Mace ce tafara ciwon wuya sai yazamana har zazzabi da ciwon kai yasakar mata ga atshawa

*DAGA  ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*  Mace ce tafara ciwon wuya sai yazamana har zazzabi da ciwon kai yasakar mata ga atshawa

Tasha pectol da pracetamol da v-c da really extra tanajin sauki sai abun yadawo

Tau yanxu kasan kirjinta na hannun hagu yake ciwo kaman ana hura mata wuta dataci abinci sai yalafa Amman datasha tea sai cikin ya kumbura

Sannan idan taje wajen fitsari tanaganin wani white discharge mai yauki kuma sai take gudawa mai kumfa bayan cikin ya kumbura, mene ne  shawara❓
🤔 *Cervicogenic headache* ne daga abinda na fahimta, wani ciwon kai ne dayake farawa daga bakin kashin  baya wajen wuya wani lokaci yana kamada migraine headache watau ciwon kai na gefe kuma yana zuwa intermittently watau yanyanke saiya bazu zuwa wani barin kai kuma saiya zama ya cigaba kuma saiya shafi yadda wuya zairika motsawa kokuma wani bangare na wuya.
 Cervicogenic headache yanada alaqa da yawan stress da wuya yake samu wanda yake shafar wani faifai na bakin kashin baya ta inda wuya ke juyawa sannan bony structures watau kasusuwa dasuke da kamannu iri daya ko tsari iri daya a wuya misali kamar facet join dakuma tsokoki masu laushi na wuya nakara girman irin wannan ciwon kan.
 Abinda yasa akejin har ciwon kirjin da hannunta suke ciwon, jijiyoyin dasuke tareda lakka suna shiga ciki suma ta hanyar sune masu isarda sako ko masu shiga tsakani na bayanai tsakanin kwalwa da jiki ta hanyar spinal cord. Kuma kowane level na bakin kashin baya yana shirye ne akan jijiyoyin lakka ne daya bangaren hagu daya bangaren dama.
 C1,C2,ko C3 suna iya shiga ciki dalilin cervicogenic headache din, wadannan wasu jijiyoyi ne dasuke bada damar motsawa dakuma sensation na wuya dakai to compression na wadannan jijiyoyin saisu haifarda kumburi da ciwo
 *ALAMOMIN CERVICOGENIC HEADACHE*
Shi cervicogenic headache za arika jin ciwon daga baya kuma yakare akan skull, wani lokaci yasafko zuwa wuya harzuwa tsakanin kafadu, wani lokacin yatabo saman girar ido zuwa goshi.
 Dayawa ciwon kan yana farawa da zaran anmotsa wuya koda anyi atishawa.
 Sauran alamomin da akan iya jinsu kokuma mai irin ciwon kan ke barazanar jinsu sunhada, kasala, rashin bacci, rasa iya juya wuya, dasauransu.
 Sauran alamominsa sunhada kagewar wuya, yawan tashin zuciya da amai, jiri, gani bushi bushi, mutum yaji bayason haske ko kara k hayaniya, ciwon kafada ko duka kafadun, kasa zurga zurga
 Akwai treatment dinsa da dama amma ba wanda za ayi bayani anan bane ko asibiti akwai bukatar yin wasu gwaje gwaje kafin asan miyakamata ayi irinsu, MRI, CT scan, X-rays, Nerve blocks inj. Dasauransu
 ✍ *DR SHUAIBU MB*                     Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com

Comments

  1. Ni kai nane yake ciwo sai naji da wuya na amma ta bayan wuyan kaman yana hawa a kai, sai kuma ina saurata awanna lokaci ni na aza ko zai bari yanzu nayi kusan wata hudu dashi. Don Allah menene maganin kuma menene yake damuna?

    ReplyDelete

Post a Comment