*DAGA ZAUREN KIWON LÀFIYA🚑🚑*
*HAWAN JINI*
Yawan da karfin zagayawar jini yake akan jijiyoyi na jini da tsari
wani ginshiki na alama ta hawanjini. Matsi da gewayawarda jini yake saiya rage
tafiyar jinin zuwa ga kofofi, hanyoyi da jijiyoyin jini. Hawanjini a takaice de
matsi da jijiyar jini take samu, jijiyar dake dauko jini daga zuciya
Hawan jini ba
daya ne da yanayin bugawar zuciya ba watau pulse ko yawan ko saurin bugawar
zuciya ba.
Akwai hawanjini dayake sama da
akecewa jinin mutum yahau Akwai wanda kuma akecewa yayi kasa.
Idan mutum zai auna a gida yadda zai
iya ganewa pressure ta jinin sa tayi kasa shine.
Akwai systolic dake sama sai
diastolic dake kasa.
Kamar yadda zamuga idan za a
rubuta sakamakon awon hawanjini akan rubuta number guda biyune daya sama daya
kasa to systolic number din itace sama misali *125/70*
*90/60 mm Hg* yana nuna
pressure din tana kan iyaka daya kafar a ciki daya a waje watau de abu kadan na
iyasa ace hawanjini mutum yayi kasa haka kuma kadan zaisa ace yayi daidai
*60/40* wannan yanuna hawanjini
mutum yayi kasa shine wani lokacin zaifara jin alamomin marsalar
*50/33* wannan mataki ne
dayake da hadari sosai wanda mutum yake bukatar kulawar gaggawa ta musamman
kuma.
*MINENE NORMAL*❓
*120/80* shikuma normal
hawanjini kenan.
*130/85* normal ne amma high
*110/70* shikuma normal ne
amma low.
*MINENE HAWANJINI DAYA HAU*❓
Kafin fadin numbers yakamata musani
cewa mataki mataki ne shi hawanjini din daga mataki na farko zuwa na hudu
*210/120* hawanjini na mataki
na 4.
*160/100* hawanjini mataki na
biyu.
*180/110* hawanjini mataki na
ukku.
*140/90* hawanjini mataki na
daya kenan.
*YA ZA AYI ASAN MATAKAI NA SHEKARU
YAZAI KASANCE*❓
Shekara *17-19, 90/60* yayi
kasa, normal kuma *120/80*, yahau kadan ko yadan gota amma baizama hawanjini ba
*120-129/80*
Shekara *25-29, 90/80* yayi
kasa, normal kuma *120/80*,yahau kadan ko ya dan gota amna ba hawanjini ba
*120-129/80*
Shekara *20-24, 90/80* yayi
kasa, normal kuma *120/80,* yahau kadan ko yadan gota amma baizama hawanjini ba
*120-129/80*
Hakade table din yake tafiya
har zuwa yan shekara samada *60+*
Yaro dan shekara daya zuwa ukku
namiji yana kamawa daga *80/34 - 120/75,* mace kuma yar shekara 1-3 yana kamawa
daga *83/38-117-76*
Saina yara kanana sukuma.
Yaro dan shekara 7-10 namiji
yana kamawa daga *92/53 - 130/90,* mace yarinya mai wannan shekarun yana farawa
daga *93/55 - 129/88*
Yaro dan shekara 4-6 namiji yana
kamawa daga *88/47-128/84* yarinya mace mai irin wannan shekarun itakuma yana
kamawa ne daga *88/50-122/83*
Mutane dayawa inba wadanda
suka san alamunsa ba bare suyi tunanin shi basusan sunada hawanjini ba harsai
an aunasu anfada masu wasu dama suna tsammani wasukuma suyita mamaki sabida
basusan minene yakawo masu shiba kuma kaima kila bazaka iya gane miya kawo masu
shiba amma de akwai sanadi dasuke bada gudunmuwa wajen jinin mutum ace yahau.
*MIYAKE KAWO HAWANJINI NE*❓
Shekaru
♦Nauyi ko kiba ko size
♦ Shan barasa ko cigarette
♦Maza sunfi kamuwa dashi a yarinta
amma mata sunfi kamuwa dashi a tsufa
♦ Rashin motsa jiki
♦ Cututtuka irinsu kitse, ciwon
kashi, ciwon suger, kidney disease
♦Cin gishiri dayawa da yawan amfani da
abincin gwangwani da robobi
♦ Cin abinci masu karancin sinadarin
potassium
♦ Gado amma sai ga wanda yakasa
managing stress dinsa
*ALAMOMIN HAWANJINI*
Alamominda yake nunawa
lokacinda yazama yayi sama sune ciwon kai da jiri, sai laba ta hanci da kunne.
Shi hawanjini shu'umin ciwo ne
dayawa kamar yadda nace basu jin wata alama Sai lokacinda yakai mataki dazai
zama hadari yake baiyanar alamominsa shiyasa yawan aunawa ko a gida yakeda
mahimmanci.
Yazama halitta systolic number
watau number tasama tazama atara da 100 ga maza amma cire goma ga mata, ina
nufin ga maza misali shekara 40 zaizama 140 kunga akwai + gamata sukuma yar 40
zaizama 130 kunga akwai - kenan.
Shekaru suna karuwa hawanjini
yana karuwa saboda jiki yana kara bukatar oxygen da nutrients
Daga cikin abubuwa ko cututtuka da
hawanjini ke haifarwa akwai bugawar zuciya, stroke, dqkuma cadiovasculer
disease.
*ALAMOMIN BUGUN ZUCIYA* ko
heart attack da turanci
Yawanci attack na zuciya yana
zuwa ne lokaci daya kuma nan take amma wani yana zuwa ne da wasu kananan
alamomi dasuke takura ma mutum kamar dayawa sukanzo da ciwon kirji a tsakiya
kuma aji yatafi cikin yan mintuna kuma saiya sake dawowa shine sai aji anajin
kamar ana matse kirji, ana squeeze dinsa kuma ga ciwo wani lokacin arika jin
numfashi na neman daukewa, tashin zuciya, rashin karfin jiki, gani bushi bushi
Zuciya tana bukatar jini
yakawo ko ta dogara ga jini yakawo mata oxygen da nutrients don tsokokin dake
tareda ita saboda tsukewar da jijiyoyin jini dasuke halba jini sukayi saisu
zama sunyi blocked saiya haidarda hawanjini idan wannan blockage din
yafaru ga jijiyoyin dasuke da alaqa da zuciya to duk xai shafi tsokokin dake
zagaye da ita daduk wani abu daya shafe ta saita tsaya chak ta daina aiki shine
attack na zuciya
To yau da kullum wurinda
jijiyoyin suka katse saiya fara rubewa dalili fading da wurin zairika yi saiya
haifarda stroke kokuma gudajin jini su toshe jijiyoyi shima saiya haifarda
stroke
*ALAMOMIN STROKE,* kwakwalwa
tana bukatar jini itama saboda tafiyar da ayyukanta to yawan zuwan jini dayake
faruwa saboda hawanjini sai jijiyoyi suyi rauni, to lokaci mai tsawo suna rauni
saiya kaiga sun katse sai jini yarika leaking cikin kwalwa.
Za a iya fahimtar alamominsa
ta hanyar kumburi ko weaknesses ga fuska ko ga arms ko ga kafa, musamman ga
bangare daya, sai mutum yarika confuse, matsalar magana, matsalar gani, ciwon
kai lokaci daya.
Allah yaba marassa lafiya, lafiya
wadanda keda ita Allah yakara masu mai amfani amin✍ *DR SUAIBUH M*
To taya ake samun bayanin Magungunan dakake bayanin cututtukansu
ReplyDelete