✍DR
SHUAIBU MB(KIWON LAFIYA)
***DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑***
***DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑***
TAMBAYA1⃣
DR WANNE HADARI C.S KE DASHI❓
DR WANNE HADARI C.S KE DASHI❓
✍Farko
de C. S wata hanya ce da akebi ana haihuwa ta hanyar yima mace aiki ga ciki da
mahaifa, ana C. S ne idan ansamu ciki yazo da rikitattun abubuwa kokuma abaya
haihuwa da mace tayi shima C. S din akayi wanda ba a la'akari da haihuwa ta
vagina bayan C. S abinda akece ma VBAC kuma idan lokacin farko ne sai anfara ko
ana cikin nakuda ba kamar dama wadanda aka taba yimawa ba abaya
DALILIN DAYASA AKE C.S
1⃣Idan nakuda ta tsaya bawani cigaba
misali idan bakin mahaifa yaki budewa yadda yakamata
2⃣ idan baby yana cikin wani hali
misali zuciya babyn na bugawa ba yadda yakamata ba
3⃣-idan baby ta gicce ko baby
yacanza position
4⃣-idan uwa watau placenta ta rufe
bakin mahaifa
5⃣-idan mace na dauke da yan biyu
kokuma ukku ko fiye kuma akaga zaisa asamu matsala giccewa
6⃣-idan mahaifiya nada wata matsala
babba a zuciya ko kwakwalwa
7⃣-idan mace nada babban fibroid
wanda ya obstructing na canal birth
8⃣-idan antaba yima mace aiki a baya
dukda akan jaraba ga wasu ya dangata da wane irin aiki akayi ma mace a baya
ammade ma'aikatan lafiya sukan bada shawarar ayi C. S anan
Wani lokacin mata na wannan lokacin
musamman mata yan boko ko ma'aikata sukan zabi a haihuwa su ta farko ayi masu
C. S wanda ba daidai bane gaskiya saidai idan shi likita yace ba yadda za ayi
sai anyi amma haka kawai don gudun ciwon nakuda ki zabi C. S yanada hadari
akanki inde kinada bukatar haihuwa fiyeda daya saidai in dakinyi wannan ki
hakura. Mata da akayima C. S dayawa suna cikin hadarin samun matsala ta uwa
watau placenta a turanci wanda kuma zai haifarda zubarda jini dayawa daga
karshe yakai ancire mahaifar duka watau hysterectomy a turanci, idan haihuwa
farko ce kike son ayimaki C. S to ki tattauna da likita musulmi yabaki shawara
tsakanin sa ga Allah akan matsalar ko lafiya ki data babyn.
HADARIN C. S
Hadarin dake tattareda C. S yakasu
kishi kishi biyu, hadarin da jariri dakuma hadarin da uwa zata iya samun kanta
HADARIN C.S DA JARIRI ZAI IYA SAMUN
KANSA
1⃣Babyn da aka haifa ta C. S yafi
hadarin kamuwa da matsala numfashi da za aga yana famada shi cikin yan kwanaki
bayan haihuwa sa watau transient tachypnea
2⃣-Surgical injury, ba a cika samu
ba amma ana iyasamu a ji ma babyn rauni a fatarsa
HADARIN C. S DA UWA KAN IYA SAMUN
KANTA A CIKI
1⃣-Infection bayan C. S na mahaifa
bayan C. S watau endometroisis
2⃣-zubarda jini lokacin dakuma bayan
angama C. S din watau postpartum hemorrhage
3⃣-Reaction na ita allurar da akeyi
kafin ayi C. S din
4⃣-Akwai gudajin jini da akesamu
wanda yake block din jini zuwa ga kugu da kafafuwa wanda daga baya mace zataji
tana famada ciwon kugu da kafafuwa wanda yanzu haka dasafen nan akwai wadda ta
tambayeni wai yin C. S dayawa na kawo ciwon kugu da kafa, wanda yana kawowa
bama sai yawan yinsa ba ko daya yana iya kawo haka
5⃣-akwai infection na rauni watau
wurin da aka yanka zai iya samun infection dukda de ya danganta da irin yadda
akai C. S din kinda wata tana bukatar aikin gaggawa ne wata kuma sai anshirya
kome
6⃣-Surgical injury anasamun rauni a
mafitsara watau bladder ko ga hanji dukda gaskiya ba a cika samu ba amma ana
cikin hadarin samun hakan
7⃣-Hadarin da za a iya samun kai ga
ciki mai zuwa, yawan C. S yawan hadarin da mace zata samu kanta ga juna biyu
mai zuwa musamman matsala uwa watau placenta previad dakuma yadda ita uwa watau
placenta zata zama bata tareda bangon mahaifa sosai yadda yakamata watau
placenta accreta,Wanda wannan kuma zai iya haifarda yagewar mahaifa a wurin da
tabon C. S ta baya watau uterus rupture kuma hadarin yafi yawa ga wadda aka
taba yima C. S tace zata haihu dakanta watau ta vagina VBAC.
SHIRI DA AKEYI KAFIN C.S
1⃣-Mataki na farko, akan fadi ma
matarda za ayi ma C. S tayi wanka da daddare da za ayi mata C. S da antiseptic
soap dakuma safiyar da za ayi, sannan a hanata aske gashin mararta ciki hours
24 na C. S saboda gudun infection kunga abinda nake fadamaku akan aske gashin
mara ko, idan akwai bukatar yin askin a asibiti za ayi just dan lokaci kadan
kafin yin C. S din.
Dukda de hanyoyin da akebi wajen yin
C. S yana banbanta yana dangata da miyasa za abi kowace hanya ta gudanarda C. S
amma de mafi yawa anfi bin wadannan matakan
2⃣-za a goge cikin mace, sannan asa
bututu kila ga mafitsara don a fitarda fitsari sai adaura ma mace iv don asamu
isasshen ruwa da magungunna
3⃣-Allurar da akeyi ta kafin C. S
yawanci ana yi akasa ciki don taba mace damar tashi bayan angama wasukuma anayi
a kashin baya musamman a emergency akwai wadda kuma mace najin duk abinda akeyi
akwai kuma wanda ba asani abinda ake sai bayan angama dadan lokaci
LOKACI DA AKEYI C. S DIN
Ana yanka cikin ne akan cikin kuma
yawanci anfi yin yankan ta kwance kuma ana yankan ne daidai inda gashin mara
yafara dukda akwai ire ire yankan dakuma inda ake yankawar,Sai a yanka mahaifar
itama daga kwance daga kasa kasanta dukda de itama akwai ire ire yankan da
akeyi mata ya dangata da inda babyn yake dakuma irin Umatsaloli da cikin yake
dakuma uwa watau placenta tayi,
Yaron zai fito ta mahaifar sabanin ta vagina sai acire shi a goge masa ruwan da yake a bakinsa da hancinsa dasauran abubuwa da yakamata ayi.
Yaron zai fito ta mahaifar sabanin ta vagina sai acire shi a goge masa ruwan da yake a bakinsa da hancinsa dasauran abubuwa da yakamata ayi.
ABINDA AKE YI BAYAN C. S IDAN AN
KOMA GIDA
1⃣ -Akwai heating pad da akan bada
shawarar ayi dakuma yan magungunna na rage radadi wadanda mai shayarwa zata iya
sha.
2⃣-Hutawa asamu hutu dakuma a kiyaye
daga dukwani abu mai nauyi daya wuce nauyi babyn sannan a guji tashi daga
tsugunne kai tsaye batareda an dafa wani abu ba.
3⃣-Abu mai mahimmanci da akansamu
gaggawa ko sabani tsakanin maigida da maijego shine sex, yakamata idan akayi ma
mace C. S ayi hkr da sex harsai bayan sati shidda
4⃣Sannan a kiyaye yin driving bayan
C. S harsai mace taji lafiya lau bata bukatar shan wadannan kwayoyi na rage
radadi ciwo akalla de sati biyu kenan
5⃣Sannan mace tarika kula sosai da
wurin da akayi yankan saboda infection, musamman wadannan alamomin
6⃣Zazzabi
7⃣Wurin da aka yanka yayi kumburi,
yayi ja, ko yarika discharge
8⃣ Zubarda jini sosai
9⃣Matsanancin ciwo
1⃣0⃣Idan mace tana famada bacin rai
ko rashin annashuwa, ko rashin dandano a bakinta, ko yawan jiri ko mutuwar jiki
to taje asibiti musamman idan kwanaki basu tafi ba.
Comments
Post a Comment