Dexamethasone (Sha ka Fashe,)



**DAGA ZQUREN KIWON LAFIYA🚑🚑** *Dexamethasone* wanda ake cema *shaka fashe,* wannan magani yanzu yazama ko ina a tsakankanin mata musamman wadanda sukeson kiba ko halin kaka.🤷🏻‍♀ Minene yasa akayi Dexamethasone watau shaki fashe❓
 đꤔShide Dexamethasone shaki fashe da hausa nagani ne da akayi don magance wasu matsaloli ko lalurori  daga cututtuka da mutane ke famada su misali kamar, amasanin kashi, matsalar numfashi, matsalar allergy watau borin jini, matsalar ciwon zuciya, matsalar ko rashin daidai to na tsarin jini, hormone, garkuwar jiki watau system disorder, ciwon fata, ido, cancer dasauran su
**MINENE ILLAR SHI A TAKAICE**❓🤔
đź‘€-yana chanza ma mutum yanayin gani
♦-yana kumbura mutum
♦sanya yawan zufa
♦-ciwon kai
♦-bacin rai
 ♦-ciwon jiki
♦-kumburin ciki
 ♦-matsalar bacci
♦-Bushewar fata
 ♦-tsanewar fata
♦-Tashin zuciya
♦- Jiri
♦ -kara yin zufa
♦-Dadewa ba a warke rauni ba
♦-Chanza ma ko chanza tsarin wurarenda suke da mai a jiki kamar arm, fuska, wuya, Nono, kugu dasauransu.
 ♦Chanza ma fata color
♦- Yanasa kiba
 ♦-Jinkirin warkarda rauni
♦-Idan mace na shanshi kuma tana shayarwa yana hana yaronta girma
 ♦Yanasa wasu bangarorin jikin mutum tara ko ajiye ruwa kamar gwiwa, hannuwa da ankle
 ♦Kurajen jiki
 Fitowa gashi inda ma baidaceba.
♦ Matsalolin suna da yawa hartakaiga
 Naman jiki aji kamar ana daure shi kuma ga gajiya
 ♦Yawan damuwa, da surutun zuciya marar amfani
♦Gani bishi bishi, ciwon ido dasauran matsalar ido
 ♦Kakkafewa
♦Yin bahaya da jini ko tarin jini
 ♦Yanayin bugawar zuciya yayi sama ko yayi kasa
  ♦Karancin sinadarin potassium wanda saiya haifarda ciwon kafa, kirji, yawan jin kishirwa da fitsari, ♦kyarma da yawan habo, hawanjini.
 Wadannan duk nacikin side effects watau illolin wannan maganin *SHAKI FASHE*

Comments