*DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA*🚑🚑1⃣2⃣6⃣
Wani kashi ne ya fitom in a kirji na kafin akai wuya na meye maganinsa❓
Wannan shine *costochondritis*
akwai Gurungwirtsi kokin gane hausar watau cartilage da turanci wanda hade yake
da kirji zuwa breastbone to shine yake kumbura yanasa kirji ciwo kuma yafi
faruwa ga mata akan maza
Kashi ne mai kwari dayake shiga
tsakiyar kirji daya ke farawa daga bakin wuya harzuwa saman ciki, kirji yahadu
KO hade yake da Gurungwirtsi a costochondritis joints inda a wannan mahadan
suke ciwo saisu kumbura.
Yana damun mutane Amma baicika
cutarwa ba gaskiya kuma yawanci yana tafiya dakansa ne, bayan sati biyu KO wasu
watanni haka
Za aji ma'aikatan lafiya nakiranshi
chest Wall pain kokuma Costosternal pain dukde iri dayane
Yawanci motsa jiki mai wahala
KO daga wani abu mai nauyi KO yawan tari suke kawo shi
Kuma yana kumbura da zafi yawanci
bari daya na kirji musamman barin hagu baicika zuwa dika barinba
Kamar yadda nace yawanci shine
ke tafiya dakansa saidai idan yana ciwo ne ake amfani da magungunna rage radadi
sai asamu Hutu sosai arika hutawa, anguji ayyikan karfi, ana iya gasa wurin da
ruwa dumi
✍
*DR SHUAIBU MB*
Zaku iya turo da tqmbayoyinku kai tsaye ta gmail dinmu👉kiwonlafiya51@gmail.com
ko kuma kunememu ta blog site dinmu kiwonlafiya1.blogspot.com
Comments
Post a Comment