Idan inada ciki tun farko ina samu matsalar jini,kuma da ciwon kafafu,minene shawara



*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑* Idan inada ciki tun farko ina samu matsalar jini,kuma da ciwon kafafu,minene shawara❓   Matan da suke da ciki na daga cikin mutanen da suke fama da matsalar rashin jini,saboda yawan jinin da jiki take samarwq dan saboda ciyar da baby dake ciki.
 Karancin jini lokacin juna biyu abune mai saukin warkarwa idan de akan gane matsalar cikin lokaci kuma yana zama hadari idan ba ayi treatment da wuri ba ga uwar da baby
🔹-Karancin sinadarin iron a jikin mai juna biyu, kashi 15-25% na masu juna biyu na fuskantar wannan matsala lokacin da sukeda juna biyu.
Akwai samada dalillai 400 na rashin isasshen jini amma ga masu juna biyu akwai wadanda suka kebantu dasu.
 Amfani da irinsu spinach, jan nama, naman tsuntsaye, peas, wake, busasshen kayan marmari irin dabino dakuka amfani da abinci dasuke daukeda sinadarin vitamin C kamar tomato, melon peppe
 Idan wadannan basu isa ba likita zaibada shawarar amfani da supplements na iron
🔹-Karancin sinadarin vitamin B12, wasu matan suna cin abubuwa masu kara ma jikinsu wannan sinadarin matsalar kawai shine jikinsu baya process din sinadarin
🔹-yin al'ada da ake zubarda jini dayawa nasa irin wannan matsalar
 *SHAWARWARI*
 Ayi kokari chanza abinci da ake anfani dashi idan ansamu juna biyu har lokacin da za a haifi yaron.
 Za a iya gane mai juna biyu tana fuskantar barazana samun karancin jini lokacin juna biyu ta wadannan dalillai
🔸Sanyi kafa da tafin hannu
🔸 Rashin maida hankali akan abubuwa
🔸Ciwon kirji.
 🔸Yawan bugawar zuciya
🔸 Kodewar fata, lebe da farchi
🔸Jiri, gajiya, kasala *DR SHUAIBU MB*

Comments