Me ke kawo matsanancin ciwon ciki lokacin Ovulation



*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA*🚑🚑1⃣1⃣2⃣                         
 Me ke kawo matsanancin ciwon ciki lokacin Ovulation❓
Kuma wane dalili ne Yasa ba kowace mace bace take samun irin wannan ciwon❓ Dan sai inji wasu Matan suna cewa basu sanin lokacin da suke yi❓
🤔Ciwon yana farawa ne daga kadan zuwa dayawa kuma yawanci cikin mintuna yake tafia Amma yana tafiya KO yakai har hour daya ko fiye da haka.
Wani lokacin ciwon marar yana zuwa ne bari daya ya danganta da ovary watau hannun mahaifar daya saki kwayayen a wannan watan
Wani lokacin yakanzo da Dan bleeding wani lokacin da discharge,
Wasu suna famada tashin zuciya musamman idan ciwon marar yayi tsanani sosai.
 Kowace mace na iya samun ciwon marar lokacin ovulation dinta inde tana al"ada.
 Abunda yasa akejin irin wannan ciwon lokacin ovulation, lokacin da kwayayen suke girma akwai wani ruwa dasuke haduwa dashi to sai kwayayen da ruwan da dan jini su hadu sai ovary din yayi realising dinsu tare
To shi wannan zafin ko ciwon marar yana zuwa ne saboda jini da ruwa dinda suke haduwa bakin marar
Kuma shiyasa suke tafiya dazaran ansaki kwayayen
 Amma ya za'ayi ko ya mace zatagane ciwon marar yanada alaqa da ovulation ne:
Shine zataga sati biyu kafin ko bayan daukewar jinin al'adar ta kuma ciwon yawanci gefe daya ne yake zuwa
 Amma idan ciwon yayi tsanani ana zuwa asibiti don akwai wasu matsalolin dasuke Sanya ciwon marar yayi tsanani a lokacin
 Kamarsu Endometroisis, ko cysts, wajen dubawarda likita zaiyi lokacin dubawar keke da keke inya kasa ko ganin bai gansu ba saiya tura zuwa awon jini, ko ultrasound ko x-rays
 Bawani magani tsayayye da akesha don kariya daga ciwon saidai irin magungunna da mata Kesha na rage radadi lokacin al'adar su dakuma gashin mara da ruwan dumi dakuma wanka da ruwan dumi
Sai kuma idan mace bata bukatar ovulation din duka kamar wadanda Basu bukatar haihuwa suna amfani da pills wanda ke daukeda estrogen da progesterone
idan ovulation yazo da zazzabi, amai, zafi lokacin fitsari, zafi ko radadi ko wurin yayi ja inda akejin zafin kokuma ciwon yawuce hour 24 to aje asibiti
*DR SHUAIBU MB*                     Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com

Comments