* *MEYAKE KAWO CIWON KAI BAYAN SEX❓*

*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑* *MEYAKE KAWO CIWON KAI BAYAN SEX❓*
Sex headeache yana zuwa ne dalilin activities na sex musamman lokacin da akazo wajen gamsuwa wanda za aji ciwon akai da wuya wanda yawan sha(awar ko durmiya cikin harkar ke kara yawan ciwon kokuma kawai aji ciwon kai din lokacin da ake gamsuwa ko bayan angamsu din watau realising.
Wani lokacin irin wannan ciwon kan bawanda za a damu bane wani lokacin kuma yana alaqa da hanyoyin ko jijiyoyin jini dasuke isa ga kwalwa.
Wasu ciwon kan na yan mintuna ne yatafi wasu hours wasukuma wuni daya yayinda wasuma har kwanaki yana kaiwa.
 Wasu mutanen irin wannan ciwon kan ma yakan dauki lokaci mai tsawo kusan watanni shidda ko shekara amma dawani nau'in ciwon kan amma de tushen wannan sex headeache dinne amma sai yazo as clusters headeache watau ciwon kan da ake ji a ido daya zuwa wuya da kafada, zufa a goshi, wani lokacin har kumburi bangare idon keyi.
Shi irin wannan ciwon kan na sex headeache yana faruwa ne saboda wasu dalillai misali kamar,       ♦budewa ko kara girma da jijiyo jini suke sukara girma lokacin da ake ko aka ko bayan angamsu din watau realising.
♦ Rashin alaqa ko dangantaka tsakanin kananan jijiyoyi da manya jijiyoyi na cikin kwalwa da hakan ke haifarda bleed a cikin wata jikka ruwa datake dauke da ruwan lakka cikin kwalwa da wajenta
Stroke
 ♦Bleeding na bayan kananan jijiyoyin zuwa kwalwa.
♦ Ciwon jijiyoyi.
 Amfani da magungunna na tsarin iyali watau pills.
♦ Wasu damuwar daga wasu infections din.
 Idan ciwon kan yana zuwa da tsanani mutum yarasa inda yake, ko amai, ko rikewar wuya, ko wasu matsaloli jijiyoyi de, ko yana kaiwa har hour 24 to abinda za adamu ne gaskiya da za aje asibiti.
👳‍♂Maza sunfi yin irinsa dakuma mutane dasuke yawan famada ciwon kai akai akai irinna gefe daya dinnan.
 Ana iya kariya da samun sex headeache wajen kaurace ma sex din kafin realising.
 Sannan akwai wasu magungunna da akesha hour daya kafin sex din suma don guje ma irin wannan ciwon kan.
 Akwai wasu magungunna na hawanjini da ana iya shansu kullum don guje ma irin wannan ciwon kan.
 ✍ *DR SHUAIBU MB*                     Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com

Comments