*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
Mace ce tafara ciwon wuya sai yazamana har zazzabi da ciwon kai yasakar
mata ga atshawa
Tasha pectol da pracetamol da v-c da
really extra tanajin sauki sai abun yadawo
Tau yanxu kasan kirjinta na hannun
hagu yake ciwo kaman ana hura mata wuta dataci abinci sai yalafa Amman datasha
tea sai cikin ya kumbura
Sannan idan taje wajen fitsari
tanaganin wani white discharge mai yauki kuma sai take gudawa mai kumfa bayan
cikin ya kumbura, mene ne shawara❓
🤔 *Cervicogenic headache* ne
daga abinda na fahimta, wani ciwon kai ne dayake farawa daga bakin kashin
baya wajen wuya wani lokaci yana kamada migraine headache watau ciwon kai
na gefe kuma yana zuwa intermittently watau yanyanke saiya bazu zuwa wani barin
kai kuma saiya zama ya cigaba kuma saiya shafi yadda wuya zairika motsawa
kokuma wani bangare na wuya.
Cervicogenic headache yanada
alaqa da yawan stress da wuya yake samu wanda yake shafar wani faifai na bakin
kashin baya ta inda wuya ke juyawa sannan bony structures watau kasusuwa dasuke
da kamannu iri daya ko tsari iri daya a wuya misali kamar facet join dakuma
tsokoki masu laushi na wuya nakara girman irin wannan ciwon kan.
Abinda yasa akejin har ciwon
kirjin da hannunta suke ciwon, jijiyoyin dasuke tareda lakka suna shiga ciki
suma ta hanyar sune masu isarda sako ko masu shiga tsakani na bayanai tsakanin
kwalwa da jiki ta hanyar spinal cord. Kuma kowane level na bakin kashin baya
yana shirye ne akan jijiyoyin lakka ne daya bangaren hagu daya bangaren dama.
C1,C2,ko C3 suna iya shiga
ciki dalilin cervicogenic headache din, wadannan wasu jijiyoyi ne dasuke bada
damar motsawa dakuma sensation na wuya dakai to compression na wadannan
jijiyoyin saisu haifarda kumburi da ciwo
*ALAMOMIN CERVICOGENIC
HEADACHE*
Shi cervicogenic headache za arika
jin ciwon daga baya kuma yakare akan skull, wani lokaci yasafko zuwa wuya
harzuwa tsakanin kafadu, wani lokacin yatabo saman girar ido zuwa goshi.
Dayawa ciwon kan yana farawa
da zaran anmotsa wuya koda anyi atishawa.
Sauran alamomin da akan iya
jinsu kokuma mai irin ciwon kan ke barazanar jinsu sunhada, kasala, rashin
bacci, rasa iya juya wuya, dasauransu.
Sauran alamominsa sunhada
kagewar wuya, yawan tashin zuciya da amai, jiri, gani bushi bushi, mutum yaji
bayason haske ko kara k hayaniya, ciwon kafada ko duka kafadun, kasa zurga
zurga
Akwai treatment dinsa da dama
amma ba wanda za ayi bayani anan bane ko asibiti akwai bukatar yin wasu gwaje
gwaje kafin asan miyakamata ayi irinsu, MRI, CT scan, X-rays, Nerve blocks inj.
Dasauransu
✍ *DR SHUAIBU MB*
Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail
dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blog site dinmu
kiwonlafiya1.blogspot.com
Comments
Post a Comment