*CIWON NÀMA(GOUT)*



**DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*                            
 *CIWON NÀMA(GOUT)*       Gout(ciwon nama), wani nau'in ciwon kashi gabobi ne ko amasanin gabobi dayake haifarda ciwo, zafi  kumburi da girman gabobi. Yawanci yafi shafar gabobi na babban dan yatsa kafa,
  Gout yana saurin kai hari ga gabobi kuma yarika dawowa akai akai a hankali harya kaiga ya taba tsokoki dake wajen saisu kumbura, a lokutta baya yafi addabar maza fiyeda mata, yawanci mata saisu gama jinin al'adarsu duka a rayiwarsu sannan yafi damunsu watau *menopouse*
 Gout yakasu kishi kishi, daga Viki akwai:
 1⃣ *Asymptomatic hyperuricemia* , wannan nau'in na ciwo gout yana faruwa batareda wani alamomin ko daya ba kawai uric acids ne zai ginu a cikin tsoka yana iya yin barna ga tsokar amma ba sosai ba, yawanci wannan basai anyi treatment ba shawarwari ne kawai yadda zai kauce ma abubuwanda suke kawo shi ko kara tadashi
 2⃣ **Acute gout**  wannan nau'in ciwon gout yana faruwa ne lokacin da *uric acids* din yashiga ciki tsoka lokaci daya ya haifarda kumburi da ciwo a wajen wanda ake kira flare yawanci ciwon yakan kai kwanaki ukku zuwa goma kafin yafara rage radadi da kumburi amma yana iya ta'azzara yarika zafi sosai kuma yawuce kwanaki goma saboda stress, ko ruwan sanyi ko wasu magungunna da ake anfani dasu
 3⃣ *Interval/ intercritical gout* , wannan nau'in na ciwo gout shikuma yana faruwa ne a tsakankanin lokacin da uric acids yakawo hari, shine wanda yakan dauki watanni ko shekara inba ayi komeba saiya haifarda ciwon gout din mai tsanani kuma na lokaci mai tsawo
 4⃣- *Chronic tophaceous gout,* wannan nau'in na ciwo gout shine mafi muni daga cikin nau'ikan ciwo gout da akeda su shike haifarda lalacewar tsoka ta dindin dakuma kidney
 Wadanda yasamu wannan shine yake famada tsakanin ciwon gabobi da kumburi musamman a wurare da sukeda sanyi na gabobi
 Idan ba a dauki matakan warkarda shi ba shine yakan kai shekara goma kuma a lokacin ne zai yima mutum illa sosai
  5⃣ *pseudogout* wannan nau'in na ciwo gout ne koda yake shi akwai rudu tattare dashi domin wasu na ganin ba gout bane kawai kama yake da gout
 Babban banbancin su da gout shine shi pseudogout ba uric acids bane ke haifarda shiba, *calcium phosphate crystal* ne ke haifarda shi, Idan ba a dauki matakan warkarda shi ba shine yakan kai shekara goma kuma a lokacin ne zai yima mutum illa sosai
 Sannan kuma *treatment* din yana banbanta dana gout
  *ABUBUWANDA SUKE KAWO GOUT*      Ciwon gout yana faruwa ne lokacin da yawan sinadarin uric acids a cikin jini. *Uric acids* yana samuwa ne lokacin da *purines chemical* sukayi breaking down wanda akesamun su cikin wasu abincin kamar jan nama, naman kaji da seafoods watau abincin teku.
 Yawanci uric acids yana narkewa ne a cikin jini saiya karu cikin fitsari zuwa kidney shiyasa yake shafar kidney, idan yayi yawa kuma bai narke cikin jini ba saiya zama ya ginu kamar allura saiya haifarda kumburi da ciwo a gabobi dakuma tsokoki dake wajen.
 Akwai mutane dasuka fi hadarin kamuwa dashi misali kamar
♦ -maza sunfi mata hadarin kamuwa dashi, amma bayan menopouse mata sunfi hadarin kamuwa dashi
 ♦shekaru suna tasiri sosai wajen samunsa
♦-Gado, idan akwai iyaye dasuke dashi to akwai hadarin kamuwa dashi ga yayansu
♦Amfani da wasu nau'in magungunna shima mutum yana kan hadarin kamuwa dashi
♦-Tsarin tafiyar da rayuwa kamar mutane masu shan barasa dakuma mutane masu chin *purines foods* watau irinsu nama dasauransu
 ♦-kiba da maiko a jiki suma suna kara zama hadarin kamuwa dashi
♦Rauni ko surgery a gabobi suma hadarine wajen kamuwa dashi
Sauran matsaloli na lafiya kamar karancin renal na koda, matsalar koda, hawanjini da ciwon suger duk suna zama hadari wajen kamuwa da ciwon gout
 *ALAMOMIN GOUT* Dayawa yakanzo batareda wata nuna alama ba yawanci yana tasowa ne a tsakiyar dare, yawanci alamomin sune zafi sosai da kumburi da wurin yayi ja ga gabobi musamman gabar babban dan yatsa kafa, amma yakan shafi gwiwa hannu data kafa  yatsu, harda kugu.
 *KARIYA,* za a iya kare kai ta hanyar yawaita shan ruwa litre 2-4 a rana, a guji shan barasa dakuma ayi kokari ayi maintainning lafiyayyar kiba ba kiba datake ta cuta ba, sannan arage cin abinci masu wannan purines chemical dinba,
 Abinda mutum zai iyayi idan matsalar gout ta sameshi shine, a kulada abinci domin shine babba maganin gout, duk mai gout yayi kokarin kaucema nau'ikan abinci dasuke da karancin sinadarin carbohydrate. Hikimar anan shine amfani da nau'in abinci masu karancin sinadarin carbohydrate zaisa jiki yakasa kona runbun kitse a jiki saikuma jiki yasaki abinda akecema ketones a cikin koramun jini
 Wannan shizai haifarda ketosone din saiyayi sama saiya haifarda abinda akecema ketosis wannan saiya haifarda yawan uric acids a cikin jinin mutum. Saboda haka kiyaye cin abinci masu dauke da karancin sinadarin carbohydrate dakuma wadanda sukeda purines chemical abubuwa ne dasune gaba wajen warkarda matsalar gout
Wasu daga cikin abincin dasuke da purines chemical a ciki da ya kamata a kaurace ma wa sunhada, sardines, hanta, naman kai musamman kwalwa, busasshen wake da peas, kidney na kaji, aspharagus, sweetbreads, kashi kaji, jan nama musamman na manyan dabbobi, mushroom,
 Wadannan abinci basuna kara yawan uric acids bane saidai suna kara ta'azzara ciwon sosai sannan akwai wasu abincin suma da suke da wannan purines chemical din a cikinsu dukda de wasu na ganin su nasu baya ta'azzara ciwon kamar dukwani abinci nau'in protein irinsu wake, kwai, dasauran su.
 Sannan daga cikin vegetables da fruits ma akwai wadanda sukeda purines a cikinsu saidai su nasu baya tasiri akan uric acids kamarsu hatsi, nau'in gyada, legumes, da kayan marmari dasukeda zaki kadan, coffee, vitamin C dukkansu sunama rage yawan hadarin kamuwa da gout ne
*** Ga wasu jerin abubuwa da zasu taimaka wajen warkarda matsalar gout insha Allah a gida
1⃣-Juice na cherries ko tart cherry na kwana biyu ko sour dinsa ko mai zskinsa ko red ko black dinsa ko danyansa yana tasiri sosai akan gout na kwana biyu kawai ya isa
2⃣-kullum aci abinci masu sinadarin magnesium sosai a cikinsu  kamar dark chocolate, avocado, tofu, yayan kabewa  alkama, Ayaba, spanish
 3⃣-Ginger, asamu sauyar ginger din amma garinta cokali daya babba adafa ta sosai sai asamu towel a tsoma a ciki sai a dora akan wurinda gout din yake minti 15-30 a cire kullum sau daya har sati biyu amma afara jarabawa agani idan fatar mutum zata iya dauka saboda wasu yanasa irritation akai
 4⃣- *Epsom salt* wannan gishiri na wanka idan aka sanya kamar marfi biyar cikin ruwa sai arika tsoma gabar dake ciwon ciki zuwa minti 20 za arika jin saukin ciwon
 Kokuma asamu garin sauyar ginger din cokali biyu adafa ta zuwa minti goma sai asha cup ukku a rana daya dasafe daya da rana daya da daddare
 5⃣-Amfani da banana daya da apple daya a rana zasu taimaka amma kada asamasu komi
6⃣-Arika tsoma gabar dake ciwon a cikin ruwan dumi ko na sanyi zai taimaka. 

Comments