*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑**ABINCIN
DAYA KAMATA MAI JUNA BIYU TACI*❓
Mai juna biyu tana
bukatar abinci masu gina jiki sosai fiyeda lokacin da batada ciki, jikin mai
juna biyu yana bukatar karin sinadarin vitamin, minerals, da nutrients.
Akalla mai juna biyu na
bukatar calories dayawa akalla 350-500 a rana
Rashin abinci mai gina jiki ga
mai ciki na iya shafar girma yaro a cikin ciki, sannan kuma dabi'ar cin abinci
da batada tsari wadda ka iya zama sanadiyar karin nauyi ga mai ciki ko kiba na
iya kara jefa ta ciki samun matsala wurin haihuwa kokuma yawan matsaloli ga
ciki din
🔹-Diary products, mai ciki
na bukatar karin sinadarin protein da calcium saboda girman dantayi dake cikin
cikinta, wannan rukunin sunhada da yoghurt musamman greek yoghurt yafi amfani
ga mai ciki, amma idan mace nada matsalar narkewa abinci watau baya saurin
narkewa saita yi amfani da probiotics yoghurt. Amfani da probiotics supplements
lokacin juna biyu na rage hadarin kamuwa da jijjiga, ciwon suger na masu ciki,
matsalar borin jini da infection
🔹-Legumes, sunhada lentils,
wake, peas, chickpeas, soybeans, peanuts. Wadannan rukunai suna dauke da folate
wanda munsan ana ba masu juna biyu a asibiti. Rashin isasshen wannan sinadarin
yana iya kawo matsalar neural tube defects, yanasa a haifi jinjiri wanda
karami, yanasa jariri yarika yawan rashin lafiya ko zuwa girman sa ne
🔹-Sweet potatoes, nada
matukar amfani saboda yana kunshe da vitamin A wanda mai juna biyu ke bukatar
sa matuka kodan girman jariri ta
🔹-Salmon, salmon nada
mahimmanci musamman ga masu ciki saboda Omega 3 fatty acids saboda yana kara
gina lafiya kwalwa na yaro yazama mai fahimta sosai dakuma samun lafiyayye
idanun jariri sosai
Ana iyasamu Omega 3 fatty acids a
seafoods, amma kada a wuce sau biyu a sati. Wani karin mahimmanci ga samun
Omega 3 fatty acids shine yana kara yawan jini na EPA da DHA, sannan lafiyar
kashi da samun garkuwa jiki mai inganci
🔹-Eggs, kwai yanada amfani
ga jiki kowa yasani, sannan wani abu da mutane basu saniba shine kwai yana
dauke da wani sinadari mai suna choline wanda yake kara girma jiki da kwakwalwa
ga kowa da abinda yake cikin ciki uwarsa.
Rashin wannan sinadarin na choline
na ragema yaro kaifin basira kuma a cikin kwai daya dukansa akwai choline
samada 113 mg wanda daidai yakeda 25%na RDI na mai juna biyu kwatankwacin 450mg
🔹-Brocolli, dark green
leafy, wadannan abubuwa dasuka kunshi kale da spinach suna kunshe da abubuwa da
masu ciki ke bukata matuka daga cikin amfani su shine suna rage yawan ciwon
ciki gamai juna biyu dakuma haihuwa yaro da nauyin sa baikai ba
🔹-wasu daga cikin abincin
dasuke da amfani sosai ga mai ciki sunhada lean meat, fish liver oil, berries,
hatsi, avocado, busasshen kayan marmari irin dabino, da shan ruwa sosai.✍ *DR SHUAIBU MB*
Comments
Post a Comment