*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑*
Meke kawo yawan nishi koda bacci na tashi sai in dinga
nishi kuma har inajin karan nishi
Kuma bawai in ina aikiba ko a zaune
nake bana komai❓
🤔Duk lokacin da mutum yake
motsa jiki ko wani aiki ko hawan bene irin wannan takan faru gareshi saboda
jikin mutum yana bukatar oxygen fiyeda kafin haka
Irin wannan nishin haka
lokacin da mutum bayayi kome ko aikin kome kawai alama ce dake nuna jikin mutum
yana bukatar oxygen sosai a lokacin
Wannan kuma zai iya zama
karancin iska dayake shiga ta hanci ko bakin mutum kokuma oxygen kadan ne yake
shiga cikin magudanar jini
Don a fahimci minene yake kawo
haka akwai bukatar sanin yadda iska ke shiga ta hanci da baki zuwa hunhu
Akwai abubuwa dasuke iya kawo wannan
yanayi kamar
🔹Yana shiga wata mabusa
watau baloons haka kamar jikkar iska ana kiranta alveoli daga nanne oxygen zai
tafi zuwa magudanan jini zuwa cikin jiki
🔹-Mura innace mura
tahada da duk wata nau'in mura saboda duk lokacin da mutum ke mura oxygen yana
samu tsaiko cikin hanyoyin iskan, wani lokacin kuma majina da jiki ke haifarda
ita dayawa kokuma sukan su hanyoyin da iska ke shiga ta hanci su kumbura watau
sinus infection
🔹-Allergy, saboda wasu
abubuwa a mahalli da mutum ke sha, ko ci ko mu'amulla dasu
Garkuwar jiki takan maida
martani wajen kokarin yakar bakon abu daya shiga jiki
Za a iya gane idan allergy ne
ta hanyar jin ko ganin wadannan alamomin
♦ Atishawa, zubar hanci da ido,
zazzabi musamman na dare, kuraje, tashi zuciya da gudawa
♦-Asthma wannan basai na kara bayani
ba
Ana iya gane haka ta wadannan
alamomin, tari da majina da jini wani lokacin, zazzabi, ciwon jiki, kasala,
ciwon kai, rashin dandano, ciwon kirji
♦-Infection na hanyoyin iskan ko
numfashi, wadanda suka hada infection na hunhu, tb, dasauran
♦-Kiba itama tana kawo wa
♦-COPD wata cutar hunhu ce
♦-ANXIETY, kwanaki nayi maganar
anxiety, za a iya gane hakan ta hanyar yawan bugawar zuciya, jiri, zufa sosai,
shaking, damka a ciki, gudawa
♦-Cancer ta hunhu
Idan kuma ana bacci ne ake jin
haka to matsalar itace akecema *_obstructive sleep apnea_* sauran alamomin ta
sune
🔸-matsalar zuciya
🔸 Munshari
🔸Ciwon kai dasafe
🔸 Yawan bacci rana
🔸 Yawan mantuwa ko maida
hankali akan abubuwa dasuke mahimmai
🔸Kiba
Sauran abubuwa dasuke sanya
haka lokacin bacci sune
🔸COPD
🔸 Gazawar zuciya
Toshewa hanci ko infection na
hanyoyin iskan ko numfashi
✍ *DR SHUAIBU MB*
Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail
dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blog site dinmu
kiwonlafiya1.blogspot.com
Comments
Post a Comment