*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
*FIRGITAR JARIRI*
Firgita ga jariri sabuwar haihuwa tana farawa da kara ko kuka
sai motsinda yake zuwa lokaci daya, sukanji kamar zasu fadi saisu yi respond,
wani lokacin su mikarda hannuwa ko kafafuwansu, koma duka, bayansu ya guntsura
wani lokacin yaro yayi kuka wani lokacin kuma bazaiba.
Wannan shi akecema ' *Moro
reflex* ' akwai abubuwa makamancin firgita dayawa da jarirai suke zuwa dasu,
wasu abubuwa suka tafi cikin dan karamin lokaci wani lokaci kuma suka dauki
watanni basu tafiba,.lokaci postdelivery wanda shine checkups na farko da akeyi
ma yaro likitan yara yana duba irin wannan respond din.
Firgita jarirai takasu daban daban,
akwaima wadda muke dauka ba Firgita ba amma Firgita ce, kuma da anhaifi yaro
batareda bata lokaci ba suke fara yin wadannan firgitar. Ga kashe kashenta
♦- *Rooting,* idan aka taba kumatun
jariri za aka yana bin inda aka taba din da fuska yana juya fuskar yana buda
baki yanaso yakama hannun ko nono wannan jariri yadda suke response kenan wajen
koyon ko neman nono ko abinci
♦ - *Sucking,* dazaran aka taba koda
ba hannune ba koma miye yataba saman bakinsu za a ga sunbuda bakinsu, haka ake
halitta kowa basai ankoya masa yadda zaisha nono ba daga farko saidai daga baya
ayita gyara masu
♦- *Grasping,* a lura, za'aga
jarirai suna rintse idanunsu duk lokacinda aka taba tsakiyar tafin hannunsu ko
aka basu wani abu suka rike a hannunsu zasu rufe idanunsu wannan wata hanyace
dasuke koyon rike abubuwa ko kamo abubuwa musamman idan aka taba yatsan hannu
ko babba dan yatsansu wannan shiyasa ake koya masu dabarun rike abubuwa ta
wannan hanyar
♦ *Stepping* , idan aka rike jariri
a mike kafarsu ta taba kasa za a ga suna janye ko dage daya saikuma aga itama
dayar suna kokarin dageta amma ba lokaci daya ba a lokitta daban daban, wannan
jariri na koyon yadda zaiyi tafiya ne kuma suna yine dazaran an haifesu.
Wadannan sune irin firgitar da
jarirai keyi wadda batada matsala saima fatan surika yin irinsu.
*FIRGITA DA AKAFI SANI*
Dayawa jarirai na firgita ne
wadda kowa yasani a firgita lokacinda ake kokarin kwantarda jariri ko yaro ko
daukarsa ko daga shi kokuma kwantardashi batareda wani abu dazai rika ji kusada
shiba, yana firgita ne saboda yana tunanin ko jin kamar zaifadi ne sai aga yaro
yayi firgitar koda yana bacci ne kuwa wani lokacin. ♦Idan jariri ko yaron yana
figita hadashi da jikin uwa lokacin da ake kokarin kwantardashi yazama jikinsa
dana uwarsa suna like tana zare ko janye nata a hankali kada a janye jikin duka
harsai bayanshi yataba katifar ko shinfidar, wannan zairage yawan firgita.
♦Goya yaro, dayawa wadanda basu cika
goya yaransuba suna fuskantar wannan matsalar, goya yaro yanasa yasamu bacci
sosai kuma yana rage firgitar shiyasa wasu lokacinda za a kwanto su daga baya
sai uwa ta mike hannunwa dazai sa jariri yayi nisa da jikinta kafinta maido shi
wannan yanasa firgitar, amma da wajen ciro shi daga bayan za arika juyoshi zuwa
gaba a hankali kuma ta goga jikinsa da jikin uwa za asamu saikin firgitar.
♦Amfani da blanket babba
kuma mai kauri wajen kwantarda jariri a sarari zai rageta.
Sannan wajen shinfidar a linke
karshen blanket din, sannan a hankali a juyarda fuskar sama shikuma kan yana
daidai inda aka linke din daga blanket din.Sannan sai akara linke wani bangaren
na blanket din ya gitta ta jikin yaron.
Amma wajen kafar kada asata a
cikin bargon sai a linke karshe abar tafin kafar da kafar na motsi ko lilo
Sannan sai kingin gabar ta
blanket din sai a rufa masa shi abar fuskar da wuyan kawai a bude
Wannan shine akecema
*swaddled* , kuma anayinsa ne kawai idan jariri na kwance akan bayansa ne kuma
insuna bacci kuma ana yawan dubasu saboda zafi
kokuma yarika dadewa baiyiba lokacin
yana iya motsa jikinsa dakanshi
*ABIN LURA DA DAMUWA AKAN FIRGITA*
Idan aka lura misali kamar na
farko danace yawanci bamu daukesu firgita ba, akaga wani bangare daya ne kawai
yaron ke motsawa to tana yuwuwa kafadarshi yaji ciwo a wajen, idan kuma dukane
ma jikin baya motsawa tana yuwuwa akwai matsala daga kwalwa ko lakka.
Idan akwai damuwa aje asibiti
likitan yara zaiduba yagani Idan akwai damuwa zaisa ayi examine muscles da
nerves na baby don gano matsalar. ✍ *DR SHUAIBU MB* (KIWON LAFIYA whatsapp group)
Yarona asAlin firgitarsa TafarnUway aka shafamasa abani shAwAra
ReplyDelete