*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
*MATSALOLIN JININ AL'ADA*
Mata dayawa na jinin al'ada kwanaki hudu zuwa
bakwai, daya daga cikin matsalolin al:ada shine yin kwanaki kasada 21 ko samada
kwanaki 35 na circle din mace. Rasa jinin al'ada sau ukku a jere watau watanni
ukku a jere sannan kuma inya zo yazo dayawa kuma da haske sabanin yadda yake
zuwa yana nuna matsala
Yawanci mata sunayi kwanaki 28
na circle, amma normal circle na mace shine yake kamawa daga kwanaki 21-35.
Sauran matsalolin al'ada sune bayan kasada kwanaki 21 ko samada kwanaki 35 na
circle, kokuma rashin zuwan jinin al'ada a jere sau ukku ko fiye ahaka, jini
yarika zuwa sosai kuma da haske, jinin al'adar da yake wuce kwanaki bakwai, yin
al'ada tareda tsananin ciwon mara, amaiy, tashin zuciya, da fitarda jini
tsakanin al'ada biyu ko bayan jima'i ko kuma bayan menopouse.
Rashin zuwan jinin al'ada
kwanaki 90 a jere ba lafiya bane inde ba mace nada cikiba, ko shayarwa, ko
menoupouse, ko wadda takai shekaru 15-16 sannan tafara al'ada ko wadanda suka
fara yin nono da shekaru biyu zuwa ukku har zuwa hudu sannan suka fara jinin
al'ada.
Yin al'ada wadda ba kasafai akeyinta
ba
Wahala sosai lokacin al'ada,
amma don yin ko jin wasu alamu dabasu yi tsanani ba ba damuwa.
Akwai abubuwa dasuke iya kawo
matsalar al'ada ga diya mace kamarsu
🔸- *stress* akwai mata
saboda hidimar kasuwa, aiki, karatu ko gida sukan samu kansu cikin wannan
yanayin na matsalar al'ada
🔸- *Tsarin rayuwa*
kamar chanjin abinci, nauyi, kiba, tafiye tafiye, motsa jiki dayawa
🔸-Tsarin iyali dukansu
🔸- *uterine polyps ko
fibroids* kamar karine na hannuwan mahaifa yawanci suna zuwa da zubarda jini
lokacin al'ada dakuma jin matsanancin ciwo lokacin al'ada, wani lokacin yakansa
ma mafitsara pressure sosai yakawo matsalar rashin rike fitsari, shi wannan
karin yakasu kishi biyu kananan kamar yayan apples suke manyan kuma kamar
grapefruits
🔸 *-Endometroisis,* wata
tsokace datake lines da mahaifa saita rika kecewa dukwata saita fitarda jini
tareda jini al'ada shiyasa jinin ke zuba dayawa, shi wannan endometroisis din
yana faruwa ne lokacinda tsokar tafara girma bayan mahaifa saita hade da
hannuwa ko fallopian tubes watau ovary ko fallopian tubes wani lokacin takan
manne ma hanji tarika girma a jikinsa kokuma wata gaba dake wajen narkarda
abinci a kalkashin ciki.
Tsakanin takashi watau bututun
da kashi ke fitowa dakuma mahaifa,, *endometroisis* yana haifarda rashin
daidaito na al'ada, yanasa rika jin ciwo sosai wajen al'ada, yanasa arika jin
ciwo lokacin saduwa, kuma shi wannan ciwon marar zai iya faruwa kafin ko bayan
al'adane
🔸 *-pelvic inflammatory
disease,* infection ne dayake shiga mace ta vagina ta hanyar saduwa saiya yadu
zuwa mahaifa da sauran genital area sannan kwayoyin bacteria din zasu iya
shiga ta bututun haihuwa, ta dalili haihuwa ko bari
Alamominsa sunhada, fitarda
jinin al'ada dayawa tareda karni ko wari maiyawa, rashin tsayayyen al'ada,
ciwon kugu da mara musamman lokacin al'ada, zazzabi, tashin zuciya, amai,
gudawa
🔸- *Pcos, ovaries* hannun
mahaifa suna samarda androgens wanda na mazane maimakon na mata to sai ruwa
kadan yacika wata yar jikka dake tareda hannun mahaifa wanda sai anyi
ultrasound ake iya ganin sa. To saboda chanjin da hormones din yayi maimakon na
mace saiya zama na namiji saiya hana kwayaye da mace ta saka su zama matured,
wani lokacin macenda takeda pcos jinin ta na wasa koma yadauke duka. Daga cikin
alamun da akan iya fahimtar pcos sune fitowar gashi ko gashi dayawa inda ba a san
mace dashiba kamar a kirji, gemu, kafa dasauransu
🔸 *_premature ovarian
insufficiency* , yawanci yana faruwa ne ga mata masu shekaru kasada 40 ta yadda
wadanna hannuwan mahaifan zasu zama basu aikinsu sosai, wanda daga karshe mace
nada kananan shekaru saitaga jinin ta gaba daya yadauke
Sauran abubuwanda suke kawo
irin wannan matsalolin sune, cancer ta bakin mahaifa ko mahaifar, magungunnan
tsinke jini, cikin bayan mahaifa dasauransu.✍ *DR SHUAIBU MB* KIWON LÀFIYA WHATSAPP GROUP
Comments
Post a Comment