*CUTAR SICKLE CELL*



*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
 *CUTAR SICKLE CELL*          
     Sickle cells anemia laluri ne ko cuta ce da ake Gado siffar anemia watau yanayi da karfin ko yawan jinin dayake tafiyar da oxygen zuwa ga tsokoki yake raguwa kode saboda karancin halittu jini na jajjye watau red blood cells kokuma saboda karancin hemoglobin watau iron daya kunshi wasu abubuwa cikin red blood cells dasuke daukar ko dakon oxygen daga hunhu zuwa sauran sassan jikin mutum. Yawanci su wadannan kwayoyi halittu jini din jajjaye watau red blood cells sunada laushi kuma zagayayyi ne ta yadda cikin sauki suke tafiya cikin jijiyoyin jini, amma ga mutane masu sickler wadannan red blood cells din saisu zama masu tauri, danko dakuma shape din saiya zama kamar na karamin wata saiya zama red blood cells din sun makale cikin jijiyo jini wadda saiya haifarda karancin ko tafiyar hawainiya ko su dade jini da oxygen daga isa ga sauran sassan jiki
**ALAMOMIN SICKLER**
♦-Anemia, yawanci ko dayawa ma su wadannan kwayoyi halittu jini din jajjaye watau red blood cells suna rayuwa ne cikin kwanaki 120 saisu bukaci a maye gurbin su da wasu, to su masu sickler din nasu basu wuce kwanaki 10-20 saisu mutu saisu bar gibin rashin su ga mutum to idan akasamu wannan yankewar jikin mutum bazai samu oxygen ba wanda jiki ke bukatar sa don yasamu karfi shine rashin su din saiya haifarda kasala ko mutuwar jiki sosai
♦-Ciwo, kumburi hannu da kafafuwa, wanda wannan rufewar ko dadewar da jijiyo jini sukayi ta haifar
♦ -Jin zafi daban daban, wanda da turanci ake kira crises shine babban alamar sickler, ciwon yana karuwa ne yayinda wadannan kwayoyi halittu jini din jajjaye dasuka koma kamar jariri wata suka dade kananan jijiyoyin jini zuwa ga kirji, ciki dakuma gabobi sai ciwon yarika zuwa daga kasusuwa.
    Ciwon yana kamawa daga wasu hours zuwa satittika, wasu suna samun ciwon daban daban amma bada yawa ba, wasukuma suna samun nasu crises din yana yawa wasukuma har shekara ma suna famada crises daban daban harta kaiga sai an kwantarda su a asibiti. Wasu matsakaita masu shekaru da wasu manya masu sickler na famada ciwo mai tsanani sosai ta inba hankali akayi ba zai kaiga lalacewar gabobi da kasusuwa, ulcers dawasu matsalolin
♦-Yawan samun infection, sickle cells din suna lalata duk wata gaba datake fada da infection a cikin jiki, saboda mai sickler yake zama baida wata kariya ga infections. Shiyasa akeba jarirai da yara kanana vaccines don samun kariya daga manya manyan infections dazasu iya sanadiyar rasa rayuwakansu
♦-Jinkirin girma, *red blood cells* wadannan kwayoyi halittu jini din jajjaye suna ba jiki *oxygen* dakuma wasu sinadarai don jiki ya girma, to karancin su wadannan halittu jini saisu hana jariri ko yaro girma sukuma ga wadanda suka tasa su hanasu balaga cikin lokaci
♦-Matsala gani, kananan jijiyoyin dasuke samarma idanun masu sickler jinin, sukan rufe ko toshe daga wadannan *sickle cells* din tayadda idanu basu samun isasshen jini saiya haifarda lalacewar retina watau wurinda yakeda alhakin ganin hoto wanda saiya haifarda matsalar gani.
 Yawanci ana gane alamomin ta ga jarirai, idan jariri ka ko yaron ka kaga yana famada wadannan abubuwa to aje asibiti
🔸-Yawan ciwo kuma yarika tsanani, musamman ga ciki, kirji, kashi ko gabobi
🔸 -kumburin ga hannuwa ko ga kafa
-kumburin ciki musamman wurinda yakeda taushi
🔸-Yawan zazzabi wanda infection ke kawo ma masu sickler kuma shine alamar farko ta shigar infection ga masu sickler
 ðŸ”¸-Duhu fata ko idanun suyi fari sosai
 ðŸ”¸-Kokewar fata ko gadajen farce
🔸-kamannu ko alamomin *stroke* watau shanyewar jiki kamarsu, jin barin fuska kamar yagaji, ko kafada, ko kafa, kokuma comfused, ko tafiya ko magana suyima mutum wuya, ko lokaci daya aga ganin yaro na ragewa, ko ciwon kai ko kumburi wanda idan akaga wadannan ko wasu daga ciki a hanzarta zuwa asibiti
 *ABUBUWANDA SUKE KAWO SICKLER*               👉 *autosomal recessive inheritance* , watau tana yaduwa daga wannan karnin mutane zuwa karnin mutane masu zuwa watau ta hanyar Gado kenan wanda uwa ko uba duk zasu turama jaririn da zasu haifa.
Idan daya daga cikin iyaye ne keda su ko yatura ma jariri kenan shine akecema *traits* akwai *sickle cells* din a jikinsa amma duk wadannan alamomin nata ba aganinsu a jikinsa wanda ke nuna zasu iya turama yayansu suma
 Idan aka haifi *sickler* to yanuna duka iyaye nada *sickle cells* a cikin jininsu kenan
 *RIKITARWAR SICKLER*
 Alamomin stroke, ciwon kirji sosai, *pulmonary hypertension* watau hawanjini na hunhu, lalacewar wani bari, ulcer ta kafa, matsalar makanta, *priapism* watau maza masu sickler susamu matsalar mazakutarsu, *gallstones*
 Idan akaga yaro da kamannu da alamomin da aka fada asama sai aje asibiti akwai gwaje gwaje da akeyi don gano haki kanin matsalar.
 *MATAKAI DA AKE DAUKA A GIDA DON SAMUN SAUKIN MATSALOLI DATAKE HAIFARWA*
◼-Arika daurewa ana amfani da kwayoyi folic acids da ake bayarwa a asibiti kullum, dakuma samun lafiyayye abinci masu kara jini
◼-Arika samun isasshen ruwa anasha, saboda rashin isasshen ruwan jiki nakara ma matsalar girma, idan kuma mutum ko yaro na dadewa a cikin zafi ko sanyi yakara shan ruwa sosai
 ◼-A kiyaye shiga inda zafi yake sosai da inda sanyi yake sosai
 ◼-Abubuwa dayakamata masu sickler surika amfani dasu, surika cin abubuwa masu calories dayawa saboda magance ma rama, amfani da fruits da vegetables masu color kamar carrots, mushrooms, asparagus, tomato, da bell peppers, sai abinci masu protein da fats kamar cage free eggs, grass fed beef, salmon, sardines, hanta, da kayan ciki, man kwakwa, madarar kwakwa, man zaitun, avocado, nuts, pinto beans, spinach, lentils, a kiyaye cin abubuwa da basuda calories a ciki, kayan gwangwani ko na roba irinde abincin shagunan nan na yan gayu, da irinsu fast foods dinnan
 ◼-Arika motsa jiki kullum amma bawanda zai iya cutarwa ba kadan kadan
-Sai irinsu vitamin D wanda shan hantsi ma za asameshi anan, calcium, folic acids, man kifi, vitamin B6 da B12, copper, zinc, magnesium
◼ -Arage stress kuma arika samun isasshen bacci da motsa jiki daidai bakin gwalgwado
◼ -A kulada shan ruwa sosai da sosai
 -saboda ciwon gabobi, jiki da kashi, ciki da da kirji kada amaida hankali ga *pain killers* suna iya shafar hanta da kodar mutum, akwai hanyoyin da mutum zai iya management wadannan abubuwa ga masu sickler kamar arika gasa jikin ko cikin ko wadanda ke ciwon da ruwan dumi na mintuna 15 sau ukku a rana, yin wanka da ruwan dumi ko zama cikinsa,
 Sannan *peppermint oil* ana anfani dashi sosai wajen magance wadannan abubuwa ko irritation na fata da akesamu, *frankincense* ma ana anfani dashi wajen magance kumburi a jikin mai sickler, Lavender oil wajen magance stress, orange da grapefruits oils.
Allah yakara mamu lfy amin. **DR SHUAIBU MB*  *1/9/2018*

Comments