*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA*🚑🚑
Don Allah kamar macen data haihu jiya da Asuba har xuwa yau nono
bai zoba miyakamata tayi Don yazo.❓
🤔 Matanda suka wuce shekara
30 ko sukayi nauyi dayawa ko kiba dayawa suna samun irin haka wani lokacin ma
sukan wuce kwana daya ruwan nonon baizoba.
Bayan mace ta haihu kafin
ruwan nono yazo yacika nonon akwai wannan dakashin watau ruwan nonon dayake
zuwa farko wanda wasu ke zubarwa yana daukar wani lokacin hour 72(kwanaki uku)
kafin yazo.
Abin damuwar ba ita uwar ba a a
jariri domin tun farko zaifara samun rashin isasshen ruwan jiki dakuma ramewa ko
rage nauyi dukda ba kowace rama ko rage nauyi keda damuwa ba bayan haihuwa
jariri ba.
Damuwa da fargaba na uwar
shima yana kara nisanta ruwan nono din maimakon kila bayan hour 24 saiya kai
hour 48 wasuma har sati daya.
Sannan ga macenda haihuwa ta
ta farko ce wannan itama ba damuwa bane don haka tafaru, amma wadda keda kiba
tafi wadda batada kiba irin wannan Jinkirin na zuwa ruwan nono bayan haihuwa,
wasukuma matan insuka samu dakashin yazo suka shayarda jariri sau biyu cikin
hour 24 saikuma ya dauke
Sannan idan mace nada soreness
na kan nono itama tana iya samun wannan delay din ga shayarwa din.
Idan akwai damuwa kokuma aka kai
hour 72 bai zoba to akwai kwararru akan wannan akwai na unguwa dana asibiti,
sannan abata shawarar ta rungumeshi bada riga jikinsa itama haka watau fatarsa
da tata suna haduwa.
Kokuma ga wasu dabaru na gida
da za a iya inganta zuwa ruwan nonon da wuri basai anje asibiti ba.
🔹 Tafarnuwa idan zata iya ta
tauna tafarnuwa kamar kwara ukku a rana.
🔹Kokuma ta jika
fenugreek cikin ruwa misali kamar kwarori cikin cup daya na ruwa tunda daddare
dasafe sai a juye ruwan da hulbar cikin tukunya adafa su minti biyar acire
atace asha kowace safiya haka.
✍ *DR SHUAIBU MB*
Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail
dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blog site dinmu
kiwonlafiya1.blogspot.com
Comments
Post a Comment