*MENOPAUSE*



*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYÀ🚑🚑* *MENOPAUSE*
 Menopause, wani lokacine da mace ke zuwa inda zata gama jinin al'ada ta gaba daya kuma bazata sake daukar ciki ba lokacinda ovaries dinta zasu daina aiki, kada amanta su wadannan ovaries din sunada matikar mahimmanci da ayyuka dasuke yi a jikin mace banda kwayaye dasuke samarwa suna kuma sakin kwayaye zuwa fallopian tubes inda sperm yake yana jiransu don a kyankyashe su
Ovaries suke samarda wannan hormones din na estrogen, sannan kuma hormones dinda yake samarda cigaban jikin mace daya hada da nono, gashin jikinta, shape din jikinta, da kariya daga kashinta dakuma regulating na al'ada. *SHEKARU NAWA MENOPAUSE KE ZUWA*❓
Matsaikaiciya shekara itace shekara 51 amma kafin wannan shekarun menopause na zuwa ta hanyar bayyanar wasu akamominsa, wasu matan kuma na riskar sa a shekaru 45-50 inda wasu kuma na riskar shi cikin shekaru 30-40 ga wadanda suka riske shi da wuri kenan.
Akwai wadanda ma saisunkai shekara 60 ko fiye sannan su riske shi.
Akwai kalubale ko matsaloli dayawa da menopause yake zuwa dasu a matakai ukku, na farko akwai kafin zuwanshi, zuwanshi dakuma bayan zuwanshi.          *KAFIN ZUWANSHI* wannan wani lokaci ne da idan mace takai wasu shekarun daga 30 abinda yasama al'adar ta nayi mata wasa wanda kuma bawani dalili mai karfi musamman yana zuwa da wasu alamomi yana nuna menopause yana tunkaro maxe watau tsufa, rayuwa zata chanza alamar yawan kwayayenta sunfara raguwa, ovaries dinta sunfara rage aiki,
Babban abu mai mahimmanci shine mata su fahimci wannan susan da zuwansa don yana zuwa da kalubale dayawa matuka domin a shirya managing din su yadda zasu zo dasauki.
Dayawa mata kanyi kokarin boye alamominsa ko cewa suna cikin damuwa ko jin chanje chanje a jiki to wannan yana kara ta'azzara matsalar sosai,Kowace mace tun lokacinda aka haifeta aka halitta yawan kwayayenta a Kowace ovaries, lokacinda take tasowa tana zama adolescence lokacin a centre ta kwalwarta akwai wata gaba da take kulada balagar mace zata fara zama matured tafara samarda duk wani abu watau halitta ta kawar mace irinsu nono.
 Zata fara al'ada, duk wata daya daga cikin ovaries din Zata saki kwayaye idan akwai aure sai a kyankyashe inkuma ba aure bayan sati biyu da nasa su saisu rube a fitarda su shine al'ada.
Shekaru sunata tafiya, ovaries na cigaba da saka kwayaye sukuma sakesu sannan sukuma kwayaye kode su zama ciki ko su lalace ammade sunata karewa daganan sai nasa kwan yazama yana raguwa sai aga mace tana bleeding kuma ba al'ada ba.
 Gaba daya lokacinda mace take al'adarta lafiya lau wadannan ovaries din suna samarda hormones kowane wata shiyasa akejin wadannan cramps din lokacin al'ada
 *ALAMOMIN MENOPAUSE*♦-Rashin tsayayyen al'ada kokuma yin bleeding da baida tsayayyen lokacin zuwa kokuma idan yazo zaizo dayawa da tsananin cramp fiyeda baya
♦ -Hot flashes ko flushes, mace tarika jin zafi a wuyanta da sashen fuskarta zuwa wasu sassan jikinta sai zufa kuma zufa sosai yana iya daukar lokaci sosai haka na faruwa
♦-Nono, zasu kara girma za aga kamar ruwan Nono idan aka taba su
♦-Yawan tashin zuciya, wata zaizo mata akai akai wata kuma abin yana munana sosai harsai ankaiga treatment
♦-Zufar dare, mace zata rika zufa da da daddare sosai hartakaiga tana tashinta daga bacci kokuma tahanata baccinma wanda saiya jawo da rana jikinta ya mutu tarika wuni cikin damuwa
♦ -Kara nauyi ko kiba kokuma zubewa lokaci kankane, ga yawan jin yunwa
♦-Rage damar daukar ciki, saboda ovaries sunrage yawan kwayayen da suke saki shiyasa zamuga yawanci yanmatan da suka kai shekara 35 batayi aure ba saikaga dayawa ko ansamu ciki sai ansha wuya♦-Ciwon kashi ko dandakar kashi, saboda kashi yana rasa sinadarin calcium a cikin        ♦-Rashin annashuwa, za aga mace koba ayi mata kome ba ranta na baci wani lokaxinma har dangantaka yake shafa
♦-Karin kitse marar kyau a jiki
♦-Rashin sha'awa ko raguwar sha'awa amma shekarar da ko yan watanni kafun afara jin alamomin menopause za aji wata irin sha'awa mai karfi tana damun mace har manaki zatarika yi taji ko lokacin baya bataji haka ba daganan kuma a hankali saita rika fade shikenan
♦ -Bushewar gaba, gaba mace zaifara Bushewa sai tarika jin zafi lokacin jima'i
♦-Matsalar mafitsara, sai mace taji tana yawan fitsari ko jin fitsari, kuma atishawa ko tari mai karfi yana iya kawo fitsari kawai yafito
♦-Wani lokacin mace zataji alamomi komi na diabetes har awon diabetes ayi amma babu, hakama ayi tunanin gout ne shima aga babu kokuma akwai amma bada yawa ba. Zamuci gabà insha Allah. *DR SHUAIBU MB*

Comments