Ina fama da yawan saqe saqe da tunani, sai inyita saqe saqe cewa zan mutu ko kuma wani abu zai sameni. Wata rana har saqawa nike zanmutu mijina ya auri kanwata abubuwa iri iri kokuma inzanyi tafiya sai indinga jin hadari zanyi ko in wani nawa yayi tafiya. Minene ke damuna Don Allah Dr
*.✍DR SHUAIBU MB*
DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑
TAMBAYA❓❓ Inqa famada yawan saqe saqe da tunani, sai
inyita saqe saqe cewa zanmutu kokuma wani abu zai sameni. Watarana har saqawa
nike zanmutu mijina ya auri kanwata abubuwa iri iri kokuma inzanyi tafiya sai
indinga jin hadari zanyi ko in wani nawa yayi tafiya. Minene ke damuna Don
Allah Dr.
🤔✍Wannan bawani abubane *anxiety* ne watau da hausa ina iya
cewa *juyayi ko fargaba,* anxiety ba kawai tunani ko hankali mutum yake shafa
ba. Anxiety yanada irin wadannan abubuwan wanda bazama a san suna faruwa ba ko
asan shine sila. Daya daga cikin abubuwa manya da yake kawoma mutum irin
wadannan miyagun tunani da saqe saqe
Miyagun saqe saqe da tunani
suna daga cikin alamomin anxiety kuma abin takaicen irin wadannan tunani da
saqe saqe suna kara girman anxiety kuma ana bukatar taimakon wani wajen magance
matsalar anxiety
Anxiety yakasu kashi kashi
kusan kashi hudu kuma bazaka san wane irin anxiety bane sai kasa yadda kashe
kashen su yake
1⃣- *Obsessive compulsive Disorder,*
anxiety ne wanda yake zuwa ba sosai ba kuma za aga yana taba alaqar ka da
mutanen da kake kauna dakuma tunanin cewa kayi wani abu mummuna dazai iya taba
mutuncinka kuma bakayi dinba kokuma tunanin kinbar wuta kunne a kitchen amma
baki bari ba kuma kinsani amma zakita tuna haka
2⃣- *Generalized anxiety disorder* ,
shikuma irin wannan misalinsa kamar ace idan mace ce tatafi unguwa
saitaga kamar ta makara ko ta dade sosai saita ringa sauri duk hankalinta
yatashi, kokuma namiji yayita damuwa da fargabar cewa yazasu kare da maigidansa
gobe ko ya zata kare da mijinta gobe inya dawo dasauransu
3⃣ *-Panic disorder,* shikuma wannan
yashafi tunanin lafiyar mutun ne dakuma tsoron faruwar wani abu gareshi ko ga
wani nashi kamar hadari, kamuwa da ciwo dasauransu. Panic disorder zairika
sanya mutim yana tunanin zanfa iya kamuwa da ciwon zuciya misali ko zanfa iya
kamuwa da ciwon hanta dasauransu
4⃣- *Social anxiety,* shikuma wannan
anxiety ne dayake karewa ga mutane, misali mutum yayita tunanin za aci masa
mutunci, za a wulakantasa ko cin zarafinsa ko ayimasa dariya inyaje wuri kaza
ko inya shiga mutane harma yarika tunanin ko kawo yadda abin zaifaru dashi.
Muhadu a rubutu nagaba insha Allah
✍ *DR SHUAIBU MB*
*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
*TAMBAYA*❓❓ Meyake kawo wa mace Mai ciki fitar da wani Abu
zare kamar majina Kuma kusan kullum sai anganshi ❓❓ 🤔
Wannan majinar bakin mahaifa ce its normal, abune da kafin shigar ciki take
taimakawa ma sperm isa ciki fallopian tubes, sannan idan ciki yashiga nanma
tanada rawarda take takawa, saikuma wajen haihuwa nanma zaitaimaka wajen
fitowar babyn.✍
*DR SHUAIBU MB*
***DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑***
***MATSALAR FITSARIN KWANCE1⃣
Kusan akwai mutane samada
5,000, 000 dasuke famada matsalar nan kuma munan mutanenmu suna zuwa har
Rukiyya ayimasu da tunanin ko matsalar jinnu ne kuma abin yaki tafiya kuma baza
aje asibiti ba sai ayita maganin galgajiya, wannan matsala ce da akwaita a
likitanci na zamani kuma akwai har aune aune da magungunna da akeyi kuma insha
Allah a warke.
A turanci ana kiran fitsarin kwance
da BED WETTING
amma a likitance ana kiransa
da NOCTURNAL ENURESIS kuma wasu za aga tun suna yara abin yake samunsu wasukuma
za aga sai daga baya, ynz de zamu duba matsalar ne a tsakanin manya, idan yaro
yakai shekaru 13-18 yana futsari wani abune abin damuwa dayakamata iyaye suyi
wani abu to bare kuma ace mace harda yaya ko namiji shima harda yaya yana
famada fitsarin kwance.
Daga cikin abinda yake kawo ta
akwai gado, sannan koda wanda yadade da yarintarsa yanayi shima yaronsa akwai
yuwuwar zai iyayin haka da kashi 40%.
***ABUBUWANDA SUKE KAWO
FITSARIN KWANCE GA MANYA ***
1⃣Na farko de matsalar fitsari idan
akaje asibiti da ita kamar kowace matsala ce ta rashin lafiya kokuma cututtuka
akwai bukatar afara duba tarihi domin idan akasamu daya ko biyu daga magabata
suntaba ko sunada irin wannan matsalar to akwai yuwuwar mutum zai iya samunta
shima da kasu kusan 77%
2⃣Dalili na biyu, shine ADH
watau antidiuretic hormones shi wannan hormones din babban aikinsa shine yayi
ma kidney signal watau yarika ankararda kidney yarika rage yawan fitsarin
dayake fitarwa ko samarwa to kuma jiki yakan samarda wannan hormones din na ADH
saboda yarage yawan samarda fitsarin Allah cikin hikimarsa wasu mutane jikin su
baya samarda kode duka ko yawan wannan hormones din na ADH da daddare,Kokuma
wasu jikin na samarwa amma kidney baya respond na yasamarda fitsarin daidai da
Hormones din na ADH saiya samarda fitsari dayawa da daddare kuma lokacinda ake
bacci wanda ake kirada noctural polyuria.
3⃣ akwai alamu na ciwon suger amma
ba wancan mai tsananin ba watau diabetes 2 a a diabetes one wanda haryara ma
kanana suna samunshi
4⃣Akwai mutane masu karamar bladder
amma fa ba ana nufin wajen girmanta ba, ana nufin karfin aikinta kokuma tanada
rauni sosai wajen rike fitsari inyakai wani level watau inya wuce yawan da zata
iya rikewa
5⃣Sannan wani dalili kuma
dukde yanada alaqa da bladder shine akwai tsokoki dasuke tareda ita mafitsarar
wadanda ake kira detrusor muscles idan suna aikinsu dayawa watau suna wuce gona
da iri shima yana haufarda matsalar fitsarin kwance ga manya ko yaran
6⃣ Sannan akwai bladder iritants
watau abubuwa dasuke iyasa mafutsara ta gaji kokuma tasha wuya kamarsu barasa
da coffee dayawa idan ana shansu dayawa, akwai kuma wasu magungunna da idan ana
anfani dasu sukan haifarda haka kamar magunginna na minshari dana matsalar
bacci dana abinda yashafi kwalwa
7⃣Akwai matsalar maraina ga maza
wadda takan haifarda irin wannan matsalar dakuma raunin kugu ga mace watau
organ pelvic prolapse
8⃣Sannan duk wadannan abubuwa
suma suna haifarda wannan matsalae ta fitsarin kwance ga manya, infection na
hanyoyin fitsari, diabetes, stone na urinary tracts, neurological disorder
abinda yashafi jijiyoyi, cancer ta maraina data mafitsara, anatomical abnormalities,
urinary tract calculi, girma maraina.
Wadannan a likitanci na zamani
sune dalillai ko manyan dalillai dasuke kawo ma mutum har girmansa yana fitsari
kwance.
Zamu dakata anan sai rubutu nagabq
insha Allah
Comments
Post a Comment