Idan na zauna ko na kwanta kamar na 5minutes, Ina tashi zanji gaba daya tafin qafata ya riqe yana min ciwo,har said na dauki wani lokaci bai saki ba menene ya jawo hakan Dan gaba daya jijiyar qafar take riqewa.Allah ya qara basira
*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA*🚑🚑
Idan na zauna ko na kwanta kamar na 5minutes, Ina tashi zanji
gaba daya tafin qafata ya riqe yana min ciwo,har said na dauki wani lokaci bai
saki ba menene ya jawo hakan Dan gaba daya jijiyar qafar take riqewa.Allah ya
qara basira
🤔 *Plantar fasciitis*
ne yake damunki, plantar fasciitis yana daya daga cikin abinda yake kawo ciwon
diddige. Akwai wata tsoka mai kauri data tashi daga diddigen kafar mutum tahada
da tafin kafar sa zuwa babban dan yatsan kafa datake kumbura saita rika haifar
da wannan ciwon lokacinda za a fara taka kafar musamman dasafe ko bayan antashi
daga kwance ko daga zaune amma ana takawa tana sauki haka za aji tabari sannan
tana iya dawowa daga baya bayan mutum yadade tsaye ko kokuma in mutum yatashi
daga zaune.
Plantar fasciitis tafi faruwa
ga mutane dasuke gudu, masu nauyi ko kiba sosai, ko wadanda suke sanya irin
takalmannan marar support
*Alamomin plantar fasciitis*, za
aji kamar ana suka wuka ga diddige kafar mutum, kuma, za aji zafin yana yawa ne
lokacinda akafara taka kafa, kuma za a iya jinsa lokacinda mutum yadade tsaye
kokuma yatashi daga zaune kokuma bayan mutum yayi tafiya ba lokacinda yake
tafiyar ba saiya tsaya sannan yarika ji
*Akwai abubuwa dayawa dasuke kawo
plantar fasciitis*, wasu haryanzu basu zama tabbas ba wasu kuma antabbatardasu
daga cikin wadanda aka tabbatar shine yagewa da ita wannan tsokar keyi ce
wadda nace tanada tauri datake tundaga diddigi zuwa tafi ta dangana da yatsan
kafa babba saita kumbura saboda yar yagewa
Wadanda suke yawan ko iya
saurin ko hadarin samunsa sune, shekaru daga 40-60, masu gudu, rawa, tsalle
kode motsa jikin da zaishafi diddige, masu aiki dasuke yawan tsayawa akan
diddigensu, dakuma kiba
Ana duba diddigen mutum ne inda yake
ciwon inma kunburine yayi a duba, yawanci baya bukatar wani awo saidai x-rays
ko MRI, wani lokacin za aga wani dan kashi yadan kamar nuna to idan yana ciwo
akan yi surgery acire
Akwai magungunna irinna ciwo
jiki da ake amfani dasu batareda rubutun likita ba da mutum zaije chemist
yasaya yasha kamarsu, *ibuprofren ko naproxen* suna saukaka matsalar sosai
Arika mikarda diddigen da gwiwa,
sannan da daddare Arika chanxa position inza ana kwance, inzai yuwu arika
amfani da night splints zata taimaka sosai
Idan akwai kiba ayi kokarin ragewa,
arika amfani dasuka dace ba irin masu tsini dinba, ana iya jika tsumma da ruwan
sanyi a nade diddigen dashi zuwa minti 10-20 a rana sau 3-4 koda bayan anyi
wani aiki ko tafiya✍
*DR SHUAIBU MB*
Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com
ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com
Comments
Post a Comment