*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑* *🍌WANDA YAKE DA CIWON SUGER ZAI IYA CIN AYABA🍌* ❓ 1⃣2⃣3⃣ 🤔Ayaba de abune datake da matukar amfani da kara lafiya ga jikin mutum, saidai dukda amfani ta tanada suger da Carbohydrates sosai da sune manyan abubuwa dasuke saurin daga suger cikin jinin mutum.
Idan mutum yanada suger yanada kyau duk abunda zaici yarika sanin yawan carbohydrates dinda ke cikin abinda zaici saboda carbohydrates yana daga suger fiyeda duk wani sinadari wanda zai iya shafar treatment da mutum keyi na rage suger din
Idan suger yadaga ga mutanen da basuda diabetes sai jikin yasamarda insulin Wanda yake taimakawa yacire suger daga jinin mutum da kuma wasu cells da suger ke zama ko ake ajiye shi a ciki
Wanda ga Mai diabetes bahaka bane saboda kode baida insulin din ko yayi kadan kokuma suger yaki ko ya watsar da insulin dinda jikin mutum ya samar
Kusan Kashi 93% na calories cikin ayaba sunzo daga carbohydrates ne wanda suka kasu cikin fiber, starch, da kuma suger, kuma ayaba matsakaiciya ta kunshi kusan grams 14 na suger da grams 6 na starch
🍌A hannu daya kuma saboda fiber da ayaba keda shi zata iya rage karuwa suger din a jikin mutum wanda fiber din duk ayaba matsakaiciya tanada grams na fiber 3 a cikin ta kuma duk mutum anaso a rana yarika cin fiber harda masu diabetes dinkuwa
Fiber yanada matukar amfani ga masu suger saboda yana taimakawa wajen narkarda abinci da kuma yadda jikin mutum ke tsotsar carbohydrates wanda zai taimaka sosai wajen rage suger ko daidata suger a jiki
Hanyarda mutum zai iya gane cewa wannan abincin zai iya daga suger jikin sa shine ta GI watau *glycemic index* wanda munan inba kaje food stores ba ba a likawa a jikin abinci ko fruits amma wasu wuraren suna lika GI a jikin abubuwa
Shi wannan GI din shine ke nuna yadda abincin ke saurin dakuma yawan suger dinda zai iya karama mutum.
Karancin GI shine 55 ko kasada haka
Tsaka tsaki na GI shine 56-69
Wanda yayi yawa shine GI daga 70-100
Duk wani abinci da yake da low GI watau daga GI 55 zuwa kasa abune Mai mahimman ci gamasu ciwon suger sosai
🍌 Saboda haka ayaba tana tsakanin GI low da kuma GI medium watau tsakanin na kasa dana tsakiya don tana kamawa daga GI 46-62 ya danganta da nunar ta
🍌 Tsanwar ayaba wadda ba nunanna ba sosai tanada karancin suger a cikinta dakuma carbohydrates sannan kuma tana watsi da starch wanda daidai yakeda fiber
😆 Wanda wannan labarine mai dadi ga masu suger musamnan masu diabetes 2,bincike yanuna cewa mata masu diabetes 2 ayaba mai koren bawo wadda ba nunanna ba na taimakawa sosai wajen daidai ta suger garesu.
Ayaba nunanna KO Mai yellow bawo tanada GI dayawa kenan tana kara daga suger a cikin jini kuma baikamata masu diabetes suci ayaba nunanna ba KO mai yellow bawo ba
*Misali*
Sannan girman ayaba nada mahimman ci gamasu diabetes ba kawai nunanna ba harda girman ma abin kulawa ne don yanada mahimmanci sosai
🍌Ayaba Mai tsawon inch 6 kuma nunanna tanada yawan carbohydrates 18.5 grams cikinta
🍌 Ayaba mai tsawon inch 6-6.9 tanada carbohydrates 23 grams a cikinta
🍌Ayaba Mai tsawon 7-7.9 tanada carbohydrates grams 27 cikinta
🍌 Ayaba Mai tsawon inch 8-8.9 nada carbohydrates grams 31 cikinta
🍌 Ayaba babba Mai tsawon inch 9 nada carbohydrates grams35 cikin ta
🍓Duk KO dayawa tsarin abincin masu diabetes akwai fruits watau kayan marmari cikinsu, saboda cin fruits da vegetables na taimakawa wajen inganta lafiya mutum, suna taimakawa wajen rage hadarin kamuwa da diabetes din kokuma karuwa diabetes din, suna taimakawa wajen hadarin kamuwa da ciwon KO matsalolin zuciya, cancer saboda haka cin fruits da vegetables abune muhimmi
🍑Ba kamar sauran abubuwa dasukeda suger KO carbohydrates ba irin abubuwa da akayi a companies bawo, fruits dayawa dasuke da carbohydrates suna zuwa da fiber kuma a bangare guda Wanda harda ayaba ciki kuma sunada wasu minerals da nutrients da antioxidant din dayawa dasuke amfanar mutum
🍌 Musamnan ayaba harda su potassium, B6, vitamin c duk akwai su a cikinta
🍒 Shine ake ganin maimakon ahana Mai diabetes amfani da fruits saidai a takaita masa misali zuwa amfani da fruits kwara KO Kala biyu kawai a rana
🍌Wanda takaita amfani dasu din bazai sa suger yakaru ba kuma bazai Kara jiki ba KO nauyi ba, shiyasa ake ganin mutane dayawa masu diabetes yanada kyau surika amfani da fruits amma a takaice ciki harda ayaba
🍌 Saboda haka girman ayaba, nunarta, duksunada mahimmanci gamasu diabetes kuma sunason cin ayaba
🍌 Sannan yanada kyau idan zasuci ayaba surika hadata da yoghurt KO gyada yadda narkewar zata zama bada sauri ba zaizama a Hankali take narkewa
🍌 Kuma yanada kyau kafin mai diabetes yafara cin ayaba yayi monitoring tukuna yaga inyaci karama wadda ba nunanna sosai saiya auna suger bayan hour daya idan yaga bata daga masa suger ba to shikenan idan yagata daga suger to saiya hakura
✍ *DR SHUAIBU MB* Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com 6/11/2018
Comments
Post a Comment