Wani lokacin sai inji numfashi nayimani wuyar yi, ko innayi to ban iya maidoshi sosai



DR SHUAIBU MB(KIWON LAFIYA)
**DAGA ZAUREN KIWON LAFIYA🚑🚑**
**TAMBAYA 4⃣
❓❓Dan Allah doctor matsala ce gareni a kirjina ko zuciya zance. Hakanan kawai wani lokacin sai inji numfashi nayimani wuyar yi, ko innayi to ban iya maidoshi sosai. Sannan idan naci abinci sai inji shima kamar numfashin zai dauke. Sannan ga yawan ciwon kai da nike fama dashi tamkar zai cire❓
Da alama kinada matsalar ciwon COPD,(CHRONIC OBSTRUCTIVE PULMONARY DISEASE). Yawanci masu matsalar COPD a takaice sunfi samun irin haka.
****COPD wani ciwo ne dayake sa huhu kumburi saiya haifarda kawo tangarda ko toshewar hanyoyin iska daga hunhu wani lokacin yankanzo da tari, ko yawan kakin majina, ko atiwashawa kuma za aga duk safiya sai anyi kakin majina sabida za aji kamar ta tokare makoshi. Wannan yana faruwa ne saboda dadewa da daukar hangula(irratation) na gasses kokuma wasu abubuwa musamman kamarsu hayaki to saiya kara ma mutum hadarin kamuwa da ciwon xuciya, Sauran alamun za aji numfashi na neman daukewa bayan yin tafiya kasa ko wani aiki ko motsa jiki koya yake, za aji ba karfi, ramewa, kirji yarika ciwo kamar ana daure shi, kakin majina dasafe, yawan tari da majina, dasauransu
Ga wasu mutane dayawa kuma wannan COPD din, saiya haifarda kumburin hunhu dinda yawa saiya mamaye kirji wanda yana faruwa ne idan iska tabi ta inda hunhu yasamu matsala to kuma idan muka cika ciki sai atura hunhun da karfi saiya haifarda alamar daukewar numfashi,
Sannan shi wannan matsalar ta numfashi da kike ji bayan kingama cin abinci da wanda shikuma cikinsa ke kumbura duk abune wanda yake uncommon ga mutane dasukeda wannan matsalar ta COPD, idan mukaci abinci muna bukatar energy dinda zai narkarda shi to idan kuma mukaci dayawa muna bukatar energy fiyeda yadda yake zuwa normal to ananne saimu kara ma kirjinmu da diaphragm dinmu sai arika jin wannan alamar ta daukewar numfashi.
***MAFITA***
1⃣Arika chin abinci kadan a lokaci daya sai arika chin abincin dan lokaci zuwa lokaci, idan mutum bayada kiba kokuma daidai ne to saiya rika yawan amfani da abinci masu calories sosai
2⃣ Sannan sai a takaita amfani da gishiri saboda gudun tara ruwa da yawan kumburin ciki dakuma dorama zuciya aiki
3⃣Sannan a kiyaye kokuma taka tsantsan da simple carbohydrates saboda gudun haifarda CO2 yaginu a cikin jini ya haifarda karancin oxygen
4⃣Sannan arika shan ruwa sosai, a kiyaye duk wani nau'in abinci dayake kumbura ciki sannan arika amfani da abincinda basai andade ana taunawa ba
5⃣Arika cin abinci a hankali bada sauri ba, Arika samun tazara tsakanin loma zuwa loma, bayan angama arika dansamu lokaci abinci na bin jiki.
ALLAH YABADA LAFIYA MAI AMFANI.
DR SHUAIBU MB(KIWON LAFIYA)
Top of Form

Comments

  1. Alhamdulillah doctor mungode Allah ya saka da Alkhairi wallahi doctor abunda nake Fama dashi Kenan Kwana biyu sai yanzu na gano matsalar to insha Allahu zamu kiyaye kamar yadda kafada mana mungode

    ReplyDelete

Post a Comment