✍DR
SHUAIBU MB(KIWON LAFIYA)
***DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑***
***MATSALAR KIBA1⃣
Idan mutum nada kiba ko akace wance
ko wane nada kiba ana kallon mai ko kitse yayimasa yawa a jiki kenan. Kiba
takasu kishi biyu akwai kiba akwai mummunar kiba wadda takeda matsaloli fiyeda
dayar kibar, Yawanci idan mutum nada kiba kuma yanada tsawo, tsawon yakan
shanye kibar koya rage kibar, amma idan mutum nada kiba kuma bayada tsawo tafi
fitowa sosai sannan wasukuma kibar a cikin su take watau tumbi.Awasu mutanen
kiba wani abin alfaharine musamman a kasashe irin namu wanda sabanin wasu
kasashe inda mutane masu kiba ke kashe kudade dayawa don ganin sunrage kokuma
suncireta, inda wadanda basuda ita suketa kokarin ganin basu sameta ba ko
kadan. Saboda gwamnatocinsu suna kashe makudan kudade don wayarda kan mutane
akan illar kiba.
KIBA tanada lahani sosai ga
magudanan jini na zuciya dana kwalwa dasauran sassan jiki mutum idan
daskararren mai ya toshe magudanan jini dasuke gewaye da zuciya dakuma kwalwa
don sune suke bata kason jini
Wanda faruwar haka kan jawo matsala
ta mutuwar bangare da abin yashafa, hawanjini da yawanci masu kiba ke dashi
saiya karama zuciya aibu.
ABUBUWANDA SUKE KAWO KIBA
KIBA na jawo ciwon suger
batareda angaje shiba, da ciwon kashi da wasu cututtuka daji watau cancer
1⃣ -Gado shine babban dalilin zuwan
kiba saboda dayawa masu kiba gadonta sukayi
2⃣-Yawan cin abinci barkatai kokuma
fiyeda bukatar mutum
3⃣Akwai wasu cututtuka kuma dasuke
kawo kiba misali makoko, ko na kwayaye haihuwa mace
4⃣-Rashin motsa jiki, watau zaman
dirshen daga mota sai mota sai office ko shago sai parlow ayi kallo sai daki a
kwanta wanda yafi yawa a mata
5⃣-Akwai damuwa, tana sanya kiba
kuma tana sanya rama, itamade tanasa kiba
6⃣-Akwai kuma magungunna dasuke
haifarda kiba kamarsu na tsarin iyali dawasu magungunna daban
7⃣-Akwai cin abinci masu mai dakuma
irin dabi'ar ci a kwanta musamman nau'in abubuwa na madara dasu waken suya.
Akwai de dalillai dayawa dasuke hadasa kiba
***ALAMOMIN KIBA***
Nasan za ace to kuma kibama
har wasu alamomin gareta sabanin abu a zahiri da ake gani, eh akwai alamomin ta
ai tun farko nace kibar takasu kishi biyu ne ta yuwu mafi muni nake maganar
alamomin ta
1⃣Akwai hada cinyoyi yayin tafiya su
rika gugar juna kokuma a tsaya a tsaye ahada kafafu a sunkuyar da kai a kasa
batareda an sunkuyar ba,
aga cewa ko ina za a iya ganin
yatsun kafa amma masu teba watau tumbi kenan bazasu iya hango yatsunba wannan
kibace datayi muni
2⃣-Sannan awon nauyi na body mass
index BMI yakai maki 20-24 shine normal de amma maki 25-29 shine kiba, wanda
kuma yawuce 30 shine mummunar kiba. Idan akasamu sikeli kamar kilo 90 sannan a
gwada tsawo da tape irinna teloli da bangare da aka sa Cm lambar dayasamu
saiyayi sau ita misali tsawon sa yakai 175 saiyayi × 175 zai bashi 30625 saiya
rabata sau 1000 zaibaka 3.0 kunga idan kukayi × da nauyi kilo dinmu na 90
zaubada 30.
To kunga idan mutum mai nauyin
kilo 90 da tsawo na 175 kunga yanada ciwon kiba tayi matuka muni kenan
Shiyasa ake samun yawan
matsala hawanjini, suger, kitse, ciwon zuciya da mutuwar barin jiki
*** HANYOYIN KARIYA DAGA KIBA***
Rage kiba abune mai wahalar
gaske, ba karamin aiki bane, wani lokacin ma maimakon ragewa sai akara kokuma
arage kwana biyu kuma ayi wadda tafi ta baya muni, kuma zaman mutum lafiya
shine yarage kibar yakuma tabbatarda baisake yinta ba
1⃣-Rage cin abinci mai maiko kamar
su manja, man Gyada, ko gwaiduwar kwai watau yellow yolk na kwai, da cin nama
mai maski ko kitse, da man butter musamman mai color na dark blue amma mai
marfi light blue bayada matsala, sai manshanu da man kakidee
*** HANYOYIN RAGE KIBA***
1⃣ Ga masu mummunar kiba zasu
kauracewa wadannan abubuwa duka ne bawai su rage cinsu ba inde nasara akeso,
amma zasu iya cin kwai idan ancire yellow din kokuma kifi maimakon nama, kuma
arika yin abinci da mai bayada cholestoral watau free cholestoral oils
2⃣Yawan amfani da kayan marmari da
tsanwayen ganyayyaki suna tsane mai a jiki, hadasu kuka,
3⃣Saikuma hatsi amma wanda ba
a sirfa ba aka niko su a haka, saikuma oat shima hatsine amma na turawa
dukkansu sunada fibre dayake tsane mai kafin abinci yaje ga hanji,amma misali
kamar bayan break fast dasafe wajen 12pm na rana kafin launch ana iya amfani da
kayan itatuwa hakama da daddare
4⃣-Motsa jiki, wannan muhimman
gaba ce datake taka rawa sosai wajen magance matsala kiba misali tafiyar kasa
ta mintuna 30 a rana kokuma sirsirfa ta minti 20 a rana ga wadanda zasu iya ga
mashina na motsa jiki sunyi yawa ynz
5⃣-Rage yawan ciye ciye barkatai,
cin abinci sau ukku kokuma azimin masu kiba wanda ake ci sau daya a rana amma
yanada illa saboda yanasa mutum yarasa wasu kananan sinadarai da jiki yake
bukata kuma
6⃣-Duk bayan wadannan ga masu
mummunar kiba kuma suje asibiti a auna su watau lafiya su dakuma kitse dake
jikinsu sai afara basu magungunna na tatse kitse.
NOTE :Akwai wasu dasuke son
kara kiba kunga de matsala ta za aga ina kauce kauce idan akace anaso kara kiba
ya za ayi saboda illarta yasa bawai banason ayi kibar ba musamman mata, bayan
wadancan illolin kiba fa har haihuwa tana hanawa ga mace ko namiji musamman mata
kinda har chanza masu al'ada takeyi.
ALLAH YAKARA MANA LAFIYA MAI AMFANI.
Comments
Post a Comment