Dr. shekara biyar kenan nayi aure mun fara jima'i amma cikin azaba daga bayama ko yatsa baya shiga cikin gabana haryau
*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
Dr shekara biyar kenan nayi aure mun fara jima'i amma cikin
azaba daga bayama ko yatsa baya shiga cikin gabana haryau.ðŸ˜
🤔Wannan matsanancin
zafin da ake ji shine matakin farko da mace ke gane cewa tanada vaginismus kuma
zafin na zuwane duk lokacinda akazo saka wani abu ciki yawanci da ancire shikenan
wasu kuma ko ancire suna kwanaki suna famada radadi.
Za'aji masu matsalar suna cewa kamar
anyaga su kokuma kamar namiji ya tabo masu karshe bangon gabansu saboda azaba
zafi, koda lokacin pelvic exams da likita zatayi matan suna jin wannan masifar
Haryanzu gaskiya ba wani ko
wasu abubuwa tsayayyu akan minene ke kawo haka dukda wasu nada ra'ayin cewa
anxiety ne watau fargaba amma abin tambayar shine wanene yake zuwa farko
anxiety ko matsalar ta vaginismus?
Wasu matan sunada vaginismus
ga kowane irin abu komin kankantarshi baya shiga amma Wasu matan sunada
vaginismus ne kawai akan Wasu abubuwa misali wani namiji lafiya lau zaiwuce
wani kuma a a, wata kuma hannu komin girmansa zaiwuce amma azzakari komin
karaminsa baya wucewa
*Treatment*
Yawanci a gida mace na iya
magance matsalar, ta hanyar matse da motsa cinyoyin ta da tsokokimta na private
part dinta.
Wannan shine akecema
progressive decentralization farko shine kegel exercise, yadda mace ke
rike fitsari zatarika yi ta matse saita saki second 2-10 saita kara matsewa
haka zaki iyayi kamar sau 20 ko fiye yadda zaki iyayi a lokaci daya.
Bayan kwana ukku, hudu ko biyar
kinayi saiki fara jaraba sanya dan yatsanki daya harzuwa farko abinda zaki tabo
a gabanki amma duk zakiyi haka lokacinda kike wannan matsewa da sakin amma
ayanke farce kuma ranar farko kiyi amfani da versiline mai kyau.
A hankali kina haka wani
lokacin musamman farko farko zakirika jin kin tabo wani abu inkinji zafi ki
cire anjima ma kiyi, insha Allah cikin sati biyu zuwa ukku zakiji kinbude
kokuma ko asibiti akaje akwai pelvic exams daza ayi maki kuma wannan ne za abi
wadannan matakan amma aje asibiti dukda haka.
✍
*DR SHUAIBU MB*
Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com
ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com
Comments
Post a Comment