*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
*GENOTYPE* Alhamdulillah yanzu ansamu cigaba sosai ta yadda ake gwajin
GENOTYPE din masoya biyu kafin suyi aure wannan ba karamin alkairi bane ga
al'ummar dazata taso nan gaba.
Babban abinda ya hada ko ya
kunshi jinin mutane shine cells watau kwayoyin halitta wadanda suka kasu kishi
kishi to wanda yafi mamayewa daga cikin wadannan cells din shine Red Blood
Cells (RBCs). Wannan cells suna dauke da wani substance mai suna Hemoglobin
wanda inbabu shi kokuma batareda shiba wadancan Red Blood Cells din basu da
amfani.
To shima Hemoglobin din yakasu kishi
biyu heme da globin koda yake basaina yi nisa ba saboda lokaci bari intafi kai
tsaye wajen dalili yin rubutun tunda wannan ba shine mafi mahimmanci ga mutane
ba susani inba dalibi ba.
Yadda kashe kashe ko rabe
raben rukunai na genotype suke, amma yanada kyau kafin rabe raben genotype
mutafi ga yadda shi wancan Hemoglobin din yakasu don sanin haka zautaimaka mamu
wajen fahimtar bayanin da nikeso inyi.
Hemoglobin yakasu kishi ukku,
A Hemoglobin, S Hemoglobin C Hemoglobin, C hemoglobin yanada karanci
dukda yanzu yazama ruwan dare saboda kowa yanada biyu watau couples a cikin
jininsa na wannan hemoglobin din da ake gado daga uwa da uba wanda sakamakon
wannan Hemoglobin dinda ake gado daga iyaye biyu watau uwa da uba sune suke
haifarda kashe kashe genotype dinda mukedasu kamar, AA, AS, AC, SC, SS ko CC
*YA AKE MUTUM KE SAMUN GENOTYPES
DINSA?*
Idan kuma Baba YADO yazama AA
maman YADO tazama SS za aga duk yaran maman da baban YADO zasu zama AS, ana
iyasamun ba AS ba amma gaskiya yanada wuyar gaske asamu wanda ba AS ba cikin
yayansu abinda yasa nace kila ma asamu wanda ba AS ba saboda poo yana faruwa
wani lokacin.
Anasamun genotypes ne daga
iyaye dasuka hadu akasamu cikin ka har aka haifeka, misali baba da mama suka
hadu akasamu ciki aka haihu akasamu yaro mai suna YADO, to YADO zai gaji
wadannnan hemoglobin din guda biyu daya daga maman YADO daya daga baban YADO
saimu dauka baban YADO nada AA itakuma mama YADO nada AS to dole YADO zai kasance
cikin daya kode YADO yazama AA ko AS. Saboda haka duk sauran cikinda za asamu
daga baban YADO da maman YADO dole yazama 50:50 watau yakasance AA ko AS
genotypes.
Daga karshe ana iya samun
kanen YADO yazama AA ko SS komade minene baza asamu wanda zai tsallake ko fita
daga tsarin wannan genotypes din na iyaye sa ba.
Misali na biyu, ace Namiji yanada AA
genotypes matarda ya aura itama AA ce yanada wuya su haifi mai genotypes daya
fara da C ko da S ba kokuma yakare da C din koda S ba watau de yayansu zasu kasance
AA ne duka haka sauran genotypes din suke
*GENOTYPES DASUKA FARA DA C KO
S KOKUMA SUKA KARE DA C KO S*
Mutanen da Allah ya jarabta
suke dauke da genotypes SS wanda suke famada ciwo da matsalaloli na lafiya da
akecema crisis da turanci sune sukafi wahala sai masu bi masu wajen shan wuya
sune SC genotypes, mutane dasukeda AC genotypes basu tareda symptoms na
matsalar saidai lokutta zuwa lokutta za agansu da jaundice.
Misali, AA sune lafiyayyi
sosai, AC, AD, AF, AG, A+Fast suma regular ne dakuma normal sai AE da AS suba
regular da normal bane amma basuda wani alamu na matsalar a bayyane wani
lokacin ana daukarsu ko suna kusada AA, genotypes dasuke fama sukeda matsala
sune SS, SC, da CC genotypes.
Misali, AA sune lafiyayyi sosai, AC,
AD, AF, AG, A+Fast suma regular ne dakuma normal sai AE da AS suba regular da
normal bane amma basuda wani alamu na matsalar a bayyane wani lokacin ana
daukarsu ko suna kusada AA, genotypes dasuke fama sukeda matsala sune SS, SC,
da CC genotypes.
*ABINDA YASHAFI AURATAYYA
TSAKANI*
Shawara shine idan anaso a
kaucema samun yara masu famada matsalar shine a kaucema dukwata hanyar da
zatakaiga samun yara tsakanin wadannan genotypes din, SS, SC, CC, abune mai
wuya wasu lokuttan a iya banbance wahalar da masu SS da CC suke sha
*ALURA*
AA genotypes normal ne.
AS genotype bawata alama ta sickler
amma carrier ne,
SS sickler ne.
AC shima carrier ne amma
bawata alama a bayyane,
CC wannan yana kusa ko kamada SS,
SC yana famada yawan matsalar
karancin jini, da matsalar kashi daya shafi bargo.
*SHAWARA*
Idan AS da AC suka auri juna sunada
chance na samun sickler cikin yaransu da kashi 25% idankuma suka auri SS ko SC
sunada chances na haihuwar masu sickler kashi 50%, idan kuma SS ko SC suka auri
junansu to zasu rika haihuwar duka yaran masu sickler saboda SS da SC duk
dayane banbancin kawai mai SS yafi mai SC shan wahala.
Duk namiji ko mace idan anaso a
kaucema haihuwar yara masu matsalar to mai AC ko AS, SS ko SC ko CC su
kauracema auren juna in anaso a kaucema samun matsalar ga yara
*TREATMENT*
Ana Born Marrow Transplant BMT
amma gaskiya ko a turai dasuke yi ba kowa ne yakeda halin yiba dukda ma yana
tattare da matsaloli musamman ga wadanda ta jima jikinsu tafi sauki ga jarirai,
kuma dik africa inaga ba inda ake sai turai da america amma alhandulillah
kwanakin baya ko kwanannan wani likita dan kano dayake Shugabantar irin wannan
cibiya a america yazo yatara likitoci da dalubai antattauna yayi alkawalin
cikin shekara biyu zuwa ukku zai samarda cibiya ta farko a jihar kano insha Allah
kuma yayi alkawalin kudin aikin zasu zo da sauki saboda kayan aikin masu sauki
kudi zaikawo.
Gameda magani akwai wani
magani ko ince suppelements ma suna CELLSGEVATY alhandulillah daga America suke
kuma angwada acan da nan Nigeria kuma alhandulillah gaskiya inde andaure akayi
amfani dashi a kaidar tun ranarda akafara shanshi za afara jin chanji.
Sai a kulada abinci wanda ake
bukata, da kaucema wanda ba a bukata da yanayin da ba a bukata dakuma daurewa
arika amfanin da magungunna da ake badawa asha. Allah yabada mafita amin
✍ *DR SHUAIBU MB*
Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail
dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blogsite dinmu
kiwonlafiya1. blogspot.com
Comments
Post a Comment