Mijina ne yake fama da ciwon ciki tsawon shekara goma yana fama dashi kuma baya damunsa sai kusan asubahi kamar karfe 4 har gari ya waye yaje asibiti har ya gaji shine muke neman shawara
✍
DR SHUAIBU MB (KIWON LAFIYA)
**DAGA ZAUREN KIWON LAGIYA🚑🚑**
**FILIN TAMBAYOYI**
Dr mijinane yake fama da ciwon ciki
tsawon shekara goma yana famadashi kuma bayadamunsa saikusan asibahi kamar
karfe 4 hargari yawaye yaje asibiti har yagaji shine muke neman
shawara Dr.❓
🤔✍Ramin ciki yana dauke da ko tattare da sassa dayawa a
cikinsa tundaga hanta, spleen watau saifa, pancrease watau wata gaba ce datake
dauke da ruwanda yake datsa abinci zuwa kanana, gallbladder, koda, hanji karami
ko babba. Shi ciwon cikin anasamun saukin fahimta wane irine ta hanyar fahimta
ta bangare dayake saboda duk ciwon cikin da za ayi yana fitowa ne cikin daya
daga cikin wadannan bangarorin na bangaren dama ko hagu ko saman ciki watau
right upper quadrant (RUQ), epigastric pain da left upper quadrant (LUQ).Ciwon
ciki akwai wanda yake mai sauki kokuma wanda yazama ya ta azzara, bayada wani
lokaci da za ace mai sauki ko wanda ya ta'azzara yake dauka don dayawa mai
sauki ne ke zama wanda ya ta'azzara amma idan bawani chanji tsawon
shekaru kamar na mijinki shine yazama chronic kenan watau ya ta'azzara.
**CIWON CIKI NA BANGARE DAMA**
Yana faruwa ne daga kalkashi
awazzun mutum wani lokacin yatafi zuwa kasan cikin daga gefen damar zuwa sama
wajen kirji yadawo ya gewaya zuwa baya zuwa bangaren hagu ta dalilin wadannan
abubuwa kuma yawanci sai wannan gall bladder din ya rufe yazama yahana wannan
ruwan madaciyar wucewa kamar yadda yasaba, rauni ma a wajen yana daya daga
cikin abubuwa dasuke kawo wani ciwon ciki da ake kira BILLIARY COLIC wanda yake
daukar mintuna 30 zuwa hour daya amma wani lokacin yana wuce hour daya ma
harsai dai ita wannan jikkar madaciyar ta samu hanya ta tura zuwa hanjin sannan
za aji ansamu sauki.
1⃣-Gallstone, wurine da ake ajiye
madaciya wadda hanta take saki ko samarwa saboda narkarda maiko da muke ci sai
ruwan madaciyar yafito daga jikkar madaciyar zuwa gallstones zuwa karamin hanji
inda acan ne ake chakuda abinci da madaciyar
2⃣-Acute Cholecystitis, shikuma
wannan kumburin gallbladder ne wanda shine yake haifarda wancan rashin wucewar
ruwan madaciyar na farko danake magana. Wanda keda irin wannan matsala za'aga
yana famada ciwon ciki daga sama dakuma amai ko tashin zuciya tareda zazzabi
3⃣-Acute cholangitis shikuma yana
tasirantuwa ne ta dalilin wannan gallbladder din De wanda yake jawo kwayoyi
bacteria su shiga yana zuwa da zazzabi, da yellow color na idanu da fata dakuma
ciwon ciki wanda ita wannan ake kira da charcot's triad
4⃣-Sphincter of oddi dysfunction,
shima de duk yanada alaqa da jikkar madaciyar kuma yana budewa ya kulle, shi
wannan wata gaba ce datake controlling yawan madaciyar da zata fito to idan ta
bude shikenan idan kuma bata bude ba sai ciwon ciki wanda wani lokacin yakanzo
da tashin zuciya, amai, zazzabi da ciwon jiki, da gudawa kuma yawanci wadanda
akacire ma gallbladder sunfi samun irin wannan matsalar
5⃣-Hepatatis, ciwon hanta kila
basaina yi dogon bayani ba kuma hepatitis A, hepatitis B, hepatitis C, duka
suna zuwa da ciwon ciki
6⃣-Budd-chiary syndrome, shi
wannan baicika samun mutane ba gaskiya don cikin mutum million daya akansamu
mutum daya kawai dashi yana kama wurare gudun jinine dayake tafiya zuwa ga
hanta
7⃣-Perihepatitis, kokuma fitz-hugs
curtiss syndrome, kumburi ne nawani shafi na hanta amma yafi damun mata yana
zuwa da atishawa, tari, matsala numfashi da zirga Zirga.
**CIWON CIKI NA TSAKIYA*
Wannan shine yake faruwa daga saman
ciki dayake faruwa daga kashin numfashi dayake wanda yake like da kirji dakuma
callerbone watau kashin da yake zuwa ga wuya zuwa sama cibiya wanda a dunkule
duk ciwon ulcer da akeda su tanan ne suke kamar gastric ulcer, ulcer ta ciki
data farkon karamin hanji watau duodenal ulcer, wanda gaba daya biyun akecema
PUD
peptic ulcer disease.
♦ GERD, shima yana cikin abubuwa
dasuke haifarda irin wannan ciwon na saman ciki kuma yana faruwa ne daga
matsalar rashin narkewa abinci wanda kusan kowane mutum yana samun heartburn a
rayuwa ko sau daya ne bayan gama cin abinci amma idan anasamu haka sau biyu a
sati zuwa sama shine yazama GERD
♦ GASTRITIS, shima wannan ulcer ce
ta ciki da za arika jin zafi ko radadi akan kirji wanda wani infection yake
haifarwa watau H. Pylori kuma wani lokacin amai da tashin zuciya
**CIWON CIKI NA BANGARE HAGU**
Shi wannan ciwon ciki na bangaren
hagu saifa yake kawo shi.
**CIWON CIKI NA KASAN CIKI**
Abubuwa dasuke kawo irin
wannan ciwon ciki na kasa sunhada da appendix, kari, kidney stone dasauran su.
**CIWON CIKI DAYAKE YADUWA**
Bawani wuri tsayayye da irin
wannan ciwon ciki suke kuma duk yawanci sunhada da hanji ne dakuma cancer.
**Akwai irinsu murar ciki, da
matsalar rashin narkewa abinda mukanyi amfani dasu kamar nau'ikan madara
dasauran su,Sauran wasu hanyoyin kuma sunhada da yadda jiki ke aiki kamar ga
mata jinin al'ada, matsala hanji da abinda yashafi dabi'ar cin abinci,
magungunna da guba. Sannan akwai abubuwa dasuka shafi rayuwa misali kamar
stress dayawa, damuwa ko fargaba, ko personality ko social stuation na mutum.
autotune Free Download
ReplyDeletestellar phoenix windows data recovery key generator
ReplyDelete