***DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑***
***MATSALAR FITSARIN KWANCE2⃣
Akwai abubuwan dayakamata alura dasu
ga me fitsarin kwance.Wane lokaci ne mutum ke samun kanshi ciki irin wannan,
shin da rana ne ko da daddare?
A likita ce na zamani idan anaso a
fahimci minene yakamata ko wane mataki za afara dashi na fahimtar ciki wadancan
dalillai wanene yakawo ma mutum irin wannan laluri kuma a saukaka ma likita
dakuma shi kansa mai lalurin to sai ansamu wadannan tambayoyin dakuma amsar su.
1⃣Yanayin shaye shayen ruwa da
sauran kayayyakin ruwa irinsu juices, lemun kwalba kona roba, sannan wane
lokaci akafi shansu?
2⃣Yanayin fitsari da mutum keyi shin
anayinsa lokaci daya dayawa ne koko ana yinsa guntu guntu ba yawa ne?
3⃣Shin idan aka kwatanta da yawan
dare da akeyi fitsari da wadanda ba ayi wadanne sukafi yawa?
4⃣-Wane irin abinci mutum yake yawan
amfani dashi watau hatsi ne kokuma yana anfani da abubuwa masu suger ne dayawa?
-5⃣Zà a tambayi mutum ko
yanada urinary tract infection koko babu?
6⃣Mutum yana zufa da daddare sosai
koko?
Sannan akwai wasu gwaje gwaje
da likita zai iya sawa ayi misali bayan physical examination watau yaduba mutum
sai Neurological evaluation sai urinalysis da urine culture na mutum
Sauran gwaje gwaje da kila
idan ba asamu abinda ake nema ba acan sai anhada dasu sune, uroflowometry da
post void residual urine measurement
***TREATMENT***
Treatment din wannan matsala
sai anyi hakuri, aiki tukuru dakuma bin ka'idoji da kila daza a shinfida, akwai
hanyoyin da ake treatment dayawa akwai na hannu watau ta amfani da wasu
kayayyaki da ake saye arika amfani dasu dukda anasamun matsala rashin
ingattattun kayayyaki din, sannan akwai magungunna na sha da ake anfani dasu
wajen warkarda matsalar akwai kuma har surgery anayi inta kama duka de ya
dogara ga abubuwa da aka gano ko aka fahimta suka har dasu matsalar
Misali akwai
1⃣-NAFC's Dry night solution kit,
cikin wannan dan akwatin akwai wata jikka da mutum ke sawa kamar
underwear ne, akwai wasu irin pads a ciki dasuke matuka hana fitsari kwance din
2⃣Akwai magungunna kamar yadda
nace akwai na asibiti wanda za a rubuta ma mutum saikuma na gida wanda za a iya
yi a gida insha Allah babba ko yaro amma zanfadi wasu da bazasu zama matsala ba
anan
3⃣Ayaba, idan babba ko yaro na
fitsari kwance a jaraba bashi Ayaba kwara ukku a rana insha Allah kullum kenan
za aga yadda yawan yin fitsari zairagu.
4⃣Cinnamon ko kirfa da hausa,
arika cin iccen munsan akwai iccen akwai powder to iccen za a ga kamar aswaki
yake to haka ake cinsa kamar aswaki din guda daya a rana kokuma idan cin yazama
damuwa sai asamu garin ahada da suger a yayyafa dan ruwa kadan zaki dunkule sai
arika breakfast dashi
5⃣Man zaitun arika dundumashi ana
shafawa a kasan ciki bawai kawai shafawa ba a'a shafawa sosai za ayi ayita
shafawa har kusan minti goma inza a kwanta ga babba da yaro
6⃣Zuma, arika ba yaro inde yakai
shekara biyu cokali Zuma karami daya in babba ne banban cokali daya na Zuma da
daddare
7⃣Apple cider vinegar watau tuffa
yana rage yawan acids na cikin ciki saboda haka yana rage bukatar yawan yin
fitsari arika zuba cokali daya a cikin cup na glass da ruwa anasha sau ukku a
rana
8⃣-Brown suger, kamar yara idan
jikin su yana warm basuyi fitsari saboda haka kuma Brown suger yana taimaka ma
jiki yazama warm, idan anaba yaro Brown suger kadan duk bayan cin abinci har
tsawon wata biyu ko kuma ahada Brown suger da black sesame seeds, clery seeds
awo daya ahada su arika ba yaro su Cokali daya karami duk safiya sannan abashi
cup daya na madara har wata biyu
Akwai su de da dama da ake
treatment na fitsari kwance wasu za a iya a gida wasukuma baza a iya a gida ba
sai ansamu kwararrun likitoci.
Zamu dakatq anqn sai rubutu naga a
iñsha Allah.
✍DR
SHUAIBU MB(KIWON LAFIYA)
Comments
Post a Comment