CIWON CANCER***1



DR. SHUAIBU MB(KIWON LAFIYA🚑🚑)
***DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑

***CIWON CANCER***1⃣

 Cancer kamar yadda muka santa da hausa anace mata cutar daji, a likitance ana nufin duk yawaitar ko karuwar wasu kwayoyi da ba kan ka'ida suke ba kuma wadanda aka kasa ko suka gagari ashawo kansu bawai a wani sashe na jiki ba a 'a kowane sashe, akwai rabe raben cancer samada 200. Dukwani abu dazai sa koya kara yawaitar kwayoyin halitta na jiki ba akan ka' ida ba to zai jawo cancer.
      Akwai alamomi dasuke taimakawa wajen gane cutar cancer kamar sauran cututtuka saidai kowanne cancer Akwai irin nata amma akwai inda suka hadu watau sukayi tarayya a kamannu kamar mutuwar jiki, rama ko ramewa, tari, chanjin fata, fitarda jini kota baki kota dubura ko gaba, chanjin murya, zazabi, ciwon naman jiki dasauransu. Zamu dauki cancer NONO muyi bayani.

***CANCER MAMA***

 Cancer MAMA takasu kishi kishi itama kuma ba mace kawai take samuba harma maza  kuma abuce shu'uma don tana iya bazuwa har sauran sassan jiki ma, kuma alamomin ta data mata dana maza dayawa suna kamancece niya da juna kamar, fitarda ruwa daga kan nono, yamutsewar fatar nono, ko kullutu a cikin nono, ko chanza color fatar nono duka alamune nata data mata data mazan kuma tana iya kama mutum a kowace shekaru saidai su maza tafi kama yan samada shekaru 60 a duniya.

 Wasu nau'ikan na cancer din sunzama ruwan dare saboda yawaitarsu Wasu kuma basu cika samun mutane ba, sannan Wasu kuma nau'ikan cancer biyu ko fiyema na samun su lokaci daya.

1⃣-Ductal carcinoma, wannan nau'in Cancer nono ce datake kama bututu nono kuma bata yaduwa zuwa ga sauran sassan jikin mutum.

2⃣-Invasive ductal carcinoma, watau cancer yarcin zalin wadda take kama gland watau sashen da yake samarda ruwan nono, yawanci tana cin zalin wani bangare ne na cutar sankara

 3⃣-paget's disease of the nipples, wadda ke farawa daga bututu saita yadu zuwa kan nono harta kama tsokarda ke gewayen kan nonon ta canza ma fatar color.

 4⃣-Triple negative breast cancer, wadda tafi kama mata masu kananan shekaru

 Akwai de rabe rabe ta ita cancer din nono din kusan har 15.

 CANCER NONO, bawani abu takamamme da za ace yana kawota kokuma tsayayyen abu, amma akwai abubuwa dayawa da a iya cewa mutum yana kan hadarin kamuwa da ita misali.

 1⃣Shekaru

 2⃣Gado

 3⃣Personal history, ace kila ta tabayi ga dayan nonon

 4⃣Family history, ace ai su gidansu suna samunta

5⃣ Mata dasuka fara al'adarsu tunda wuri kasada shekaru 12 ko wadanda menoupouse dinsu yazo bayan shekaru 55

 6⃣Mata masu nono dayawa ko babba

 7⃣Mata da aka yawaita yima chest hoto ko gashin kirji dayawa

8⃣ Matanda basu taba haihuwa ba ko sunhaihu farko sunada shekaru 30 ko samada 30

 9⃣Shayarwa harzuwa shekara daya da rabi zuwa kasa da biyu na rage hadarun kamuwa da ita

1⃣0⃣Kiba ko nauyi na mace.

 1⃣1⃣Dadewa ana amfani da kwayoyi na tsarin iyali

1⃣2⃣ Mata dasuke amfani da barasa

1⃣3⃣ Mata dasuke motsa jiki nada karancin hadarin kamuwa da ita.

 Akwai maganganu kan deoderant na hamitta ko yana kawo ta amma nide ban tabbatarba.

ALLAH YAKAREMU

Comments