✍
DR SHUAIBU MB (KIWON LAFIYA)
**DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑**
**SHAFIN TAMBAYOYI**
❓Dr me yake kawo asma koma na
inheriting❓❓
🤔✍To kusan kishi uku cikin hudu na asthma cases gado ne da
akeyi idan daya daga cikin iyaye nada ita ko yan uwan iyaye nakusa ko na yaro,
saboda wanda yakeda iyaye daya ko biyu masu ita suna cikin hadarin kamuwa da
ita daga uku zuwa shidda akan wadanda basuda iyaye masu ita.A yara maza sunfi
kamuwa da ita akan mata saboda hanyoyin iskan yara maza karamine akan na
mata,amma a mataki na matasa yan 20 years banbancin yana daidaita cewa duk
yawan dayane,amma a matakin shekaru 40 zuwa sama kuma mata sunfi maza yawa
wajen kamuwa da asthma
BUGUN JINI (PULSE), bugun jini
watau yadda zuciya take bugawa duk cikin dakika ko minti daya ke hutawa ga
mutaneda shekarunsa yawuce koya kama daga goma zuwa sama bugun jini ko bugawar
zuciyarsa zaikama daga 60-100 bpm wannan shine normal.Amma ga mutanenda suke
motsa jiki manya zaikama daga 40-60 bpm ne shima wannan normal ga irin wadannan
mutane,amma ga mutanenda bugun jininsu yawuce 100bpm a cikin minti daya koda da
digo ne wannan yazama ba normal ba.Akwai abubuwa dasuke haddasa irin haka, wasu
na wani dan lokaci ne wasu kuma dalillan bana dan lokaci bane.
**DALILAN DASUKE NADAN LOKACI**
1⃣-Rashin lafiya, zazzabi, rauni, ko
infection, ko anada karancin kwayoyin jini na halitta aneamia zuciya tana
halbawa fiyeda yadda takeyi watau fiyeda 100 a cikin minti daya donta samarda
isasshen oxygen ga duka jiki dakuma tabbatarda wasu sassan jiki na aiki.
2⃣-Emotional stress, kamar bacin
rai, ko tsorota, ko fargaba kokuma fada duka sukan sa halbawar zuciya yakaru
fiyeda yadda takeyi amma da zaran stress din yaragu koya tafi zata dawo normal
tana bugawa.
3⃣ -physical exertion, motsa jiki
yana haddasa wannan yanayin na bugawar zuciya don ta tabbatarda taba nama da
sauran tsokokin jiki oxygen din da suke bukata
4⃣-Drugs, akwai magungunna dasuke
bayarda irin wannan reaction din na karuwar bugawar jini
5⃣-Temperature, cikin sanyi idan
mutum najin sanyi yanayin halbawar zuciyar na yawa yawuce yadda yake normal
saboda tana kokarin dumama fatane hakama lokacin zafi tana kokarin sanyaya
fatar ne.
6⃣-Gylocogen level, idan yawan
suger na cikin jini yayi kasa, zuciya nawuce yadda take bugawa saboda kokarin
ta gamsar ko cike gurbin suger da babu a tsokar jiki dakuma samarda energy.
7⃣-Dehydration, idan ruwan jikin
mutum yayi kasa shima tana kara bugawa sabanin yadda take bugawa saboda jini
baya samun wucewa sosai a cikin hanyoyinsa sakamakon ruwan dake taruwa a cikin
su, to sai zuciya tarika halbawa sosai donta fitarda wannan ruwan jinin yasamu
damar wucewa
8⃣-Caffeine, Caffeine beverages,
snacks kamar chocolate coffee beans suna kara bugun zuciya
9⃣-Barasa da cigarrete, shiyasa
cigarrete take haifarda matsalar ciwon hawan jini na lokaci mai tsawo.
**DALILIN DAYASA BUGUN JINI
WANDA YAKE BAYA TAFIYA**
Idan aka karanta can baya nace su
wadancan dalillan sune wadanda suke kawo bugun jini yawuce yadda yakamata amma
nace su masu tafiya ne watau idan abinda yakawo shi yatafi shima yatafi.Nankuma
matsalolin ko dalillan da suke haddasa bugun jini yawuce ka'ida anma su suna
nan.
1⃣-Lalacewar jijiyoyi, yana faruwa
ne a cikin peripheral nervous system dasuke da rassa a cikin kafadar mutum
dakuma kafar mutum idan suka samu matsala suna shafar jijiyoyin dasuke da alaqa
da zuciya.
2⃣-Akwai rashin daidaito na gishiri
a cikin jikin mutum ko bugun zuciya wanda suke sa zuciya tarika bugun jinin
fiyeda yadda yakamata dasauri kenan anace masa arrhythmias
3⃣-Anemia, karancin kwayoyin
jini jajjaye watau red blood cells dalili rashi isasshen sinadarin iron a cikin
jiki yana sanya yawan bugawar zuciya, saboda tana kokarin ko aikin samarda
jinin da ba isasshe ba a jiki
4⃣ -Diabetes, ciwon suger yana
haddasa matsalar
5⃣-Hyperthyroidsm yana sa
wannan matsalar shima wanda kode ayi treatment kokuma ayi surgery
6⃣ -Congestive heart faillure, idan
zuciya tana aiki tukuru donta rika halba jini yanasa tarika bugawa fiyeda yadda
tasaba, wannan na iya jawo bugawar zuciya.
7⃣-Hyperthyroidsm yana sa wannan
matsalar shima wanda kode ayi treatment kokuma ayi surgery
**TREATMENT**
Treatment din wannan matsalar
ya banbanta ya dogara ga abinda yakawo shi, shekarun mutumin da yanayin
lafiyarsa dasauran wasu abubuwa.Idan aka fahimci miyake kawo shi sai ayi
kokarin a takaita gudun ko bugawar dasauri don a kiyaye afkuwar abin a gaba
dakuma irin matsalolin da zai iya haddasawa,wani lokacin kuma ana rasa dalili
matsalar to irin wannan sai ayi tunanin sauran theraphy din.
Hanyoyin da akebi don arage
wannan saurin bugawar zuciyar sunhada da tari, yunkurin kamar za ayi bayan gida
sannan sai asamu ice block a dora akan fuska,sannan a kiyaye amfani da dukwani
abu dayake da coffee a ciki dukda de mutane sun banbanta amma ko yazama sai
ansha asha cup daya a rana.Ta bangaren magungunna kuma akwai magungunna wasu
anasha a baki wasu kuma allura ne wani lokacin ma har overdose take kamawa amna
duk wannan sai asibiti.
♦Black tea, cola soda ko chocolate a
kiyaye anfani dasu
♦A yawaita anfani da abubuwa dasukeda
potassium dayawa A cikinsu kamarsu ayaba, avocados, vegetables, potato, madara
da lemun fata.
♦Akwai wani ganye amma daga china
yake gaskiya kuma antabbatarda yana maganin wannan matsalar sosai anace dashi
motherwort ana suraci dashi ne idan aka debi cokali daya aka zuba a tafasasshen
ruwa cup daya sai arika shakar suracin,daga baya sai asha.
♦ Akwai shima wani magani na india
ne anace dashi Arjuna shima yana magance matsalar duka dashi da wancan
motherwort din ana kawo su a nigeria.
♦Valerian shima de a china
suke yin amfani dashi kuma yana aiki gaskiy shima anasamunsa anan.
♦Idan abin yataso kuma arika
numfashi ta hanci kamar seconds 4,sannan sai arike numfashin second 4, sai
asaki numfashi ta baki shima second 4, ayi haka sau biyar zuwa goma insha Allah
za aji ansamu lafiya. Kokuma asamu wuri dayake da shiru bawani motsi a zauna
sai akawo ma rai tunanin wata halitta dake kusa.Yawan zaman da tunani Yawan
samun saukinka.
♦ Akwai yoga, zaka iyayi a gidanka
ko a yoga class.
♦Motsa jiki, zaitaimaka wajen
zagayawar jini, dakuma rage ma mutum stress, akalla minti 30 arana sau hudu ko
biyar a sati.
Allah yabamu lafiya.
Comments
Post a Comment