**AMFANIN MADARAR SHANU GA LAFIYAR MU**



DR SHUAIBU MB(KIWON LAFIYA)
**DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑**

**AMFANIN MADARAR SHANU GA LAFIYAR MU**

 Madarar shanu tana dauke da sinadarai dayawa dasuke taimaka ma mutane wajen lafiyarsu, saidai gawasu mutane da sukeda da karancin lactose bai kamata suyi amfani da ita ba kamar kananan yara saboda suger dayake cikinta yana bukatar lactose don narkewa kamar yadda yakamata dakuma manyan da suma sukeda matsalar lactose dinnan wanda za aga abinci baya saurin narkewa bayan anci sannan akwai masu allergy na madara wadanda da sunsha madara jikinsu ko cikin su yana bada reaction suma baikamata sunsha ba, Maimakon madara akwai waken suya da almond da zasu iya maye gurbin ta

 **AMFANINTA GA HAKORI**

 Madarar shanu hanya ce tasamun sinadarin calcium sinadarin dayake da matuka amfani ga hakori da kashi
Madara shanu tanada sinadarin calcium da vitamin D wadanda suke da amfani sosai ga lafiya kashi dakuma kare kashi daga amasanin kashi.

 ***Sauran hanyoyin da akebi wajen kariya daga ciwon kashi sune motsa jiki, gujewa shan taba, cin abinci mai kyau dayake da karancin sodium dakuma yawan potassium

**Sannan shikuma vitamin D bayan cikin madarar shanun anasamun sa a hantsi idan mutum nashan hantsi.

**AMFANINTA GA LAFIYAR ZUCIYA**

 Madarar shanu hanya ce tasamun sinadarin potassium wanda yake taimakawa wajen rage hawanjini. Yawan amfani da abubuwa masu sinadarin potassium dakuma rage abubuwa masu sinadarin sodium na rage hadarin kamuwa da matsala zuciya kokuma idan akwai ta asamu saukin ta.
Su wadannan abubuwa dasuke daukeda sinadarin potassium din dayawa sunhada madarar shanu, tomato, lima beans, Ayaba, oranges, prunes, da yoghurt. Saidai wani abu mai kama da drama shine idan potassium din kuma yacika yawa yana iya haddasa ciwon da akace yana magani ko kariya daga samunshi watau matsala zuciya.
Yawanci akayi amfani da 4069mg ko 1000mg a rana kokuma de a tuntubi masana kafin afara sha.Kada amanta madarar shanu nada kitse da mai dazai iya cutarwa.

 **MADARAR SHANU GA CANCER**

 Dayake sinadarin vitamin D yanada amfani wajen daidaita matsalar cancer dakuma kariya daga gareta kuma ita madarar shanu tanada wannan sinadarin, kuma dayake akwai wasu wurare da hantsi watau hasken rana baya kaiwa kuma kila cancer acan take kuma munsani tana bukatar wannan sinadarin don warkarwa to shan madarar shanu zata taimaka don isar sinadarin.

 Sannan yawan samun sinadarin calcium da lactose daga ababen nau'in madara yanada kyau wajen kariya daga ovarian cancer.

 **AMFANINTA AFANNIN DAMUWA (DESPRESSED)**

 Karancin sinadarin vitamin D yanada haifarda samarda hormones na serotonin wanda yakeda alaqa da damuwa, da yawan bacin rai, da matsalar rashin dandano da matsalar bacci. Sannan karancin vitamin D yanada alaqa da damuwa, yawan kasala da matsaloli da akesamu lokacin al'adar mace na ciwace ciwace, saboda ita kuma madarar shanu nada wannan sinadarin dayawa a ciki.

 **GIRMAN JIKI**

 Madarar shanu tana sanya girma jiki musamman ga yara dasuka fara tasawa saboda yawan sinadarin protein dake akwai a ciki dakuma sinadaran amino acids duka akwai shi a cikin madarar shanu din.

 🤔Akwai de sauran amfani da take dashi amma ayi da kula domin intayi yawa tana da illa gaskiya.

Allah yabamu lafiya mai amfani.

Comments