BARIN CIKI 1




DR SHUAIBI MB(KIWON LAFIYA)
***DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑***

***BARIN CIKI***1⃣

 Dayawa ana maganar matsalar barin ciki har wasuma sukeda shakkun ko zasu iyasamun wani ciki bayan yawan barin ciki dasuka yi famadashi a baya, ana iya cewa yawan barin ciki idan mace barin cikinta yakai ukku kuma daga farko ciki zuwa wata ukku, saboda duk cikin dayakai wata hudu ba bari ciki bane.

*** BANBANCIN BARIN CIKI DA MUTUWAR BABY A CIKI***

 Yakamata a banbance minene barin ciki minene mutuwar baby a ciki ciki, duk cikin dayakai wata hudu to baby halittarsa ta, amma kasada haka shine akwai tawaya watau ba mutum bane amma idan wata hudune to mutuwar baby kenan a cikin ciki, Dayawa mata masu barin ciki sukan damu idan sukaje asibiti bayan barin ciki ba ayi masu kome ba kila sai magungunna karin jini kawai kokuma wankin ciki, eh hakane ana fara bincike ne agano matsalar dake sawa ana yin yawan barin. Akwai dalillai dayawa da sukan kawo matsalar yin bari wasu za a iya magance ta hanyar magungunna ko allurai ko kuma daure bakin mahaifa ko kuma shawarwari dasauransu.Abin takaici Abin tausayi kuma kashi 50-75% na yawan barinda akeyi ko anyi bincike ba acika gane matsalar dake kawo suba, amma ga abubuwanda suke kawo barin ko yawan barin ciki a likitancin zamani

 1⃣Kusan kishi 50% anasamun matsalar mahaifa ne saboda tsarin mahaifa din

2⃣-Akwai matsalar bakin mahaifa yawanci bata iya daukar baby dayakai wasu watanni kamar ukku, amma ana daurewa idan yakai wata ukku

3⃣ -Akwai banbancin kwayoyi halitta, yawanci tsakanin uwa da babyn kokuma tsakanin miji da mata ko da babyn ba kowane lokaci bane akesamun matsalar ga uwa ko ga babyn ba wani lokaci anasamun matsalar ne wajen uba. Saboda haka idan akasamu irin wannan alhmdlh ynz ana treatment din matsalar

4⃣ -Shekaru, akan iyasamu wannan matsalar yayinda germs cells sukayi rauni saboda Shekaru

5⃣ -karancin sinadarin progestrone a cikin jini uwa na haddasa wannan damuwar anma shima alhamdulillah ana treatment din matsalar

6⃣ -Wani lokacin mace nada ciwon suger batareda tasani ba kokuma tasani amma ba ayi treatment sosai ba shima yanasa yawan zubewar ciki

7⃣-Akwai matsalar pcos inzaku tuna lokacinda nayi magana akan matsalar yawan gashi ga mace har a wuraren da mata basu fitarda gashi amma wasu matan na fiddawa ko irin mata masu muryar maza ko masu wasu kamannu de na maza wanda suka fito sosai don duk mace nada wata siffa ko yaya take ta maza hakama maza suma saidai mutum yace bai luraba.To akwai matanda hormones din na maza sunyi yawa a cikin jininsu suma za aga suna yawan bari

8⃣ -Matsalar gudajin jini ga mace

9⃣-Matsalar kariya da mahaifa ke rasawa wani lokacin

 1⃣0⃣-Yawan Natural killer cells, wasu halittune dake cikin mahaifa idan sukayi yawa suna haifarda haka ga macenda ta tabayin barin.

*** TREATMENT***

Akwai karin mahaifa, Akwai infection cututtuka irinsu malaria, typhoid, akwai matsalar yanayin rayuwa irinsu shan cigarrete  barasa da kwayoyi, dasauransu de.Ana treatment mafi yawan dalillai dasuke kawo matsalar yawan barin ciki, kuma duk mace mai wannan damuwar haryanzu tanada damar samun ciki ta haihu da kusan kaso 65% insha Allah.Baikamata ace tunanin mace mai wannan matsalar ba yatafi dacewa ai ita ta hakura ma shikenan bata samun haihuwa a'a akwai dama agaba insha Allah aje asibiti akuma bada hadin kai da kara hakuri da yin addua a matsayin mu na musulmai munsan ba abinda yafi karfin Allah.Akwai hanyoyi na gida da mace zata iya bi wajen ganin ta taimaka anshawo kan matsalar.

1⃣ -Arika samun lafiyayyen abinci kamarsu fruits, vegetables, kifi, manzaitun, kur kur a cikin girki, hatsi

 2⃣-A yawaita amfani da itatuwa masu colors kamarsu cherries, berries, tomato, carrots, dasu tsanwayen ganyayyaki

 3⃣-Ayi kokari rage kiba ko nauyi inyayi yawa

4⃣-idan akasamu cikin inde ba dole ba a kiyaye yin x-rays don yawan yin yana taimakawa wajen zubewar cikin

5⃣-Arika motsa jiki bakin gwalgwado

 6⃣-Ana iya amfani da progestrone cream bayan an tuntubi likita, kinda akwai bukatar awon hormones level kafin amfani dashi

7⃣ -Ana so amfani da abinci dasuke da magnesium da vitamin B6 dayawa cikinsu kamar yellow din tsakiyar kwai, nau'ikan gyada da ganyayyaki masu duhu kamar alayyahu

8⃣-Arika shan ruwa sosai

9⃣-idan mace taga tana yawan bari ta buncika lokacin tana yarinya ko akwai rigakafin da ba ayi mata ba, idan akwai taje tasamu likita wannan duk za ayine kafin samun cikin


1⃣0⃣-Idan akwai stress ayi kokarin ragewa

1⃣1⃣-Ayi gwaje gwaje cututtukan sanyi da ake dauka ta saduwa

1⃣2⃣ -Arika amfani da abubuwa masu vitamin c a ciki kamarsu lemun zaki da tsami da grapefruits

 1⃣3⃣-Yawaita amfani da cold water fish.

My hadu a rubutu nagaba insha Allah.

ALLAH YAKARA LAFIYA MAI AMFANI.

Comments