MARURU

*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
 Don Allah nine wani Abu Kamar maruru yafitomin a wuyana kusa da keyana ta ciki wajen harya Dan kumbura kuma gashi yana zafi, wani shawari za a iya taimakamin dashi da magungunar da zan sha❓
🤔Kurji ko kullutu na wuya da akecema lump ko masses suna ko yana girma har arika hangensa ma ta waje kamar yadda kace naka ya kumbura kuma wani lokacin su tsaya kanana gasu suna sanya mutum yarika jin ciwo, irin wannan kullutun ko marurun a cikin wuya wani bayada hadari wani kuma yanada hadari sosai don wani infection ne, wanima cancer ce.
Amma ga yadda suka kasu watau rabe rabensu don ka fahimci naka wane irine don asan taya za abullo masa.
1⃣- *infectious mononucleosis,* yawanci irin wannan yana zuwa ne ta kwayar cuta ta virus watau Epstein-Bar virus yawanci yafi damun matasa da shekarunsu ko wadanda suke a shekaru na manyan makarantu.
Alamominsa sune zazzabi, ciwon kai, wahala ko zafi wajen hadiya, kasala, zufar dare, ciwon jiki, kuma yana kaiwa har watanni biyu
2⃣- *Thyroid nodules,* kullutu ne da yake tauri wani lokacin kuma ana iya jinsa da taushi harda ma ruwa a cikinsa, kuma irin wannan yakasu kishi ukku warm, cold da hot yadanganta da irin hormones dinda ya samar.
Shi wannan yana cutarwa kokuma mai hadarine don yawanci cancer ce kokuma abinda yashafi garkuwar jiki ce.
Alamomimsa sune, kumburi makoshi, tari, budewar murya, ciwon makoshi ko wuya, numfashi da hadiya su zama anajin zafi
3⃣- *Branchial cleft cysts,* shikuma wannan wani karine da yawanci ake haihuwar jarirai dashi bari daya na wuya kokuma duka barin na wuya kokuma akan wani kashi da akecemea callerbone.
Yana faruwa ne lokacinda ake halitta mutum a cikin ciki a wajen halitta tsokokin wuya sai asamu yar matsala ta matsewar tsoka , kuma baicika cigaba da girma ba amma wani lokacin bayada hadari wani lokacin kuma yana haifarda infection harma cancer.
 Alamominsa sunhada, za'aga dimple, kullutu, ko skin tag a wuyan yaro watau jariri ko saman kafadarshi ko daga kasan  collerbone watau kashin da yake kusada ko gabda kafada daga wuya.
Sauran alamomi za aga kawai ruwa na bulbula daga wuyan yaro, kumburin wuya, yawanci daga saman wuya
4⃣- *Goiter,* Goiter maruru ne ko kullutune da yake girma sosai a cikin wuya aga wuyan mutum bari daya ya kumbura harya kamar murgude, shi wannan ina ganin mutane dayawa dashi yana da dangantaka ne da karuwar ko raguwar thyroid hormones ne.
 Yana kara girma Yana haifarda matsalar hadiya, numfashi, tari, budewar murya, jiri lolacinda mutum yadaga arms dinshi saman kansa
5⃣- *Tonsilitis,* akwai wani kari ko nama dayake fitowa a chan cikin baki daga baya za a iya hango shima idan aka duba daga saman bangon baki yake fitowa.
Alamominsa sunhada numfashi mai wari, wahalar hadiya, kaikayi makoshi kamar mura, zazzabi, ciwon kai, ciwon jiki.
 Wani lokacin za a iya kallon shi yana kumbura, ga kuraje farare ko jajjaye akansa
6⃣- *Hodgkin disease,* shi baicika ma ciwo ba saidai kawai aga wuyan kumbure, alamoninsa suna zuwa da kumburi, zufar dare, kaikayi, zazabi kowane lokaci.
 Kasala, ramewa, tari kowane lokaci
7⃣- *Non hodgkin lymphoma,* shikuma rarrabuwa ne na halittun jini farare ne amma dasuke da alaka da canxer, sukanzo da zazzabi, zufar dare, rama, hanta takara girma, kumburin wuya, rashin ciwo a wajen kumburin, kurajen jiki, kasala, kumburin ciki
8⃣- *Thyroid cancer,* cancer ce ta makoshi yana faruwa ne lokacin da cells watau halittun makoshi suka rika girma ba gaira ba dalili harsu wuce yadda yakamata.
 Alamomin sunhada budewar murya, kullutu a wuya, ciwon makoshi da wuya, zafi ko wahalar hadiya
9⃣- *swallow lymp nodes,* akwai kullutan wuya su rika kumbura dalili stress, infection, shan magungunna, cancer dasauransu.
Yawanci irin wannan kullutun yana da kumburi sosai ko kadan, da ciwo kokuma yazo ba ciwo, bangare daya ko duka, kokuma yafito ma a kowane bangare na jiki.
Alamominsa za agansa karami kamar girmar wake, yana fitowa a hamitta, kasan haba, wqjen wuya dade sauransu wanda muke cema kaluluwa da hausa
1⃣0⃣- *Limopa,* kullutu ne karami, mai laushi, yawanci inka dannashi da hannu yana buljewa watau yachanza wuri, kasan fata yake fitowa, baya wata color, yqna fitowa a wuya, kafada, da baya, baya ciwo inba girma yayi ba yataba jijiya ba
1⃣1⃣- *Mumps*, shi wannan wani kullutune da ake dauka ko ake yadawa ta hanyar yawu, zufa, ruwan hanci, dakuma mu'amullah da masu shi.
Yana zuwa da zazzabi, kasala, rashin dandano da rashin son cin abinci, ciwo kai da jiki.
Sannan saboda gabarda ke samarda yawu ta kumbura za aga baki wurin kumatu ya kumbura
Inba ayi saurin magance shiba yana zuwa da kumburin maraina, mahaifa, da manyan cutuka ciki harda dena ji gaba daya
1⃣2⃣- *Bacterial pharyngitis,* shikuma wannan kumburine da bayan makoshi yakeyi wanda infection na bacteria ko na virus ke kawowa, yana zuwa da kuraje, bushewar makoshi, karcewar makoshi, saiya haifarda zazzabi, ciwon jiki, zubar hanci, tari, kasala, ciwon kai, tashin zuciya
1⃣3⃣- *Throat cancer,* cancer ce datake kama akwatin ko matattara ta murya dasauran bangarorin makoshi
Tana zuwa da budewar murya, zazzabi, zafi wajen hadiya, rama, murar makoshi, tari, yawan atishawa, yawanci mutane masu shan cigarette, barasa, karancin sinadarin vitamin A, oral hpv, rashin tsaftar baki sunfi kamuwa da ita
 1⃣4⃣- *Actinic keratosis,* maruru ne ko kullutu da yawanci baya wuce girman 2cm ko girman cleaner ta goge pencil, yana zama kamar ya siriri, amma yana fito wa a inda rana ke bugu kamar kafada, wuya,  hannuwa, kafada
 1⃣5⃣- *Basal cells carcinoma,*  maruru ne kuma yana kode wuri yayi kumburi, yayi kamar tabo, ana ganin jijiyoyin jini, yana fashewa, yazama kamar rauni kuma daya warke saiya dawo
1⃣6⃣- *Squamous cells carcinoma*, shima de kamar rauni yake komawa a jikin wuya musamman abayan wuya, fuska, hannu, kunnuwa, saiya fashe yayita girma yana yaduwa, shima yana warkewa kuma yasake dawowa
1⃣7⃣- *Melanoma*, cancer ne dayawanci take samun mutane masu fata mai haske, za aga moles ko ina a fata, yana girma a hankali harya girma kamar pencils
1⃣8⃣- *Rubella,* wannan wasu irin kuraje ne a fuska dasuke yaduwa zuwa jiki za agansu jajjaye sosai ko pink suna zuwa da alamomi irinsu, kumburin ko kullutu a wuya, zazzabi, ciwon kai, zubar hanci, kumburin idanu da chanza color suyi ja.
Yanada hadari sosai ga mai juna biyu da abinda ke cikinta amma akwai vaccination da za a iya ba jariri
1⃣9⃣- *cat scratch fever*, ana samun sa daga cizon mage ko yakushinta idan wata kwayar bacteria tashiga jikin mutum wurin saitayi ja, za aga kusada inda ta ciza ko yagar yayi wani kullutu, akwai zazzabi, ciwon kai da jiki, kasala.
 Maruru ko kullutu ko kumburin wuya yana iya zuwa da laushi, tauri, Yana iya zuwa kasan fata ko cikin fata ko saman fata.
 Abinda yasa irin wadannan matsalolin na wuya sukeda matsala saboda sunkunshi jijiyoyi, tsokoki, kasusuwa dasauran bangarorin jiki dasuke da alaqa da wuya kuma duka suna iya samo asalin su achan.
 Abubuwa dayawa zasu iya haifarda irin wadannan maruru ko kurji ko kumburin wuya ciki harda infection na kunne.
 Da matsalar hakori, karancin wasu sinadarai, matsalar garkuwa jiki rauni, cancer, kwayoyi cututtuka irinsu bacteria, virus, sauran abubuwa sunhada da allergy na abinci, magungunna, duwatsu cikin gabarda ke samarda yawu saisu dade hanyar yawun din dade sauran abubuwa.
 Sannan ciwon kunne nada mahimmanci wajen kulawa a mutanen da sukeda wannan kumburin ko kullutu ko karin wuya din.
 Shawara shine idan anga irin wannan ba agane masa ba aje asibiti nan ENT akwai kwararru dazasu yi abinda yadace insha Allah. Allah yakara mamu lafiya amin
 ✍ *DR SHUAIBU MB*                     Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com

Comments