TUSAR GABA KO FITARDA ISKA GABA



*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑* *TUSAR GABA KO FITARDA ISKA GABA*
 Tusar gaba iska ne dayake fita ko fitowa daga gaban mace wanda take bada sound ko kara daidai da tusar baya da akeyi saidai ita tusar gaba bata bayarda wani wari ko doyi kamar ta baya.
 Inbanda ganin kamar wani abune na tozartawa a cikin mutane amma tusar gaba batada wani illa a cikinta
 *ABUBUWANDA SUKE KAWO TUSAR GABA KO FITARDA ISKA GABA*
♦ Jima'i ko saka wani abu a ciki gaba yana haifarda ita saboda iskan dayake ciki zainemi fita shiyasa za aji ana cewa ai bude kafafuwa ga mace lokacin da take zaune nasa haka.
♦ Pelvic floor exams, lokacin da likita yake examination na pelvic floor yayinda yasaka speculum device.
♦ Motsa jiki musamman yoga yana kawo irin wannan tusar gaba din.
 ♦Juna biyu ko menopouse.
 Haihuwa, saboda rauni da pelvic floor yayi.
♦ Wani lokacin tusar gaba tana tana faruwa ne saboda raunin da pelvic floor yayi saiya haifarda wani bangare na canal protrude dake cikin gaban mace saiya buda ta.
♦ Tayita tanasa mace tarika tusar gaba kamar colonoscopy.
 Amma akwai vagina fistulas watau yagewa ko tsinkewa da vagina keyi tsakanin ta da wasu gabobi a cikin jiki.
 ♦Yagewa ko tsinkewa da vagina keyi tsakanin mahadarta da mafitsara, ko hanji ko takashi watau bututu dayake fitarda kashi shiyasa ita irin wannan tusar saita rika fitarda wari ko doyi.
 Masu irin wannan yagewar za arika ganin bayan gida yana fitowa ta gaban mace musamman idan mahadarta da hanji koda takashi ce ta yage.
 Wani lokacin haihuwa, cancer treatment, rauni, yin wasu ko hanyoyin yin wasu tiyatar. Idan akaga discharge yana yawan fita ko bayan gida ko wari idan akayi irin wannan tusar to aga likita.
Ana iya rage ko magance irin wannan tusar idan ana tunanin raunin pelvic floor ne yakawo ta ta hanyar motsa jiki kokuma mace tarika yin kamar yadda take matse fitsari na tsawon second goma saita saki kuma tsawo second  Yin tafiya da batada nisa anayi ana maimaita wa yana rage ta.
 Idan kuma anayinta ne lokacin da ake jima'i sake position shine zai taimaka musamman achanza daga kwanciya kasa ko durkusawa.
 Shiga da fice a hankali lokacin jima'i zai taimaka sosai. *DR SHUAIBU MB* (kiwon lafiya whatsapp group)

Comments