*DAGA ZAUREN KIWON LÀFIYA🚑🚑*
*MALARIA* : Wannan wani rashin lafiya ne da ake samunsa sanadiyyar cizon macen
sauro, wadda take sakawa mutum kwayoyin cuta a cikin jini.
*GA WASSU DAGA CIKIN ALAMUN MALARIA*
:
1⃣- Zazzabi
2⃣- Ciwon kai
3⃣- Tashin Zuciya
4⃣- Amai
5⃣- Gudawa
6⃣- Ciwon jiki
7⃣- Atini
8⃣- Dachin Baki
9⃣- Rashin Cin Abinci
1⃣0⃣- Rashin Karfin jiki.
1⃣1⃣- Kasala
1⃣2⃣- mutun yaji ya rasa abinda yake
masa dadi.
*KWAYOYIN CUTAR DA SUKE KAWO
MALARIA* :
1⃣- P falciparum
2⃣- P Vivax
3⃣- P ovalae
4⃣- P malarias
5⃣- P knowlesi
Amma amfi samun p falciparum a
Nigeria shi yasa mafi yawan magani da ake amfanida shi na malaria a Nigeria ACT
ne .
* GA WASSU DAGA CIKIN MUTANE IDAN MALARIA
TAKAMASU RAYUWARSU TANA CIKIN HATSARI* :
1⃣- Mace Mai Ciki
2⃣- Yara Kanana
3⃣- Masu cutan Sickler
*Malaria A Mace mai ciki Yakan kawo
mata* :
A- Haifan Macaccen jariri
B- Yakan Zubar mata da ciki.
C- Yakan Kawo Haihuwan Bakwaini .
D- Yakan Kashe Uwar Da Yaron Gabaki
Daya.
*YA AKE GANE MUTUM YANA DAUKE DA
KWAYAR CUTAR MALARIA* ❓
Ana gane malaria ne ta hanyoyi guda
biyu wanda dukkansu jini ake gwadawa, sune :
1⃣- RDTs Malaria test
2⃣- Microcopy Malaria test
*MATSALOLIN DA MALARIA YAKE
KAWOWA ( COMPLICATION OF MALARIA )*
1⃣- Rashin jini a jiki
2⃣- Matsalar kwakwalwa
3⃣- matsalar Ciwon zuciya
4⃣- Matsalar huhu da oda
5⃣- Kumburi ko fashewar spleen .
6⃣- Yana saukan da suga (
Hypoglycemia).
,Malaria an rabashi kashi biyu sune
:
⚫- Uncomplicated malaria
⚫- Completed malaria (savere malaria
)
*Ya Ake Magance Uncomplicated
Malaria*❓
*Ya ake magance Severe malaria* ❓
🇳🇬 Dukkanin
treatment na malaria a najeriya ana amfanida ACT neh.
🌎Acikin ACTn wanda hukumar
lafiya ta duniya ta zaba as first line treatment shine Arthemeter Lumefantrine.
Wanda akafi sani da Coatem.
To hukumar lafiya ta duniya
bata yarda abada wannan Coatem ga maccen da cikin ta baikai watanni uku ba.
Ko yaron da Nauyinsa baikai 5kg ba.
Coatem yana zuwa :
➡ACT
- 1
➡ACT
- 2
➡ACT
- 3
➡ACT
- 4
Ga Yadda yanayin dossage din
yake :
🔸Nauyi 5 - 15 kg ACT 1
15 - 25 kg ACT 2
25 - 35 kg ACT 3
35+ ACT 4
Shin Ya Ake Shan shi :
🕐Mutum idan yasha shan
Farko, zai maimaita bayan awanni takwas (8)
🕐Sai kuma safe da yamma har
zuwa lokocin da zai kare.
👭Misali ga Yara kasada 15kg
(6tablets )
Sai kuma ga complicated malaria :
Amma da Farko Menene complicated
malaria❓❓
Complicated malaria ko severe
malaria shine malaria wanda yakai ga wadannan alamomin :
♦- matsalar numfashi
👀- canxa launin ido da jiki
♦- hypoglycemia
♦- jijjiga
♦- matsalar kwakwalwa
♦- pulmonary edema
Da sauransu.
Shikuma severe malaria first
line treatment wanda hukumar lafiya tayarda shine *Artesunate* 💉
artesunate injection ana badashi
2.4mg/kg amma Shima hukumar lafiya bata yarda abawa mace mai juna biyu wanda
junan batakai wata 3 ba.
Hukumar lafiya ta zabi abawa mata
wanda junansu batakai wata uku ba *Quinine* for both uncomplicated and
complicated wanda shi ana badawa 20mg/kg.
*Artesunate injection* yana
zuwa kwalabe uku aciki akoi
🔹- Artesunate power
🔹- Sodium bicarbonate
🔹- Saline water
❎ *Kuma Bayan Andama Artesunate da
awa daya baza ai amfani da shi ba* .
Ga yadda ake damashi, idan za'a
abada IV
Za a dauki sodium bicarbonate 1mls ,
saline water 2mls adamasu Yakama 6mls kenan. Ko wanne ml yana dauke da 10mg .
Idan kuma IM ne ana amfani sodium
bicarbonate 1mls + saline water 2mls ya kama 3mls ko wanne ml yana dauke
da 20mg.
Kuma idan yaro baikai 6kg > ba
hukumar lafiya bata yarda abata wannan allaurar ba.
✍
*DR SHUAIBU MB*
Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com
ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com
Comments
Post a Comment