***DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑***
***MATSALAR FITSARIN KWANCE1⃣
Kusan akwai mutane samada
5,000, 000 dasuke famada matsalar nan kuma munan mutanenmu suna zuwa har
Rukiyya ayimasu da tunanin ko matsalar jinnu ne kuma abin yaki tafiya kuma baza
aje asibiti ba sai ayita maganin galgajiya, wannan matsala ce da akwaita a
likitanci na zamani kuma akwai har aune aune da magungunna da akeyi kuma insha
Allah a warke.
A turanci ana kiran fitsarin kwance
da BED WETTING
amma a likitance ana kiransa
da NOCTURNAL ENURESIS kuma wasu za aga tun suna yara abin yake samunsu wasukuma
za aga sai daga baya, ynz de zamu duba matsalar ne a tsakanin manya, idan yaro
yakai shekaru 13-18 yana futsari wani abune abin damuwa dayakamata iyaye suyi
wani abu to bare kuma ace mace harda yaya ko namiji shima harda yaya yana
famada fitsarin kwance.
Daga cikin abinda yake kawo ta
akwai gado, sannan koda wanda yadade da yarintarsa yanayi shima yaronsa akwai
yuwuwar zai iyayin haka da kashi 40%.
***ABUBUWANDA SUKE KAWO
FITSARIN KWANCE GA MANYA ***
1⃣Na farko de matsalar fitsari idan
akaje asibiti da ita kamar kowace matsala ce ta rashin lafiya kokuma cututtuka
akwai bukatar afara duba tarihi domin idan akasamu daya ko biyu daga magabata
suntaba ko sunada irin wannan matsalar to akwai yuwuwar mutum zai iya samunta
shima da kasu kusan 77%
2⃣Dalili na biyu, shine ADH
watau antidiuretic hormones shi wannan hormones din babban aikinsa shine yayi
ma kidney signal watau yarika ankararda kidney yarika rage yawan fitsarin
dayake fitarwa ko samarwa to kuma jiki yakan samarda wannan hormones din na ADH
saboda yarage yawan samarda fitsarin Allah cikin hikimarsa wasu mutane jikin su
baya samarda kode duka ko yawan wannan hormones din na ADH da daddare,Kokuma
wasu jikin na samarwa amma kidney baya respond na yasamarda fitsarin daidai da
Hormones din na ADH saiya samarda fitsari dayawa da daddare kuma lokacinda ake
bacci wanda ake kirada noctural polyuria.
3⃣ akwai alamu na ciwon suger amma
ba wancan mai tsananin ba watau diabetes 2 a a diabetes one wanda haryara ma
kanana suna samunshi
4⃣Akwai mutane masu karamar bladder
amma fa ba ana nufin wajen girmanta ba, ana nufin karfin aikinta kokuma tanada
rauni sosai wajen rike fitsari inyakai wani level watau inya wuce yawan da zata
iya rikewa
5⃣Sannan wani dalili kuma
dukde yanada alaqa da bladder shine akwai tsokoki dasuke tareda ita mafitsarar
wadanda ake kira detrusor muscles idan suna aikinsu dayawa watau suna wuce gona
da iri shima yana haufarda matsalar fitsarin kwance ga manya ko yaran
6⃣ Sannan akwai bladder iritants
watau abubuwa dasuke iyasa mafutsara ta gaji kokuma tasha wuya kamarsu barasa
da coffee dayawa idan ana shansu dayawa, akwai kuma wasu magungunna da idan ana
anfani dasu sukan haifarda haka kamar magunginna na minshari dana matsalar
bacci dana abinda yashafi kwalwa
7⃣Akwai matsalar maraina ga maza
wadda takan haifarda irin wannan matsalar dakuma raunin kugu ga mace watau
organ pelvic prolapse
8⃣Sannan duk wadannan abubuwa
suma suna haifarda wannan matsalae ta fitsarin kwance ga manya, infection na
hanyoyin fitsari, diabetes, stone na urinary tracts, neurological disorder
abinda yashafi jijiyoyi, cancer ta maraina data mafitsara, anatomical
abnormalities, urinary tract calculi, girma maraina.
Wadannan a likitanci na zamani
sune dalillai ko manyan dalillai dasuke kawo ma mutum har girmansa yana fitsari
kwance.
Zamu dakata anan sai rubutu nagabq
insha Allah
✍DR
SHUAIBU MB(KIWON LAFIYA)
Salam alaikum warhmatullah Inafatan kana lapiya. Dr Dan Allah maganin fitsarin kwance na manya mata zaka rubutamin nasaya sabida inada Mai lalurar Dan Allah a taimaka Dr
ReplyDeleteassalamu aleikum dan allah Dr ataimaka mana da maganin na manya da na yara dan allah
ReplyDeleteina maka fatan alkhairi dan allah maganin fitsarin kwance na manya kamar dan shekara 35 yrs fan allah muna neman taimako
ReplyDeleteAssalamu Alaikum, Dan Allah wane maganin fitsarin kwance ga manya
ReplyDelete