*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑* 1⃣2⃣1⃣ *WADANNE ALAMOMINE AKE GANE MUTUM YAKAMU DA CIWON HANTA*❓
🤔Itade hanta ko liver da turanci wata gaba ce datake da girman kwallon kafa kuma tana kalkashin awazzu mutum ne daga bangaren dama na ciki, hanta ta zama dole wajen narkarda abinci da wajen tace dukwata guba ko datti.
Cutar hanta yawanci ana gadonta ne, sannan wasu abubuwa ma suna kawo ta kamar shan barasa, infection wanda shine yahada hepatatis A, B, C, E, saikuma kiba tana kawota, sauran abubuwa sunhada da cancer, kitse daya taru akan hanta, rashin ingattacciyar garkuwar jiki.
👨👩👦👦 Mutanenda sukeda ko suke hadadarin kamuwa da cutar hanta sunhada da, mutane dasuke kwankwadar barasa, wadanda suke sharing allura, ko dukwani tsinke na tsaga ko na de yankar jiki, wadanda ake karama jini kafin 1992 saboda a lokacin ba a tantancewa kafin sanya ma mutum jini, haduwar jini ko yawu ko zufa jiki, masu sex batareda kariya ba, masu diabetes da masu kiba.
✴Alamomin cutar hanta sune, fata ko idanu su zama yellow jaundice kenan, ciwon ciki da kumburin ciki, kumburin kafa da diddige kafa, kaikayin fata, fitsari mai duhu, bayan gida kokakke ko ja ko maijini, yawan kasala, tashin zuciya ko amai, rasa dandano dazai kaiga mutum bayason cin abinci
Kusan kishi 10-15% na kiba tana zuwa ne daga magungunna saboda wasu magungunna nasa mutum yarika saurin jin yunwa da cin abinci sosai, wasukuma su hana jikinmu ya iya kone calories kokuma yarika rike ko tara ruwa a cikinsa. Amma ba kowane mutum ake samun hakaba wasu mutanen na iya kara har 15 pounds kan magani daya wasukuma ko pounds daya ma basu karawa.
✳ Shikuma rigakafin ta shine, a kula wajen amfani daduk wani abu mai kaifi adena sharing dinsa, yin amfani da condoms wajen saduwa, anayin rigakafinta inkuma mutum yakamu da wata anayin rigakafin ta hepatatis A, B Wanda sune sukafi hadari, adena shan magani barkatai ko hada magungunna kala kala ayi amfani dasu lokaci daya, arika kiyaye chakuduwar jini da yawu dasauran ruwan jiki, a kula wajen fesa maganin sauro ko kwari, arika kwana inda iska ke shiga, a kiyaye fata daga magungunna feshi, ayi kokarin rage kiba
✍ *DR SHUAIBU MB* Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com
Idan mutum Yana fama da ciwon hanta ana umartarsa Daya rinka cin zogale da rake Amma ana cewa abinchi Mai maiko zuwa nama ance ya daina amfani dashi tambaya anan abinchi kamar indomie mutum zai iya amfani dasu ko kuma akwai wasu abinchi Daya kamata yake amfani dasu pls Ina buqatar Karin bayani akan abinchin da zaake amfani dasu
ReplyDelete