**MATSALAR RASHIN SHA'AWA GA MATA**



**DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑**

**MATSALAR RASHIN SHA'AWA GA MATA**

 Bansan yawan adadi ba amma matan musamman na aure dasuke da matsalar rashin sha'awa sunfi wadanda sukeda ita yawa sosai,idan mutum yana da matsalar sha'awa wadda take kowane lokaci dakuma wadda take zuwa ta tafi duk matsalar sunansu daya watau hypoactive sexual desire disorder HSDD. Dayake ana rayuwa tsakanin mutum biyune mace da namiji kuma samun wani daga cikin biyun nan da bayada sha'awa kan zama matsala ko barazana ga zamantakewa.

 **ALAMOMIN RASHIN SHA'AWA**

1⃣-Mutum yaji dukwani abu daya shafi sex baya son shi harta musturbation mutum yaji baya sha'awarsa

2⃣-Mutum yaji bayama tunani ko kawo ma ransa sex ko daya kuma ko anyi bayajin dukwani dadi da akeji.

 3⃣-mutum yarika damuwa, watau matsalar tarika damunsa.

**ABUBUWA DASUKE KAWO RASHIN SHA'AWA**

 Anrabasu hudu, matsalar data shafi abuna zahiri, matsalar data shafi tunani, matsalar hormones, matsalar data shafi mu'amulla ko zamantakewa

*1⃣-MATSALAR ZAHIRI**

 ♦-idan mace najin zafi ko bata gamsuwa yanasa taji bata sha'awar sex

♦-Akwai wasu cututtuka wadanda kesa mutum yaji baya sha'awar sex kamar ciwon kashi ko amasanin kashi, cancer, hawanjini, ciwon suger, ciwon jijiyoyi kona gabbai

 ♦-Akwai wasu magungunna da idan mutum na ko yataba amfani dasu na jawo wannan matsalar.

 ♦-Akwai yanayin tafiyar da rayuwa kamar shan barasa, shan magungunna barkatai, shan taba cigarrete, kiba dayawa, rashin motsa jiki

♦-Akwai tiyata musamman wadda tashafi nonon ko bangaren al'aura

**2⃣-MATSALAR DATA SHAFI TUNANI KO KWALWA**

♦-Akwai kasala ko mutuwar jiki

♦-Akwai fargaba da damuwa

♦-Akwai stress wanda yashafi na kudi ko na aiki

♦-Rashin structures ta jiki maikyau

♦ -Karancin girma, low self esteem mutim yarika jin bai isaba.

♦-Wadda aka taba cima mutumci ko akayi ma fyade

♦-Wadda ta taba jin rauni ko ciwo ko kamuwa da wata cuta daga sex

 3⃣-MATSALAR HORMONES

♦-Ga matanda suka kusa gama al'ada a rayuwa watau menoupouse

♦-Haihuwa da shayarwa ko juna biyu

 *-4⃣MATSALAR MU'AMULLAH KO DANGANTAKA TSAKANIN MA'AURATA**

♦-idan ba a rayuwa tare, irin wanda ake dadewa ba atare sai wasu lokuta

♦-Yawan rashin fahimta da fadace fadace tsakanin ma'aurata.

♦ -Rashin kyakkyawa isarda sako ko fahimtar sako, watau miji ko mata wani nada bukata amma ba asan yadda za anuna ba ko annuna wanda akeso ya fahimta yakasa fahimtar

♦-Amincewa da juna, rashin aminci da juna na jawo wannan matsalar

♦-Jin tsoro, misali rashin son daukar ciki

 **AKWAI ABUBUWA UKU DASIKE DA MAHIMMANCI WAJEN MAGANCE MATSALAR DAKUMA GANO DALILI**

♦-Akwai pelvic exam wadda likita zaiduba al'aura yaga ko ta kumbura, ko ta kaskance ko kuma a bushe take kinda inba niima itama matsala ce ga sha'awa ko kuma yaduba ko akwai spots

♦-Akwai awon jini dayakamata ayi kamarna level na hormones, diabetes, cholestoral, thyroid ko matsalar hanta

♦-idan ba aga kome ba sai atura mace zuwa ga kwararru akan ilmin jima'i sukuma suyi theraphy dasauran abubuwa daya dace

**TREATMENT**

Akwai hanyoyi guda uku dukda de a gida ma akwai hanyoyi da za a iyabi don magance matsalar amma yanzu muna maganar asibitine.

♦-Akwai shawarwari da akan bada da ilmi da ake karama masu mstsalar da kokarin taimakawa wajen warware matsaloli na gida ko na zamantakewa.

♦-Sai magungunna da likita kan iya rubutawa ma mace taje tasaya

♦-Hormones theraphy, wannan shima yana taimakawa sosai

**A GIDA**

♦-Motsa jiki nada amfani

 ♦-Rage stress

 ♦-Tattaunawa tsakani watau mikike so kaima mikake so, wane lokaci, ta yaya dikde abine mai kyau arika tattauna mgnr sex tsakanin ma'aurata

♦-kada a ware wasu kwanaki ko lokaci kawai ace ranar za ayi, a a kawance a harkar sex na maido mutim akan turbar sha'awa

♦-Kara gishiri da kayan dandano ga rayuwar sex nasa abubuwa su dawo normal, watau kamar dabaru na kwanciya iri daban daban, chanza lokutta, chanza wuri, yin wasanni sosai kafin sex, sex chats kafin farawa dik suna taimakawa

♦-Kauracema shan barasa, cigarrete, shan magingunna zasu taimaka

♦Akwai wasu mai da magungunna da ake amfani dasu saidai kila ko sudanyi wuya misali kamar AVLIMIL ga mata, ko messaging na ZESTRA OIL da ake shafawa, yafi PLACEBO OIL da ake yawan amfani dashi.

Comments