*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑* *CIWON ZUCIYA*
Idan akace ciwon zuciya ana nufin
ciwo daga ko ina daga zuciya watau anyi jimla ne domin ciwon zuciya yakasu
kishi kishi, tundaga wanda yashafi kasan lemar zuciya daya hada da jijiyoyi
jini dasuke kawo mata jini, zuwa abinda yashafi aikinta, bugawarta dasauransu,
sai kuma abinda yashafi gazawarta shima wani bangare ne.
Idan akace ciwon zuciya za a
iya cema cadiovascular disease wanda ciwone dayake dade ko rufe jijiyoyin jini
na zuciya wanda yake haifarda heart attacks, akwai abinda yashafi kirji watau
angina dakuma abinda ya shafi stroke sauran sunhada ciwon dayake kama tsokoki
da rhythm dasauran nau'ikan cututtukan zuciya.
Dayawa cututtukan zuciya ana
treatment dinsu batareda magungunna ba saidai da yanayi na tsarin rayuwar mutum
tayau da kullum.
Na fadi rabe raben cututtukan zuciya
amma ya za ayi agane wanene yake damun mutum kuma ta wace hanya za abi agane?.
Akwai alamomin kowace irin cutar zuciya da irin abubuwanda take zuwa dasu
1⃣ *CIWON ZUCIYA DAYA SHAFI JIJIYOYI
JINI NA ZUCIYA,* Dukda alamomi ciwon na banbanta ne tsakanin maza da mata
misali kamar maza suna ciwon kirji sukuma mata suna famada karancin ko numfashi
da kyal, tashin zuciya da kasala.
Sune ace ciwon kirji, daurewar kirji,
sukar kirji dade dukwani rashin jindadi daga kirji.
Sannan akwai matsalar numfashi
da za aji yana karanci.
Ciwon, kumburin, gajiya ko jin
sanyi ga kafa da kafada.
Ciwon wuya, mummuke, makoshi, saman
ciki da baya.
2⃣ *CIWON ZUCIYA DAYA SHAFI YANAYIN
BUGAWAR TA,* shikuma wannan ciwo zuciya ne dayake zuwa da halba zuciya da sauri
ko kadan. Alamominsa sune, jiri, halbawar zuciya dasauri ko a hankali, gani
buji buji, ciwon kirji, faduwa kusan kamar suma
3⃣ *CIWON ZUCIYA DAYA SHAFI NA
NAKASA KO TAWAYAR ZUCIYA,* Shi wannan ciwon zuciya ana haihuwar mutum dashine,
kwanaki kadan bayan haihuwar jariri ake gane matsalar ta hanyar kokewar fata,
ko fata tazama blue, kumburin kafa, ciki da wajen ido, karancin numfashi yayin
shayarda jariri.
Amma akwai wadanda ba aganewa
sai sun fara girma wasuma sai sun zama manya idan sukazo da matsalar karancin
numfashi idan sukayi wani dan aiki, motsa jiki, kumburin hannu, tafi da idon
kafa
4⃣ *CIWON ZUCIYA DAYAKE DA ALAKA DA
GAZAWAR TSOKOKI NA ZUCIYA* Shikuma wannan matsalar tana zuwane da alamomi kamar
bugawar zuciyar dasauri in mutum yazo hutawa, ko yagama wani aiki, jiri, buji
buji, yawan gajiya, kumburin hannu, tafi da idon kafa.
5⃣ *CIWON ZUCIYA DAYAZO DALILIN
INFECTION NA ZUCIYA*,Endorcaditis infection ne dayake ciki daya raba chambers
na zuciya da valves.
Akwai alamominsa kamar zazzabi,
kasala, kumburi kafa da ciki, busasshen tari, kuraje a fata ko spots, karancin
numfashi.
6⃣ *CIWON ZUCIYA DAYA SHAFI BAWULOLI
(VALVES)*, zuciya kamar mota ce itama tanada bawuloli amma ita nata guda hudu
ne wadanda suke budewa su rufe suna ummurtar gudanar jini zuwa zuciya.
To suna lalacewa, kode su
tsuke, ko su rika leaking, kokuma suki rufewa insun bude.
Alamomin wannan sune, kasala,
karancin numfashi, yawan bugawar zuciya, kumburin tafin kafa da idon kafa,
ciwon kirji da wani lokaci faduwa. zamudakata sai rubutu nagaba.✍ *DR SHUAIBU MB*
Comments
Post a Comment