*MEKE KAWO KAIKAYIN HAKORA KO DASASHI KO SHINE AMASANIN HAKORA



 *DR SHUAIBU MB KIWON LAFIYA*
*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*      *MEKE KAWO KAIKAYIN HAKORA KO DASASHI KO SHINE AMASANIN HAKORA*❓
 Wannan kaikayi na hakora ba amasanin hakora bane akwai kaikayi hakora da yake faruwa bayan cin abinci ko bayan anwake su ko idan mutum bayada lafiya.
 Akwai dalillai dayasa hakora watau dadashi ke kaikayi akwai bacteria wani lokacin idan ta taru tsakanin hakora da dadashi anajin kaikayi.
 Akwai kuma allergy na fey fever shima yana haifarda kaikayi hakora
Akwai har yaude bacteria din idan mutum yaci ko yasha abu mai zaki saitazo ta daddatsa su a tsakankanin hakori da dadashi mutum kafin ta cinye su za arika jin wannan kaikayi.
Akwai farkon alamun ciwon dadashi watau *gingivitis* shima yana haifarda kaikayi hakora
** Yammata da suke balaga dakuma mata masu ciki da wadanda suka gama al'ada su duka a rayiwarsu watau menopouse suma suna jin irin wannan kaikayi,
Jin ciwo ko bushewar baki suma suna haddasa kaikayi hakora
 Saboda haka shawara aje aga likita hakora, amma kafin nan za a iya wanke baki ko kuskure bakin da ruwan dumi da gishiri a ciki sau ukku a rana, sannan arika wanke baki da antibacteias mouthwash. *DR SHUAIBU MB(KIWON LAFIYA)*

Comments