MATSALAR ÇIWON KAI



 *DR SHUAIBU MB KIWON LAFIYA*
**DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑**   **MATSALAR ÇIWON KAI🤦‍♀🤦‍♂**  Ciwon kai abune dayake faruwa saboda dalillai dayawa ko masu hadari ko marassa hadari ko manya   dalillai ko kananan dalillai, akwai rabe rabe ciwon kai dayawa. Ciwon kai yana faruwa ta dalilin rashin isasshen ruwan jiki, yawan gajiya, rashin samun bacci sosai, stress, yin treatment nawani ciwo, side effects na wasu kwayoyi, viral infection, qara ko noise, mura, raunin kai, ciwon hakori, matsalar data shafi hanci, chin ko shan abubuwa masu sanyi,dadai sauransu.
 Anraba nau'ikan ciwon kai gida biyu primary da secondary headeache.    *Primary headeache* shine wanda ke zuwa kadan, yawan zuwa kuma yatafi, kuma yawanci bawani ciwo bane babba yake kawo shiba misali kamar ciwon kan gefen kai yawanci dasuke faruwa dalili hidindimun mutum kuma basu cika zama hadari ba
 Akwai samada yanayin ciwon kai samada 200 iri iri wanda mutane ke famada su, amma anfi famada tension ko stress headeache wasu masu sauki, wasu masu tsanani, wasu kuma wadanda zasu iya kaiwa ga rasa rai, wasuma sai anyi neurological examination kafin agano su kilama harda sauran gwaje gwaje kafin agano su.
 Shikuma *secondary headeache,* yana zuwa ne ta dalili wasu cututtuka kamar raunin kai, matsalar jijiyoyin kai, infection, bleeding kwalwa, kuma sunada hadari sosai hatta alamomin sunada hadari daban tsoro sosai.
 *PRIMARY HEADEACHE* , kusan kishi 90% na ciwon kai primary headeache ne kuma suna damun matasa ne daga shekaru 20-40 na rayuwarsu, cikin wadanda sukafi kama matasan ko wadannan rukunan mutanen sune tension ko stress dakuma *migraine* watau na gefe wanda kamannunsu na zuwa da tashin zuciya, ciwon kai, gani bushi bushi, jiri, dakuma rashin son kara ko hayaniya, shikuma tension headeache yana zuwa ne batareda wadancan abubuwan ba saidai kawai mutum yarasa abinda ke masa dadi gaba daya kan yadauki pressure gaba daya
 Sauran rukunan ciwon kai dasuke cikin nau'in primary headeache sunhada :-
 *♦-clusters headeache* , ciwon kaine dayake faruwa cikin mintuna daga 15-180 tsananinsa yatafi kuma yawanci yana zuwa wajen gefen ido dayane wani lokacin hade da hawaye, idanu suyi ja, hanci yatoshe, wanda yake faruwa lokaci daya kowace rana
 ♦ *trigeminal neuralgia /occipital neuralgia,* shikuma yanasa arika jin kamar ana shooting din fuska saboda zafi ko ciwo.
♦- *stabbing headeache* , shikuma yana zuwa ne kamar guntu guntu, kuma yana zuwa cikin second zuwa yan mintuna yatafi kuma shima yana zuwa da hawaye, cunkushewar hanci, idanu suyi ja.
 ♦- *sex headeache* , anajin shine lokacin da akafara saduwa kuma yana tsanani ne lokacin da akazo realising wanda rashin ko karancin pressure ga kai lokacin saduwa yake haddasa shi, saboda idan yana faruwa lokacin da za ayi realising ne yanada kyau agano dalili don sauda yawa subarachnoid hemorrhage, wani lokacin akan hana mutum yin saduwa idan inyazo realising yana irin wannan ciwon kan harsai angano dalili.
♦- *hypnic headeache* , wannan ciwon kai yana faruwa ne a hankali zuwa tsanani yan awoyi da fara bacci kuma yana daukar mintuna daga 15-30 kuma yana iya kara faruwa daga baya duk a cikin dare daya
 Yawanci mata tsofaffi sunfi yinsa.
  *Secondary headeache* , yana faruwa ne shikuma dalili wani abu daya faru a cikin kai ko a cikin wuya yawancinsu ba masu cutarwa bane sosai misali kamar ciwon kai da zaifara daga jijiyar wuya zuwa kai, wani kuma yana faruwa ne saboda yawan amfani da pain killers watau magungungunnan rage radadi ciwo, sauran irin nau'ikan ciwon kan na cikin rukunin secondary sune :
 ♦ *meningitis* , kumburin wasu membranes guda ukku dasuke wajen kwalwa da lakka yakanzo tareda zazzabi, ko kumburin wuya
 ♦-Akwai bleeding wani lokacin dayake faruwa a cikin kwalwa, shima yana haifarda ciwon kai
♦- *suberachnoid hemorrhage* shima yana zuwa da tsanani da kumburi ko rike wuya
♦ *reptured aneurysm,* shi ciwon kaine kawai dayake addabar mutum batareda wani alama ba ko zuwa dawani abu ba
♦ *-temporal arteritis* , ciwon kai dayake faruwa saboda kumburin jijiyoyi kuma yakanzo ma tsofaffi ne dasuka kai shekaru 65-70 kuma yana zuwa da rama, zazzabi, kumburin jijiyoyi dasauransi
♦ *acute close angle glaucoma* , ciwon kai ne dayake farawa daga ciwon ido tareda gani bishi bishi, tashin zuciya, amai, jan idanu, kaskancewar idanu
 Sauran irin nau'ikan ciwon kai da abubuwanda suke kawo su akwai wanda matsalar hanji takan kawoshi za aji harda ciwon ciki, duk kusan matsalar data shafi hanji wadanda sunada yawa dukkansu na kawo ciwon kai sosai
♦ *-post-ictal headeache* , ciwon kaine dayake zuwa bayan suma ko jijjiga da mutum yasamu kansa
 *PATHOPHYSIOLOGY* , kwakwalwa dakanta bata jin zafin ciwon saboda tanada karancin receptor watau tsoka mai amsa signal sannan wurare dayawa a wurin kai da wuya sunada receptors shiyasa suke jin wannan zafi, ko ciwo ko radadi wanda yahada dawasu jijiyoyi da bansan yadda zankirasu da hausa ba amma kamarsu, extracranial arteries, middle meningeal arteries, large veins, venous sinuses, lakka, tsokokin wuya dana kai, wani bangare na kwalwa, idanu, kunne, hakora, wani bangare daga baki suke kara haifarda zafin ko ciwon
Wani lokacin kuma ciwon kai na faruwa ne saboda gogayya ko cudanya tsakanin meningitis da jijiyoyin jini a cikin kwalwa, wani lokacin kuma tsokoki da basu signal wanda kwalwa tarasa sune suke jin rauni ko ciwo saisu haifarda ciwon kai, wani lokacin kuma cudayya ko ince cakudar jijiyoyin jini cikin kai, kokuma kumburin tsokar dake bada signal ko infection yasameta sai ciwon kai, saikuma tsokar dake aika signal zuwa kwalwa tatura ma kwalwa cewa wani wuri na ciwo
 Rukunan ciwon kai na primary headeache sunfi wuyar fahimta akan secondary headeache saboda tushen sinadaran dasuke haifarda ciwon kai na gefe watau migraine, tension da cluster headeache ba asansu ba dayawa wanda nayi bayanin wadannan ciwukan kan asama.
 *** Lalle bayanin banan yatsaya ba insha Allah zanyi bayanin dukwani abu daya shafi ciwon kai da yadda za a fahimce su daban daban dakuma kokarin amsa tambayoyin mutane dasuke a cikin zukatansu gameda ciwon kai saidai saboda arika fahimta nake kawo su kishi kishi. Muhadu a rubutu nagaba insha Allah.

Comments