*RABE RABEN TSARIN IYALI*



*DAGA ZAUREN KIWON LÀFIYA🚑🚑*  *RABE RABEN TSARIN IYALI*
 Zankasa rabe raben akan yadda suke ayyukanku misali zamu iya kasasu gida ukku, tsarin iyali dasuke da makangari ko suke hana manniyi shiga ya iske kwayaye, sannan akwai wadanda kuma suke hana mata suyi ovulation watau nasa kwayaye sannan akwai wadanda sukuma suna bari ayi fertilization watau manniyi yahadu da kwayayen amma kuma suhana aiwatarwa, watau suhana kwayayen da akayi fertilization din kyankyashewa  cikin mahaifa .
    Kenan idan muka duba akwai wadanda su suna aikinsu a mataki na farko, wasu kuma a mataki na biyu, wasukuma a mataki na ukku watau mataki na karshe Kenan.
 Tsarin tazarar iyali akwai na wani dan lokaci akwai kuma na din-din akwai kuma irinna gaggawa dukkansu sunada irin tasu illolin kokuma ace matsalar wanda yakamata dukwadda zatayi suje tareda maigidanta ayimasu bayani su jinjinna kowane suji kuma suyi shawara kafin yanke hukunci
1⃣ *-Hormonal Birth control method,* shine ya kunshi pills watau kwayoyin da akesha dikda de sun rabu daban daban, patches, implants, vaginal ring
2⃣ *-Barrier Birth control methods,* shine wanda yahada da condom, cervical cap watau hular bakin mahaifa, diaphragm, spermicides
 3⃣- *Natural Birth control methods,* shine kamar ovulation test kit, cervical mucus examination, tracking menstrual cycles (rhythm method), intrauterine devices, emergency contraception irinsu morning pills
 4⃣ *-Surgical sterilization,* shine kamar tubal ligation(tube tided) , vasectomy
♦ *A-Pills* , kwayoyi magani ne da mata ke amfani dasu don kada ciki yashiga idan akasha shu daidai pills suna aikin su kusan kashi 99.9 % yana aiki, sannan akwai pills ma da anace dashi extended circles pills wanda akecema seasonal maimakon al'ada mace tayi sau 13 a ka'ida cikin shekara daya to saitayi sau hudu kawai kenan takoma dukbayan wata ukku ukku kenan wanda ana shanshi duk bayan sati 12 bayan sati daya ba a shaba kuma kala biyune watau seasonique da loseasomique. Mini pills shine pills da akafi sani sosai wanda akeba mata musamman masu shayarwa, shikuma yana hana sperm isa wurin kwayaye ne kuma shi anashanshi kullum ne sau daya shima yarabu biyu akwai mai kwara 21 da mai kwara 28 a cikinsa kuma ana fara shanshi lokacinda likita yace sannan yakanfara aiki tun watan farko kodayake wasu likitocin sukan bada shawarar watan farko idan za asadu ayi amfani da condom saboda rashin tabbas amma sauran watannin za a iyayi batareda condom ba
 *SIDE EFFECTS* , yanada side effects kamar yadda kowane tsari yakeda nashi shima kamarsu :tashin zuciya, ramewa, kiba, kumburin nono ko hushin nono, fitarda jini tsakanin jini biyu na al'ada ko spotting, jinin al'ada yazama mai haske, chanjin yanayi. Wasu matan wadannan side effects din sunada sauki gawasu abun kuma basuda sauki ko basu zuwa dasauki garesu. Akwai wasu alamomi da idan ana amfani da pills anafama da irinsu, ciwon ciki, ciwon kirji, yawan ciwon kai, matsalar gani bishi bishi, kumburin kafa ko cinya to suna nuna alamun wasu cututtuka kamar :-ciwon hanta, gallbladder, stroke, gudajin jini, hawanjini, ciwon zuciya sai ayi saurin zuwa asibiti.
 Amma yanada amfani don bayan hana daukar ciki akwai hana samun matsaloli irinsu, endometrial, colorectal, cancer ta mahaifa, amma bayan wadancan akwai wasu matsalolin da mai amfani da shi tana kara shiga cikin hadarin kamuwa dasu kamar su, cancer nono da cancer bakin mahaifa amma hadarin na tafiya ne bayan shekaru biyar.
 Ba kowace mace take ko yakamata tayi amfani da pills Ba wajen tsarin iyali, baidace matarda tayi shekaru 35 a duniya Ba tayi amfani da pills a matsayi tsarin tazarar iyali Ba inde tana shan taba cigarrete amma idan bata amfani da cigarrete zata iya amfani dashi harzuwa menoupouse dinta. Amma idan mace nada gudajin jini a arms, kafa, hunhu, kokuma wadda ke famada ciwon zuciya ko hanta kokuma wadda ke famada canxer nono da mahaifa kokuma wadda take famada hawanjini ko ciwon kai irinna gefe dinnan. Idan antabbata babu duka wadannan to sai atuna Idan akwai iyaye ko yan uwa dasuke da gudajin jini a cikin hunhu ko kafafuwa to a fadima likita kafin fara amfani dashi.
Idan kina amfani da birth control pills, incase ko kinmanta baki sha ba zaki iyayin amfani da condom ko spermicidal foams, idan kina amfani da patches kina amfani dashi duk sati zaki iya mayen gurbin sa da pills, idan kina amfani da zobe vagina acire sati ukku da sashi sannan kwanaki bakwai sai asake sawa. Zan dakata anan sai rubutu nagaba insha Allah. *DR SHUAIBU MB*(kiwon lafiya whatsapp group)

Comments