*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
*KACIYAR
YARA MATA*
Kachiyar mata de al'ada ce da
kasashen afrika kusan 17 akeyi a ciki abaya Nigeria itace kasada tafi kowace
kasa yin wannan dabi'ar amma yanzu kasar Niger ce gaba gaba dukda suma suna
kokarin yaki da dabi'ar sosai.
Itade kachiyar mata ana yanke lebia
ne duka, kokuma ayima wurin rauni da gangan kokuma achanza ma wurin fasali.
Kachiyar mata da mai tambaya
tayi tambaya tace ta jarirai da ta manya to inde Kachiyar matan ce da kowa
yasani to dukde itace abinda yake faruwa shine lokacinda yarinya karama keda
shekaru biyu zuwa hudu ko lokacinda aka haifi yarinya sai ayi, sukuma wadanda
suka girma sukayi aure akwai wannan matsalar ta rashin shigar azzakari kokuma
koda dan yatsane karami a gaban mace baya shigar ta idan aka duba cikin
tambayoyi dana amsa kwana biyu harda tambaya akan wannan harna bada wasu tips
da za a iya don magance matsalar.
Amma kuma akwai wata sabuwa
mai kama da kachiyar mata Amma ita ba kachiyar bace anace mata lebiaplastic
watau itakuma yanmata kanana ne daga shekaru 11-16 har 18 ma akemawa sukuma
suke zuwa asibiti dakansu akemasu saboda a shekaru su sunaga gabansu ba iri
daya bane da sauran manyan mata ba to saisu je ayimasu wannan tiyatar inda ake
rede wadannan lebban na vagina.
Waisu a tunanin su wurin yafi kyau
gani basusan insuka shiga matakin balaga wurin dakanshi yake chanzawa zuwa
irinna manya.
Ba a turaiba ko nan Nigeria yanzu
dayawa mata masu wannan shekarun suna zuwa dakansu suce ayimasu, wasu likitocin
sunayi kawai Ba don anaso wasukuma anasasu suyi saboda yaran suna zo masu da
karyayyaki na wanda za a iya dogara dasu ayi ma mace irin wannan gyaran kinda
dama anayima masu tawaya ne a gabansu irinta.
Mu koma ga tambayar nayi
wannan bayanin ne na biyu sabida mai tambayar tace da na lokacin haihuwa da
lokacin da mutum ya girma shiyasa don a banbance ko nangaba akaji wannan salon
to asanshi kuma fa anayinsa har a garuruwanmu ynz sosai.
Maganar illoli bama sai mutum
ya fada ba ai, illoli masu yawa ma sosai, anrabasu kamar rukuni rukuni ne dukda
suma masuyin sunada nasu dalilin dayasa sukeyi.
Bayan cututtuka irinna infection
daka iya jawo matsalar haihuwa ga matsaloli irinna kamuwa da cututtuka,
matsalar fitowar jinin al'ada, matsalar fitsari, kari a gaba, zafi wajen
jima'i.
Akwai matsaloli wajen haihuwa ga
wadanda akayima kachiyar irinsu matsalar nakuda, yagewar tsakanin vagina da
takashi, zubarda jini dayawa lokacin haihuwa, vaginal fistula watau fitsari
yarika fitowa ta vagina maimakon ta mafitsara, recto vaginal fistula aga bayan
gida na fitowa ta vagina maimakon ta dubura, yima mace CS dasauransu.
Psychologically ma yanada
nashi illar misali, fargaba, damuwa, matsalar jima'i dasauransu
Inafata mai tambayar ta gamsu
da takaitaccen bayani.
Amma akwai kwararrun likitocin
fida da suke gyara mata da akayima kachiyar abaya dukda de tiyatar tana ba
likitocin wahala dukda kwarewarsu akai , idan akwai wata matsala data shafi
wannan ko karin neman bayani aje asibiti aga likitan komi da ruwanka watau
physician sai a tattauna dasu.✍
*DR SHUAIBU MB*
Comments
Post a Comment