*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑
*(kiwonlafiya51@gmail.com) *CUTAR BASUR*
Cutace da jijiyar cikin
takashi keyi dakuma duburar kasa, akwai abubuwa dasuke kawo basur wasu sananni
ne wasukuma ba sanannuba, daga cikin sanannun yahada da kuntata lokacin bayan
gida kokuma pressure ga masu juna biyu
Basur yakasu kishi ukku akwai
wanda yake cikin dubura na can ciki akwai kuma wanda yake faruwa kasan fata
watau na waje.
Basur matsala ce data zama
ruwan dare kusan duk cikin mutum hudu anasamun mutum ukku dasuke da Basur daga
lokaci zuwa lokaci. Wani lokacin basur na zuwa batareda nuna wata alama ba,
amma wani lokacin yana haifarda kaikayi, rashin natsuwa, zubarda jini.
Sannan akwai dayan irin Basur dinda
wanda shikuma baicika faruwa ba inda jini ke taruwa yazama gudajin jini amma
bawani hadari gareshi ba ana yade shi ko a tsanar dashi
*ALAMOMIN BASUR*
🔹Yin bayan gida tareda jini,
za aganshi brown color a ciki ko jikin toilet paper.
🔹Kaikayi ko dan radadi a
wajen takashi.
🔹ciwo ko rashin natsuwa
🔹Kumburi wajen takashi.
🔹Dan kurji ko maruru wajen
takashi
Ayi hakuri za aji ina amfani da
kalman takashi, mu a hausa inmukace takashi ana nufin anus da turanci amma ance
dubura ana nufin rectum, ina takashi itace a farko dubura kuma wannan hanji da
bayan gida yake fita jikinsa shiyasa nake kiransu da haka don a fahimta saboda
shima basur din akwai na waje dana ciki.
Basur na ciki shine wanda yake kama
dubura ba ganinshi akeba ko tabashi akeba amma za aji kuntata lokacin
bayan gida saikuma aga alamun jini a cikin bayan gidan,
Yawanci kuntatar shine ke haifarda
fitar baya ta hanyar takashi
-Basur na waje, shikuma yana faruwa
a kalkashin fata ne a wajen takashi din saiya haifarda kaikayi, wani lokacin da
bleeding
Basur wanda yake haifarda gudajin
jini watau (thrombosed)
*ABUBUWA DASUKAFI KAWO BASUR*
Nace akwai abubuwa da akasani da
wadanda ba asani ba, sannan akwai abubuwa dasuke kara kawo shi kuma, daga cikin
wasu sune :
🔸 Kuntata lokacin yin bayan
gida
🔸Kiba. 🔸Dadewa
zaune akan toilet
🔸Juna biyu
🔸Saduwa ta dubura
🔸Karancin cin abinci fiber.
*HANYOYIN KARIYA*
♦Arika amfani da abinci masu zare da
dussa sosai cikin su, kayan marmari, kayan lambu, wanda wadannan zasu taimaka
wajen yin bayan gida mai laushi
♦Shan ruwa sosai matuka.
Akwai supplements na fiber, mace
zatayi amfani da 25 grm a rana namiji kuma 38 grm a rana amma dole asha ruwa
sosai
♦Nishi mai karfi da yunkuri mai
karfi yana assasa matsalar
♦Yawan rike bayan gida nasa yakara
tauri ya bushe saiya zama ansha wahala lokacin yinsa
♦Motsa jiki yana taimakawa
♦A guji dadewa akan bayi na tsawon
lokaci
♦Ana iya amfani da ruwan sanyi ko
ice block
♦Sitz bath
♦Yawan tsaftace area dinda ruwan
dimi
♦Kada ayi amfani da busassar toilet
paper da ba a dan jikata ba.✍
*DR SHUAIBU MB*
Comments
Post a Comment