaundice
🔸 Idon mutum yazama golden Brown
🔸Mutum wani lokacin yarika samun matsala wajen magana
🔸Aga ruwa na taruwa a kafar mutum
🔸Mutum yarika kyarma ko motsin da zaikasa controlling dinsa
Bayan haka akwai, red lunula itace pic dinta ke sama wadda itama lunula ce datake nuna wata damuwa daban.
Sannan akwai wata irin lunula da akecema *PYRAMIDAL lunula* itakuma musamman akafa take fitowa kuma za aga tabada size ko shape na triangle wannan tana nuna akwai rauni akan yatsan ne kuma zata tsaya ahaka harsai raunin yawarke farcin ya fadi wani sabo yafito
Daga ciki irin cututtuka dasuke sanya irin wannan lunula din taba da irin wadannan kaloli akwai
🔹Ciwo zuciya
🔹Matsalar hunhu
Da cin guba
🔹Matsala jijiyo jini
Dade manyan cututtuka wasu shiyasa in mutum yaga haka akan lunula dinsa musamman ta kafa saiya je asibiti
Zantakai ta nan akan maganar lunula amma akwai bayanai dayawa akanta amma Alhamdulillah nasan dayawa ma ba adamu da itaba ba'asan mahimmanci ta ba. Kuma nayi bayanin tane badan atayarma kowa hankali ba sai don musan mahimmanci irin wadannan halittu da Allah yayi mana a jiki da abinda suke nufi.
✍ *DR SHUAIBU MB* Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com

Comments
Post a Comment