*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
*(FANNIN CUTUTTUKA)*1⃣1⃣0⃣ *INFECTION NA
KIRJI*, Saudayawa idan akace infection anfi tunanin irinna vagina ake nufi,
Amma infection na iyasamun mutum ko ina
Infection na KIRJI yana shafar
hanyoyin iska ne KO hunhu kuma tana zuwa dasauki zuwa yazama Mai tsanani.
Infection na kirji yakasu kishi kishi amma de wadanda sukafi fice guda biyu ne
*pneumonia da bronchitis*
*Alamomin infection na kirji*
🔹Tari Wanda Zaarika Jin
kamar kirji zaifashe
🔹 Tari da yake zuwa da
majina green KO yellow
🔹Zazzabi
🔹Ciwon kirji
🔹 Numfashi yarika yin kamar
zaidauke
🔹Ciwon kai
🔹 Ciwon jiki
🔹Kasala kowane lokaci
🔹 Idan aka kanga kunne a
kirjin mutum aji Sumarniyar iska
*Chest infection na zuwa dalilin
abubuwa biyu* watau Kwayoyin cuta na bacteria dana viral ya danganta da wane
irine misali bronchitis yana zuwa dalilin virus shikuma pneumonia yana zuwa
dalilin bacteria dayawa
Za a iya daukar infection na kirji
idan maishi yayi atishawa ko tari kana kusada shi koya tofarda majina bai
rufeba, KO idan yataba majinar da hannunsa yataba wani abu wani yataba yashafi
hancinsa
*Wadannan Rukunan mutanen sunfi
hadarin kamuwa dashi* dukda kowama zai iya kamuwa dashi
◼Tsofaffi
◼Jarirai da yara kanana
◼Mata masu juna biyu
◼Masu shan cugare
◼ Masu cututtuka irinsu asthma,
ciwon suger, COPD dasauransu
◼ Wadanda sukeda raunin garkuwar
jiki
Idan mutum yayi mura data dade KO
mai wuya
Idan mutum yanada infection na
kirji kuma yana cikin wadannan Rukunan saiya hanzarta zuwa asibiti
Yawuce shekaru 65
Yanada yaro Dan kasada shekara
biyar
Mace Mai juna biyu
Wanda yakeda wata rashin
lafiyar
Majina da jini
Tarin jini KO tari da majina jini
Tarin yawuce sati ukku
Masassara da ciwon Kai
Numfashi dasauri KO yana Yi
kamar zaidauke, da ciwon kirji
Jiri, confused dasauransu to aga
likita dasauri
Anayi x-rays na kirjin, KO awon
majina KO awon jini Don tabbatardashi KO agano inda yake
Treatment
Kuskure dayawa da ake a
asibitoci shine yawanci ana bada antibiotics ne KO maganin tari batareda ansan
KO an banbance virus KO bacteria bane
Maimakon haka mutum zaiji
sauki ne nawani dan lokaci kuma Tarin yadawo
Idan virus ne antibiotics
bazasuyi maganin ba
Idan kuma bacteria dince Amma
infection din yayi tsanani dole sai ansa ruwa na IV antibiotics a asibiti
Idan bacteria ne shine za ayi
treatment din mutum da antibiotics din
Ana anfani da magungunna rage radadi
don zazzabi dakuma ciwon jikin
Idankuma virus CE akaba mutum
cough syrup nanma bazai yi maganin matsalar ba KO ta tafi dawowa zatayi
Asamu hutu sosai
Sai decongestant KO expectorant
syrup Don majina tarika fita
Arika shan ruwa sosai
Arika kwanciya kai yayi sama
Ana streaming da vapor KO
amfani da Humidifier
Idan Ana Shan cigarette abari KO
zama kusada maisha KO aguji kura KO hayaki
Idan makoshi yana zafi KO kaikayi
saboda tari ana hada Zuma da ruwa lemon fata a dumduma arika sha
Arika zama cikin iska
Dukwani magungunna tari a
kaurace masu
Yawanci yana tafiya dakansa
cikin sati ukku Amma yana iya kaiwa har watanni
*Kariya*
♦ Vaccination
♦ Arika yawaita wanke hannuwa kafin
aci KO asha KO ataba fuska, hanci KO baki
♦ Arika chin lafiyayye abinci Don
inganta garkuwar jiki
♦Karya maida majinar intariga ta
taho
♦Idan mutum yariga yakamu yarika
yawaita wanke hannunsa, inzai tari yarika rufe bakinsa daw hannunsa KO
Handkcif, yarika rufe majinar inya zubar
Allah yakara mamu lfy
✍
*DR SHUAIBU MB*
Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com
ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com
Masha allah gsky malam allah yaqara basira dayawa daga cikin abunda ka lissafo mahaifina nafama dshi kuma nadauki darasi sosai allah yaqara ilimi mai anfani ngd sosai
ReplyDeleteI feel all this symptoms even though I still feeling it don't know how many types of medicine I take,I started with little cough last month ago but things parsist turn into serious cough with blood they hospitalized me almost a week the have tried their best bc cough with blood stopped all their evaluation shown that I have chest infection no pneumoniae neither tb but I'm serious concerns with my chest congestion and cough I also meet another doctor he put me on cifrocoxine and emzolin cough syrup all this type s medication didn't work, impact I'm diabetic so now I need your help advice these are the list medicine I use before across your advice
ReplyDelete1 azithromycin
2 ethromycin
3 clairthromycin
4 cciflocoxine
Cofmix syrup
Emzolin syrup
Cofmix syrup
Menthodex cough syrup ttank your till heir Your respond
Dr Allah saka da alheri shin zan iya kunna fanka a lokacin zafi? Saboda yarona da yake fama da pneumonia watanshi 4 sau 2 muna kwanciya asibiti saboda pneumonia na gode
ReplyDeleteYana tari cikinshi na kumburi in rashin lafiyarshi ya tashi yana numfashi dai daya da kuma zazzabi mai zafi a halin yanzu dai yaji sauki amma inaso in kiyaye saboda gudun tashin rashin lafiyarshi
ReplyDelete