*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
*BLOOD SUGER* ( *hyperglycaemia*) yawan suger cikin jini
matsala ce datake damun mutane dasuke da ciwon suger, koda masu diabetes 1 ko
2, dakuma mata masu ciki dasuke da gastational diabetes.
Yana samun mutanen da basu da
ciwon suger ma musamman masu wasu cututtuka kamarsu ciwon zuciya ko heart
attack, infection mai tsanani, stroke dasauransu
Ga masu ciwon suger duk yanda zai
kiyaye zai iya samun suger cikin jini yadaga wasu lokutta saidai arika kokarin
treatment saboda barin matsalar batareda treatment ba zai iya jawo wasu
cututtuka.
Wani lokacin kuma yana safka
da kanshi amma idan yahau dayawa kokuma yadade bai sauka ba akwai bukatar
treatment.
Yawan suger cikin jini yadauki
watanni zuwa shekara na iya jawo lalacewar wasu sassan jiki irinsu idanu,
jijiyoyi, jijiyoyi jini da kidney din mutum.
Idan mutum na famada yawan suger
cikin jininsa nawani lokaci mai tsawo yakamata koda yana treatment din diabetes
to ya chanza treatment kuma da life styles watau yanayin tafiyarda rayuwa
*ALAMOMIN SHI*
♦Yawan jin kishirwa da
bushewar baki
♦ Yawan jin fitsari
♦Gajiya ko kasala.
♦ Gani bishi bishi
♦ Ramewa.
♦ Infection irinna bladder watau
mafitsara, fata ko makoshi.
♦ Yawan jin mutum bayada lfy.
♦Idan mutum yana numfashi
zairika jin numfashi na kamshin kayan marmari watau fruits.
Yakamata kowa yarika yawan
awon yawan suger dinda yake cikin jininsa duk bayan watanni domin sanin haki
kanin yawan suger din da ke cikin jinin mutum wanda ake cema HbA1c level
Target na blood suger da ake
bukata ya banbanta tsakanin mutane amma gaskiyar magana shine, idan mutum na
aunawa daga gida normal de zaikama *4-7mmol/1* kafin aci kome bayan anci abinci
da hour biyu kuma yakamata yakama kasada *8.5-9mmol/1*
*MIYAKE KAWO YAWAN SUGER CIKIN
JINI NE*
🔸Stress.
🔸 Rashin lafiya kamar mura.
🔸Cin snacks dayawa tsakanin
meals.
🔸Rashin motsa jiki
🔸 Ga masu ciwon suger kuma
rashin shan magani ko sha ba daidai ba.
🔸Yawan treatment din
karancin suger din.
🔸Amfani da magungunna
nau'ikan steroid medications.
🔸 Yawan suger cikin jini
yana iya samun yara da matsakaita.
Idan mutum yanada diabetes kuma
yanada alamun ko aka tabbatarda yanada hyperglycaemia to yacanza treatment
yakamata a Chanza abinci,
Chanza abinci shine misali a
guji irinsu cakes da suger drinks.
Rika shan fruits da basuda
suger cikin su sosai, zai taimaka wajen magance matsalar rashin ruwan jiki.
Yawan motsa jiki musamman
tafiya akalla a rana ta minti 30
Idan ana amfani da insulin a
dan daga amma tareda taimakon likita.
Akwai wani magani mai suna
*cellgeravity* naga ana amfani dashi sosai yana da kyau sosai.
Idan akaji wadannan abubuwa a jiki
sai ayi sauri aje asibiti sune kamar :-
🔹 Yawan jin rashin lafiya
🔹Ciwon ciki da gudawa.
🔹 Saurin yin numfashi
🔹Zazzabi mai zafi daya
kai 38c ko samada haka
🔹Alamomin rashin
isasshen ruwan jiki kamar yawan ciwon kai, bushewar fata, kasala, yawan bugun
zuciya
Kasa tsayuwa nawani lokaci mai
tsawo.
✍
*DR SHUAIBU MB*
Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com
ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com
Comments
Post a Comment